page 37

1.2K 75 9
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION...

ALLAH KA JIKAN MAHAIFIYA TA DA YAN'UWANA KAYI GAFARA GARESU DA SAURAN MUSULMI BAKI 'DAYA.

ALLAH KA BAWA MAHAIFINA LAFIYA KA SAUKAKA MASA DON ALBARKAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Ina godiya gareku masoyana da yawan addu'o'in da kuke wa mahaifina nagode sosai.

Mallakar Jamila(Maman Amir)

Wattpad jami1020
*****************

P37

...."maraba sannunku da zuwa ku shigo ciki Mana daga ciki Abban na su Yana ciki" umma take gayawa su Dad amman idon ta na kallon Amir saboda wata irin kunyar su Dad 'din ce ta kamata.

Amir yace "to umma" ita kuwa Afnan tuni ta ja hannun Ashfaq da guda cikin 'dakin."to kiyi masa a hankali Mana karki kayar da shi mana Afnan"in ji umma."ai 'kyaleta umma hakan da tayi ma yayi kyau,idan wani ya fa'di a gidan surukai ai an Sha kunya,Kuma naje waje na bada labarin abinda ya faru" 'kyal'kyal'kyal ... Amir ya Kara sa dariya bayan ya gama tsokanar Ashfaq.sannan suka karasa cikin falon duk da murmushi akan fuskar su especially ma Dad.

Ashfaq ne a gaban Dad zaune,bayan sun gama gaisawa dashi yana Kara tambayar Abba da jiki da Kuma yadda yake ji a jikin sa Amman cikin kunya yake maganar,su Dad suka shigo suka zauna, Ashfaq ya dubi Abba yace "Abba dama Dad 'dina ne ya dawo daga tafiyar da yayi shine ya zo ya gaishe ka ya Kuma duba jikin naka "

"...Allah sarki  Masha Allah ai kuwa na gode sosai" Abba yake ta godiya
. Sannan aka sake wata sabuwar gaisuwar a tsakanin su nan da nan Hira ta 'barke,ita dai umma tashivtayi daga cikin su ta fita tsakar gida.suna cikin hirar ne fa Afnan ta dawo kuwa da Dad tare da ce masa Dad na fa kawo maka Kara,karar wa Kuma Afnan 'din Mai kyau?karar ya Ashfaq na kawo maka banji dadin abinda yayi wa ya Aleena ba,ta fa'da muryar ta na nuna da gaske taji haushin abinda yayi wa Aleena .

Falon ya dauki shuru na wasu sekonni,yayin da zuciyar Ashfaq kamar ta tsaya kirjin ta fito waje saboda tsananin bugu tare da mamaki to me yayiwa Aleena haka da har 'yar karamar yarinyar nan ta ke nuna jin haushin ta akan abin"..ko dai yarinyar nan ta gaya musu abinda ya faru a dasu ne 'dazu? Kai Ina to ai bata ma fito ballenta na ta gayamata"Ashfaq dai yayi ta magana a cikin zuciyar sa.

"...ke bana son wannan surutun naki ki tashi ki bawa mutane waje" Abba ya fa'da wa Afnan. Ya hakuri Abba yanzu zan fita,ta tashi jiki a sanyaye ta Kai bakin kofa Sai ta juyo tace da karfi "Dad wallahi Mai kyau ne ya hana ya Aleena yin barci jiya,kwata kwata bata Sami barci ba da na tashi na naga idanun ta sun kumbura Kuma ta makara bata tashi da wuri ba,na tambayeta meya same ta shine ta ce min wai mai kyau ne ya hana ta yin barci,shine nake ta tunanin ta ya akayi Mai kyau har ya shigo cikin 'dakin mu ya hana ya Aleena barci don na gani fa har wani rintse idanuwan ta takeyi fa Sai ta dafe gefen kirjin ta,shi yasa na kawo karar sa fa bana son abinda zai 'batawa yaya Aleena rai.." ta Kara she maganar a hankali idan ta har da kwalla Wai ita an taba maya 'yaruwarta.

'dakin yayi shuru ko da fahimtar da yayi wa maganganun na ta a zuciyar sa,amman ta bangaren Ashfaq kuwa wani irin farin ciki ne yake shigar sa da jin maganganun Afnan,wato ke nan idan ya fahimta ya Kuma gane tunanin sa ne ya hana Aleena barci shine ya janyo har ta makara ok wato idan bai manta ba ya tuna da lokacin da Take gaya masa 'dazu da take ce masa ai shi ya janyo ta makara,bi ma'ana dai tunanin sa ne ya janyo har ta makara bata zo gidan su da wuri ba to ke nan tana son sa.yasa murmushi da yar dariya dariya Yana shafa kansa har da fa'di Alhamdulillah a fili batare da ya  dai na murmushin ba,to Kuma Sai kallo ya dawo kansa nan da nan Kuma Sai ya wani daure fuska da yaga irin kallon da suke masa dukka dakin especially sarkin magana Amir ai kuwa kafin ya Kara daukar wani matakin don hana Amir magana Sai jin muryar sa yayi Yana cewa "..hmmm lallai kuwa ta ya zakayi ka shigo cikin gidan mutane ka hana yarinyar su yin barci?to Wai ma garin Yaya Ka shigo cikin gidan?"ya turbu ne fuska ba wasa kamar bai fahimci kan maganar ba.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now