page 38

1.3K 76 29
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN MAHAIFIYA TA DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMI BAKI'DAYA KAYI MUSU RAHAMA KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU.

ALLAH KA BAWA MAHAIFINA LAFIYA KA SAUKAKA MASA DON ALBARKAR ANNABI.

GAISUWA TA GAREKI YAYATA ZAINAB IBRAHIM ABUBAKAR ALLAH YA BAKI TSAYIN RAI DA LAFIYA

MALLAKAR JAMILA (maman amir)

Wattpad jami1020
*****************

P38

Abba dai yayi shuru ya kasa cewa komai,ganin yadda wannan mutumin mai daraja da kwarjini ya zauna a gaban shi ya riko shi ya bashi auren 'yar sa ga 'dansa,duk da tarin kudin da yake da shi Bai nuna cewa shi Mai kudi bane bai ga Kuma irin talaucin da suke ciki ba Amman ya nemi ya ha'da  zuriya da shi.kuma da alama Ashfaq din Yana son Aleena sosai,don gashi m Allah Allah take yi a bashi auren Aleena har maganar da take yi a zuci ta fito waje.

Sai ya tuno lokacin da Yana kan ganiyyar rashin lafiyar sa Yana ganin kamar a zai tashi ba sai ya nemi babban yayan su Auwalu da ya ha'da auren 'dansa da Aleena amman kememe ya ki yarda don Yana ganin ba shi da komai,Abba yayi Kuka lokacin na zuci Dana waje shi da 'danuwansa Ahmad,Sai da Ahmad din yayi ta rarrashinsa akan yayi hakuri komai na Allah,idan lokaci yayi Allah zai kawowa Aleena mijin ta 'dan babban gida.to gashi kuwa abin Yana faruwa a zahiri,Abba yace a zuciyar sa "Ina ma Allah zai kawo 'danuwansa Ahmad ayi abun nan a gaban sa,bansan wani irin farin ciki da mirna zai yi ba.." Sai jin muryar  Dad yayi Yana cewa "ka kwantar da hankalin ka son idan akwai alheri a tsakanin ku Allah zai sa a bamu ita ya tabbatar da auren ku,idan kuwa babu to ba makawa Sai dai ka hakura dik da irin son da kake yi mata" in Sha Allah ma akwai alheri Dad wallahi tallahi Ina son ta Ina kaunar ta Dad har da 'yar kwallar sa.Amir kuwa Sai da ya ji tausayi Ashfaq Yana Kara making da ma akwai wacce zata iya sa abokin sa acikin irin wannan yanayi I will fight for my friend to get his love,ya danyi gyaran murya ya kallo Abba yace" wallahi Abba tun da muke da abokina ban taba jin yace Yana son wata yarinya ko yayi friending da ita nayi masa maganar har na gaji to Sai gashi akan Aleena duk ya wani sukurkur ce akan son ta,wallahi Abba Ashfaq Yana son 'yar ka Yana son auren ta kuma zai rike ta tsakani da Allah don Allah Abba ka da ka hana mu Aleena."

Dad ya katse su da ku ba ma son shirme kun ji ko ku tashi ki fita ku bamu waje mu karasa maganar mu ni da abokina daga baya kwa ji feed back Amir zai yi magana Dad ya yace shiiii tare da dora hannun sa a bakin sa nan ya tashi tsaye,shi kuwa mutumin fa bai da alamar Mikewa tsaye Sai ma kara Zama da yayi Dad ya kalle shi Sai yaji dariya ta kama shi Amman Sai ya dake bai yi ba,yace malam Ashfaq a tashi a dan bamu wuri ko,maimakon ya tashi Sai ma kara sunkuyar da kan sa yayi kasa.Abba ya sa dariya Shima dai dole Dad yayi dariya Amir kuwa Bai samu damar yin dariyar ba saboda tausayi abokinsa.

"To ni dai kam Alhaji babu abinda zan iya cewa anan Sai dai nace Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkhairi a tsakanin su har ga Allah wallahi ni na amince da wannan batu dik da dai ya zo min ne a bazata sannan zan Kira 'danuwana na gaya masa ya Kuma yi duk abinda ya dace na al'ada da akeyi idan an zo neman aure,Sai Kuma abu na karshe idan Aleena ta dawo in Sha Allah zan tambaye ta idan tana son shi kaga Alhamdulillah idan kuwa ta ce bata son shi to gaskiya Sai dai kayi hakuri bazan iya yiwa 'yata auren da bata son mijin ba,amman don ta ni wallahi Ina Murna sosai don Ashfaq kamar 'da yake a wajena."

"Ah to masha Allah nagode sosai abokina haka ake so mutum mai dattako ba komai zamu jiraka in Sha Allah,Ina fatan Allah yasa muji labari mai dadi,don ni kaunar bana so na rasa Aleena a matsayin suruka ta"Dad Yana gama fad'in haka dik suka sa dariya har da umma da take waje amman dik tana jin abinda suke cewa farin ciki ya cika mata zuciya,don dama tun farko jikin ta na bata wani abun akan Ashfaq 'din.duk dariyar nan da ake yi banda Ashfaq da yayi kicin-kicin ya bata rai,Abba ya juyo ya kalle shi ya ce haba doctor ka Zama jarumi Mana ni fa ban ce zan hanaka Aleena ba,na baka dama kaje ka nemi soyayyar ta idan Kuma dama kuna son juna to Sai dai mu Sha biki kawai,aka karasa wata dariyar dukkan su shi dai kawai Ashfaq dan murmushi kawai yayi zuciyar shi ta Dan yi sanyi jin Abba zai ba shi Aleenan sa,to Sai dai Kuma shi ba zai iya zuwa Kai tsaye ya ce mata Yana son ta ba,ta ya ma zai gaya mata Wai duk a tunanin shi da yace Yana son ta shi ke nan raina shi zatayi gwara kawai su cigaba ahaka ya rinka nuna mata alamomin su(kuji mutum fa da wani irin tunani).su kayi wa Abba sallama suka fito waje nan ma suka yiwa umma sallama.suka nufo gida,sun fito kofar gidan ne suka ci karo da wani zai shiga gidan,suka dan gaisa da shi sama sama. zuciyar Ashfaq dai Sai lugude take ta yadda zai fuskance Aleena,tsoro shi daya Kar taje gida Abba ya tambaye ta tace ai bata son shi akwai Wanda take so."Dad baka yiwa Abban su zancen komawa school din ba fa"Ashfaq yake gayawa Dad.eh Ina sane ai idan nayi mishi maganar ai Sai abin yayi yawa Sai ya ga kamar zamuyi masa iko da 'yar sa ne,but karka da mu zan zo da Kai na personally nayi mishi maganar kamar saaura none week su koma school 'din.ok Dad tanks.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now