page 34

1.2K 70 11
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN MAHAIFIYA TA TARE DA YAN'UWANA KAYI GAFARA DA RAHAMA GARESU.

YA ALLAH KA BAWA MAHAIFINA LAFIYA KA SAUKAKA MASA.

Mallakar Jamila (maman amir)

Wattpad jami1020
*****************

P34

Not edited

Annur don Allah ka taimaka ka je kaga yarinyar nan da nake maka magana akan ta,tana da kyau ga kyawun halaye,gashi tana da ilmi daidai gwargwado,a wannan shekarar zata gama makaranta.

Kaiii momy ashe ma ko secondary school ma bata gama ba Amman kike so na je wajen ta akan maganar aure gaskiya ba zan iya zuwa ba.momy tace "idan ka ganta annur zaka so ta kada fa wani ya zo ya rigaka ka zo daga baya kana danasani akan rashin bin maganar mahaifiyar ka fa,idan kaje din kaga bata yi maka ba shi ke nan Sai a hakura,idan tayi maka Kuma dama haka nake fata,yarinyar 'yar kawata ce idan nace Ina so bazan ta hanani ba pls annur"(Ina gyafe Ina mamaki yaran yanzu da iyayen su za su yi musu magana akan abu Amman ba za su bi umarnin su ba,nace hmmm zakayi danasani kuwa da bashi da amfani annur akan rashin bin maganar mahaifiyar ka)

"Ke ma dai kin fiye baci yaron nan yace baya son yarinyar nan amman kin nace lallai Sai yaje ya ganta,ki 'kyale shi ya nemo yarinyar da tayi masa mana" alhaji bai kamata kana daure masa gindi ba fa annur yayi girman da za ace yanzu Yana da iyali ko yayi hankali amman Kai kanka Sai mayar da shi kake yi yaro karami haba saboda Allah,Ina jiye mana gaba fa,ke ai kin ji matsalar ki,baki Sai kiyi ta yi masa baki,ni ban yi masa baki ba alhaji saboda nasan illar yin haka,magana ce kawai nake fadar ta akan gaskiya ku Kuma bakwa son a fa'di gaskiyar.

Annur kana so kaje ka ga yarinyar nan ko baka so? Alhaji ya tambaye shi,gaskiya ni dady bana so ta bar ni na zabi wacce nake so Kuma lokacin da naga damar yin aure sannan zanyi.to shi ke nan an gama,yanzu kaje inda zaka je Allah yayi maka albarka,momy tace Amin Allah ya shirya,shi ko ya ka'da kansa yayi ficewar sa abinsa.

Alhaji kasan dai da irin 'barnar da annur yake tafkawa a waje ko ga bin matan banza,ga shaye shaye,Sai yaje ya kawo Mana abin kunya a matsayin jikan ka,Kai Wai duk baka tunanin wadannan abubuwan ne?wannan abun da kake masa fa ba gata ba ne ba fa.

Shi ya sa mutane suke zagin 'ya'yan masu kudi da cewa basu da tarbiyya,ba su da ilimin addini Sai na boko wato ilimin nasara.da duk Ina ganin laifin irin wadannan maganganun amman ban da yanzu,saboda gashi nan Ina gani nima a fili,don Allah Alhaji ka dawo hankalin ka.to idan kin gama busa sarewar ni nayi nan,yayi tafiyar shi ya bar ta a wajen zuciyar ta nayi mata 'kuna.
*****

Aleena ta 'danyi gaba kadan daga jikin ashfaq tana sauke numfashi saboda ba'kon abin da take ji a jikin ta,shi ma rintse idanun sa yayi don da ma karfin Hali kawai yakeyi Allah kadai yasan me yake ji.
Cin 'yan second ya bude idanun sa sannan yace ni fa da kallon yarinya nake tayi miki fa bansani ba ashe yarinya ta girma,da mamaki Aleena ta juyo tana kallon shi saboda jin maganar da yayi mata ta rainin hankali,sannan ta kalle shi tace au haba da baka sani ba sai yanzu? Ka kalle ni sama da kasa zaka san cewa ni ba yarinya ba ce ehee, ta 'dan Harare shi.

Ya danyi murmushi Mai sauti ya ja da baya tare da cewa to bari na kara kallon na ki Sai na kara fahimtar abinda Kika gaya mini ko? Tayi tsaki ta juyar da kanta,wajen minti 'daya dai taga bai dai na kallon ta ba.tace Wai malam kallon bai isa ba ne har Sai ka gano muni na haba,ni ka matsa nayi abinda ya kawo ni na bar maka kitchen din.ai ke baki da muni kwata kwata,komai naki mai kyau ne don in Ina kallon ki bana so na bar kallon ki Kuma bana so wani ya kalle min ke don Ina da kishi sosai akan abinda nake so.

