page 31

1.1K 67 15
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Ya Allah kayi rahma da gafara da jin kai ga mahaifiyata da yanuwana, muma in tamu ta zo kasa mu cika da imani.

Ya Allah ka bawa mahaifina lafiya ka saukaka masa don Annabi

Ya Allah ka sadamu da alkhairin da ke cikin wannan shekara ka Kuma nisanta mu da Sharrin da ke cikin ta.

Ina Kara godiya gareki adda ramla Mai dambu kina bani kwarin gwiwa Allah ya Kara daukaka

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P31

Not edit

Yana gama fadar haka mom da dad suka kalli juna suka fashe da dariya, dad yace" to son menene na rawa nurya da hada gumi haka kamar wani mai laifi ko dai akwai wata a kasa ne bamu sani ba ko kuma aleena ita ve surukar tawa ne da muke ta jiranta sai yanzu ta bayya na uhummm oya tell me"

Sai ya dan tsare gida saboda baya so yayi wani abun da za a gano cewa Yana son aleena don shi a ganin sa Bai dace ace Yana son karamar yarinya haka din kamar rashin aji ne wannan.ni fa ba haka bane ba dad kawai dai taimako ne nake son yi kamar yadda kuke cewa mu taimakawa na kasa damu,don idan ka taimaki wani to Allah zai taimake ka Kai ma a lokacin da baka zato ba,so they need our help.

To son Allah yayi maka albarka ya baka mace tagari,kaje kayi duk abinda ya kamata kayi a school din su but did you talk to her parent? No dad but zan je na same su in gaya musu in Sha Allah ba zasu ki ba tunda naga mahaifin yarinyar Yana so yaransa suyi karatu sosai especially ma babbar ’yar ta sa,wake nan? Dad ya tambaya ok afnan nan ko,dad ba haka sunan yake ba fa,to to to,to ka tunamin mana,"oh nikam na shiga 'daka ni na tabajin irin wannan lamari Wai a ce mutum bazai iya Kiran sunan wata ba kamar wata surukar ka"mom take fadar haka Tana tafa hannuwan ta.wai meke tsakanin ka yarinyar nan ne? Kagayamin gaskiya,haba mom wacce irin tambaya ce wannan,hmmm mom tambaye shi da kyau don wallahi ya ashfaq son sis aleena yake,ke Ina wasa da ke ne ni na ce Miki haka don kawai Ina tausaya musu shike nan Sai a fassarani da wata manufa,to shike nan na ma fasa  taimakon na su suyi ta zama haka ba karatun, "eh to gaskiya tun da dai har su sun fara fassaraka da wata manufa kawai ka rabu da su in suna da rabon yin karatun sayi anan gaba"inji dad.

Gaban ashfaq ya fadi ras! Bai San lokacin da yace dad da gaske kakeyi ne? idon shi a waje.  Da suyi ta damun ka fa suna zargin cewa son yarinyar kakeyi ba gwara a kyale su ba ko ba haka ba ni kuwa duk abinda zai sa a dameka ba na son shi,Sai kawai suka fashe da dariya dukkan su ban da amatullah da take a kufule ran ta duk a bace tun da ya sako maganar aleena

ta kalli dad tace haba dad ya za ayi su rinka hada shi da wata 'yar tsanar yarinya da bata da wani aji 'yar talakawa kawai dai don Tana da kyau ai ba Wai ya rasa masu son shi bane ba fa dad.ashfaq ko wata muguwar harara ya cilla mata jin irin maganganu da take fada akan aleena tare da cewa ki iya bakin ki malama wa ya sako dake,ita din bata fiki
Komai da komai ba ga hankali ga nutsuwa ga Jan ajin ke har kina da wani ajin da kike maganar akai me mtssss.

Ya ashfaq akan wata can kake gaya min irin wadannan maganganun haka na gaya Miki din Naga alama ke baki San darajar mutane ba shiya sa na gaya Miki hakan nan da nan ta tashi aguje tayi sama tana kuka don maganganun sun taba mata zuciya fiye da kullum ta Kara jin tsanar aleena a ranta Kuma akan ta zata rama.

Su mom da dad kuwa zuba masa ido kawai suka yi suna sauraran shi yadda yake hakikan cewa don kawai an taba aleena,mom tace sannu son nan fa ya an Kara cewa ya kusa yayi kato'bara fa Sai ya dan sosa 'keyar sa ya tafi zai bar falon ,ashafaq Bai kamata fa karinka wulakanta 'yata fa a gabana ba gaskiya fa ba zan dauka ba ,to ita mom meya sa ba zata kyale ni ba ne take ta nemi wani ko ta jira har lokacin da wani zai zo yace Yana son ta! No kam gaskiya na bana yi mata irin wannan son Kuma ba zan taba yi ba gaskiya,ni a halin yanzu na ga wacce nake so Ina jira ne kawai lokacin yayi u daidaita da ita.toh Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,amin ya juya zai tafi Sai dad yace kasan me ni fa har naji Ina son yarinyar nan fa wacce fa dad aleena nake nufi ni kaga har na rike sunan ta daga zuwa na Kai ka kasa rike sunan nan da nan ashfaq ya saki murmushi da gaske dad, yes son.tanks sannan yayi waje ya tafi in da maigadi yake zama don yasan yanzu aleena tana gab da zuwa.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now