page 4

2K 97 5
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

  Allah ka jikan mahaifiyata Kayi mata gafara kasa aljanna makomarta da duk sauran al'ummar musulmi gaba daya.

Godiya da jinjina ga mai dambu da binta aliyu

Ina mutukar ji dake billy billy

Mallakar Jamila(Maman amir)

    Wattpad@jami1020
    ******************
           P4
Ummi tayi shuru tana tunanin to wa zata samo mata da zata rinka taya ta aikin ana biyan ta suma fa suna bukatar aikin nan don su samu kudin da za su rinka amfani da shi wajen siyan kayan abinci lalurorin gida ga siyan maganin abba to ko ni zanje ina yi musu aikin ne sai ji tayi mom tana ce mata to maman afnan zan koma gida na bar amira a gida
    Ummi tace to hajiya Khadija in sha Allah zan duba miki idan na samu zuwa gobe zan shigo sai na gayamiki to ni bansan su nan  daya diyar tawa ba ummi tayi murmurshi ta ce sunan ta aleena sai waccen akun dama Kinsan sunan ta afnan suke nan wadanda Allah ya bani ni kuma suna na Zainab to Allah ya kara zumunci a tsakanin mu hajiya Zainab ummi tayi dariya tace Zainab dai ina naje hajj da za akirani hajiya tayi dariya tace hajiya zai zuwa hajj kiran Allah ne idan ya kiraka zaka ke ballanta na mai rai ai ai baya fidda tsammani sannan akiraka da hajiya ma kamar girmamawa ne ko haka ne kam to na gode hajiya Khadija to aleena yaushe za a shigo a gaisheni har gida don wannan gaisuwar ban Karba ba aleena tayi murmushi tace sai ummi tace ta yards zan shigo mom ta kara jinjina nawa a ranta lallai wannan gida akwai tarbiya  kuma da wani basu da son abin duniya to hajiya Zainab idan diyata bata shigo ba laifin na wajen ki na gode sosai da karamcin Ku to muma mun gode to kawar mai kyau sai anjima ko afnan ta kyalkyale da dariya ta rufe fuska.

Bayan tafiyar mom sai ummi ta samu Abban su aleena tana cewa ai kanjin duk yadda mukayi da ita ko kuma da alama tana da kirki sosai duk da mutum ba a shaidar sa lokaci daya game da zancen aikin da hajiya Khadija tace  shawara nake so na kawo abbansu mai zai hana ni naje na narinkayin aikin kaga sai mu samu rufin asiri sannan Ahmadu ma sai ya Dan huta da wani Abu tunda yana mana kokari duk cikin yan uwaka ba mai kula da mu sai Abban su ko ya kagani

Abban su yayi shuru yana tunani yace to ke ummin su ba a takura ki ba haba Abban su meye a ciki don naje nayi aikin don in kula da kai lokacin da kake da lafiyarka ba abinda bakayi mana don yanzu Nima zan zanyi aikin sai ya za mana akwai damuwa yayi shuru can yace to Allah ya shi miki albarka umminsu hakika nayi dacen mace mai hankali da sanin ya kamata Allah nagode ma sai tayi wani murmushi naji dadin yadda Mijin NATA ya fahimce ta cikin tsokana yace oh yaushe rabon da naga  irin murmushin soyayyar nan duk suka fashe da dariya har yaran nasu
Aleena tayi murmushin ta mai kyau soyayyar iyayen nata tana burgeta gashi akwai kyakyayawar fahimta a tsakanin su sai ta ce  ummina abbana ban yi muku katsalanda ni ina ganin da mama ta he tayi aikin gwanda ni naje nayi saboda bangs amfanina ba ace mahaifiya ta tana can tana aiki don hidima damu ni ina zaune agida alhalin kuma karfi Na ko nace girma Na ya kai da zan iya irin aikin da takeyi don Allah kubar ni naje nayi aikin ke ummi sai ki kula da Abba da afnan ta durkusa tace don Allah kar kuce  a'a

Iyayen sukayi shuru suna kallon ta to yar albarka aleena na islamiyyar fa Abba ai sai da yamma ne muke zuwa  naga ina iya zuwa da safe wajen aikin da yamma sai naje Islamiyya pls Abba don't say no idanta yana fidda kwalla tana fada cikin shagwabar ta da take yi mata kyau sai Abban ya ce to Allah yayi miki albarka ya baki miji Na gari da zur'a dayyiba amin inji ummi ita ma a zuciyar ta race amin saboda adduar iyaye tana da mutukar tasiri da yaran su kuma bata fadowa kasa(iyaye mukula a ko da yaushe mu rinka yiwa yaran mu addua duk irin fitinar da zasuyi tsakanin ki da su sai Allah ya shirya mana Ku ban da mummunan ba ki)
***********
Doctor Ashfaq kuwa yana driving yana ta fadan zuci  how dare she slapped me gashi abin haushi bansan ko wacece ba bansan gidan da take aiki ba don ba tayi kama da yaran masu kudi ba Duke ranar da suka hadu sai ya hukunta ta kuwa sai tasan ta mareni idiot mtsss har ya isa wajen daurin auren yana mita a zuciyar sa yana ji kuma wayar sa tun dazu tana ringing ya ki ya daga ya san ba zai wuce wannan akun ba wato babban amininsa  Amir

Yanayin parking ya fito ya yi dialing number Amir ringing daya  ya daga kai wallahi ka dai nayiwa mutane wulakanci don kaga ana sonka shine make yiwa mutane haka saboda Allah sai yanzu ga Dakar zuwa wajen dairin auren sai da aka gama mtsss ni yanzu kana ina gani Na tsaya adai dai osis bakery mota baza ta iya shiga ba saboda mutane Dan rain in hankali gani nan fitowa wallahi Matar ka ta shiga uku da wannan muskilancin  naka Allah ya hada ka da kitt ashfaq ya kashe wayar saboda yasan in ba kashewa yayi ba amir ba zai tabayin shuru

Yana zuwa ya kalli fuskar ashfaq ya ga tafi ta kullum daure wa yace to yau waya tabo mutumin haka ashfaq yana ganin shi ya ce muje suka he suka gaisa da ango da sauran abokanan su ana ta mamakin ganin sa tunda sun San ko cikin mutane ba ya shiga  daga nan suka wuce shi da amir suka hau mota zai ke gidan su amir ya Haida Maman sa hajiya Umma bata da lfy shiyasa ma amir bai zo da mota ba suna cikin mota sai kwafa yake tayi yana hmmm Allah ya hadani dake sai kin rains kanki budar baking amir sai cewa yayi yo ko an gano mana Amaryar mu ne sai kuuuuu ashfaq ya taka burki ya kawo wa amir suka
**************
07038185042

Comment
Comment

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now