Tayi galala tana kallon shi jin abubuwan da yake gaya mata yau ba tare da ko shakka ba Kuma da takalli idon sa iya gaskiyar shi ya ke fada.to wa yake so? Ko ni yake so ne? Sai ta wani waske ta ce to ba sai kaje ka nuna kishin naka a in da kake so ba.to gashi ko ina nuna wa,to ai ni kake gayawa haka,Ashfaq yayi dariya sosai yace na gaya Miki ke yarinya ce amman kina wani timing musu da cewa ke ba yarinya ba ce.to ni kake so ke nan ko ko me? Ya Kara matsowa gab da ita yasa idanun sa a cikin nata sannan yace mata look in to my eye you will see your answer madam,sama da minti daya suna kallon juna tana ta ganin abubuwa cikin idanun sa karshen dai ta dauke kanta,tare suka sauke ajiyar zuciya.

Ya 'dago da kansa ya kalle ta ya ga ta sunkuyar da kanta kasa tana ta wasa da hannun ta da alama ta shiga tunani.Aleena tana cikin tunani Sai ki tayi yace subhanalillahi meye wannan a wajen kafa'dar ki yake tafiya,da Sauri ta kalle shi tana cewa menene? cikin yanayi na tsoro mu gani kamar fa kyankyaso ne ya shige jikin ki ta cikin hijabin ki...kafin ma ya Kai karshen Aleena tayi wani mugun tsalle ta cire hijabin ta ta wular da shi tana ta faman karkabe jikin ta,don ita a rayuwar ta ta tsani kyankyaso tsoro shi take ji sosai balle har ya hau jikin ta Sai ta dade tana jin kamar shi ne yake mata yawo a jiki

Ashfaq ko shagala yayi da kallon ta don ashe duk yadda yake tunanin yarinyar nan ta wuce wajen,ya kalli kirjin nan tubarkalla Masha Allah a cike fam kamar na wata babbar mace,ashe dama hijabin ne ke Kara boye mata kyanta,ga hips din nan Masha,wannan Ina ga in ta Kara girma Kuma,ko ya ya in tayi motsi Sai abubuwan nan sun yi motsi,ya ga dai idan ya biye da kallon ta to fa za ayi abin kunya don a yanzu haka kinsa yake ya fara saukar 'dumi,to tun kafin abin yayi zafi gwara ya bar kitchen din

Ke ke kitsaya ki bar ihun nan ya fa tafi da wasa ma nake miki ashe shazumamu ne,cak ta tsaya Amman fa jikin nan bai dai na rawa ba.don Allah ya Ashfaq da gaske kake babu komai?eh da gaske nake yi to ki kwantar da hankalin ki,Sai ta juya kawai ta life. Kan ta ajikin dirowar da take kitchen din tana Mai da numfashi,shi Kuma Sai ya dauko hijabin ta ya sa mata ajikin ta duk tana jinsa ba ta dai ce komai ba,sai ya sunkuya Dai dai kunnan ta ya ra'da mata da cewa Sai da naga wannan abun a jikin ki sannan na San cewa lallai yarinya ta girma,kije ki gyara jikin ki ta baya Kar ki fita a haka wani ya gani don idan wani ya ga staining din nan ba zan ji Dadi ba saboda ya gane min sirri na.yana gama fa'da matar haka Sai yayi sauri ya fita daga kitchen din zuwa falo Yana ta doka murmushi,ita Kuma ya bar ta sandare awajen jin irin kalaman da yayi mata.

Yana isa falo kuwa,Yana zama ya daukar plate zai zuba abincin sa ya ci,kowa ya tsaya kallon sa,dad ma ganin yadda yaron nasa yake ta murmushi cikin annashuwa ne Sai Shima ya ji Dadi a ransa,ya dai kamata yayi wani abu akan ashfaq da Aleena idan sunje gaisawar da mahaifin ta anjima,saboda ba zai bari suna kebewa tare ba saboda Sharrin shaidan la'anan ne.

Kai Wai bangane ba ya kana dawowa daga kitchen ka zo kana serving kanka ka bari ta kawo ruwan wanke hannun Mana,Wai ya akayi ma ne suka Kuka dade acikin kitchen din, Ina ita Aleena?

Mom  'kya tambaye ni? Ni abinda ya Kai ni kitchen din daban Ina gamawa na fito Kuma na Riga na wanke hannun nawa a can ki kirata Mana ki ji.

Hmmm nace su Ashfaq manya ka dai je ka har gitsa musu yarinya ka Kuma fitowar ka,ita Kuma ta kasa fitowa ,

To ko me Aleena  za tayi ?

Wani hukunci dad ya yanke ya sanarwa abban su Aleena?

Hmmm muje zuwa
*********

07038185042

Comment

Comment

Share, vote, and follow me on my wattpad pls

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now