page 45

1K 67 3
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA.

AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION INA ALFAHARI DA KU SISTERS.

ALLAH UBANGIJI YA YAYE MANA WADANNAN FITINTUNUN DA SUKE DAMUN KASAR MU.

BAN FA MANTA DAKE BA MAI DAMBU ALLAH YA KARA DAUKAKA
MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

P45

Amira tana tsaye a bakin gate din gidan su tana jiran dawowar su Aleena tana Kuma mamakin ya aka yi yau suka Dade haka ba su iso gida ba
Ko me ya tsayar da su mtsss ta ja tsaki sannan ta ce shi wallahi ya Ashfaq ya fiye na ci duk ya bi ya nacewa baiwar Allah wannan idan akayi bikin Kuma ai shike nan kuma ba zai bar ta taje ko Ina ba ke nan kullum yana like da ita ta Kara Jan wani tsakin.

Can zuwa kamar minti goma Sai ta hango motar Ashfaq ta danno Kai cikin layin hmm ga masoyan asali nan sannan ta kyalkyale da dariya

Tana jirana su Kara so Sai ta ga wani adaidaita sahu Yana bin su a hankali kamar ba ya son yayi tafiya,Sai kuma ta ga ya tsaya yayi parking gefe,ko da ya yi parking din Kuma ba ta ga kowa ya fito ba.har dai su Ashfaq suka Kara so.

Da Saurin ta ta isa wajen motar 'bangaran da Aleena take ta fara magana da Dan fushi-fushi"tun dazu Ina ta faman jiranki kin ki ki dawo kina can wani waje Sai faman Shan soyayya kukeyi ke da yaya kin dai San Yanzu muna da abubuwan yi ba kadan,time din da muke da shi kadan ne,saura kwana nawa mu gama school din da min gama fa shike nan za a shigar shirye shirye,na ga kamar ma ke Bai da me ki ba ko?tayi kwafa Kuma kinsan Allah Sai......."ke ke ya isa haka mana"Ashfaq ya katse ta daga maganar da zata fada.

"Ke in kika fara surutu ba kya sa full stop ne balle comma,wannan fa a matsayin yayar ki take amman ji yadda kike mata magana Sai kace sa'ar ki,ko in manta ne na tuna miki ita ce fa wacce zan aura"

Aleena dai ba ta ce komai ba ta bu'de motar ta fito waje ta kalli Amira sannan ta ce "sis kiyi hakuri yayanki ya tsayar da mu amman tsayarwar ta alkhairi ce,din yayanki akwai taimako haka ake so duk wani Wanda yake dashi ya taimaka wa talaka,am proud of him.to gashi yanzu Mun dawo,zai yuwu har muje can sannan mu wuce islamiyya ?"

Amira ta rungumi Aleena tace "ba damuwa sis,raina ne ya Dan back kadan,kin San akwai shirye shirye a gaban mu da yawa,ga bikin da zamu je ranar asabar shi ma kin ga dole mudan shirya mata wani abun ko? Ko ya ya kika ganin?"

"Lah kinsan na manta da zancen bikin binta,to Allah ya Kai mu lokacin da rai da lafiya,amman ya zamuyi mu tafi ga wannan yayan naki da ya kasa ya tsare?"

"ki bari zan yi wa mom magana Sai ta ha'da mu da driver in ce ka da ta nuna masa ma"Amira ta mayar mata da amsa.

Ashfaq dai yana tsaye yasa kunnen sa sosai don yaji abinda suke cewa,amman Bai ji komai ba sai,kawai da yaji kalmar biki,Sai kuma da Aleena ta ce Allah ya Kai mu lokacin.duk Sai ya dauka ko zancen bikin su suke yi ,amman duk da haka dai ya San akwai wata a kasa don yadda yaga suna magana kasa-kasa alamar rashin gaskiya ke nan,amman dai zai bincika ya jibko menene plan din na su da ba sa son yaji.

Aleena ta juyo a kalle shi sannan tace "to ya Ashfaq ñagode Allah ya karo arziki da wadata don a Kara cigaba da taimakon mutane "

A dakile ya amsa da Amin sannan ya daka mata hararajun tace masa ya Ashfaq wato yau din ba ba cewa thank you my king.

Aleena ta sa dariya mai dauke da murmushin da yayi bala'in yi mata kyau don tasan dalilin da yasa ya harare ta,ta kama hannun Amira za su shigar cikin gidan Sai ta dan ji juyo dama Kuma ita ya ke kallo ta yi masa gwalo tare da kashe masa ido daya sannan suka shige cikin gidan.

Ganin abinda tayi masa Sai da numfashin sa ya dauke na Yan sakwanni sannan ya dawo ya Dan dako kirjin sa,Kai yarinyar nan za ta kashe ni fa,yarinya karama Sai kissa iri iri,ya daga hannun sa sama yace "ya Allah ka kawo min wannan lokacin da gaggawa"

Sannan ya shige motar sa ya shiga cikin gidan su da already maigadin ya bu'de gate din,don tunda yaji tsayuwar motar sa a kofar gidan su Aleena ya yi Sauri ya bu'de gate din yana jiran doctor ya shigo ciki.

Shalelen Alhaji kuwa yana makale a adaidaita sahu zafi ya ishe shi ga rana,yana kallon su da dum abinda yake faruwa,Sai dai ba ya jin abinda suke cewa.

Yana ta Allah Allah Aleena ta shiga gidan su,don kawai ya ga Ina ne gidan su,yana Kuma Kara jin haushi da tsanar Ashfaq a zuciyar sa don ji yake kamar ya je ya shake shi ya hutada tsanar da yake masa.

Tana ganin Aleena ta shiga cikin gida cikin gida,yayi hamdala tare da barka na yau dai karshen wahalar sa ta yanke na neman gidan su yarinyar nan.
Yayiwa mai adaidaita sahu magana cewa su tafi tunda ya gano gidan su yarinyar ya mai da shi in da ya dauko shi wajen motar sa.

Mai adaidaita sahun ya amsa masa cikin irin muryar su ta Yan yaku😂"ok oga da girman kujerar ka,amman fa Sai zan dan ce wani abu,fa Sai dai kayi hakuri,gaskiya ba karamin so ka ke yiwa yarinyar nan ba ya kamata a karamin wani abu man akan abinda za a bani Sai na kara addu'a akan Allah yasa ta zama ta ka gaba daya"

Maganar Sai ta bawa Annur dariya sosai yace" to bari muje Sai naga ya za ayi amman don't say anything to me right now pls"
Ai fa an zo wajen oga ban ma fa San abinda ka ce ba na karshen,nasan dai pls Sai kuma right shine rubuta ko? Da yake nima Ina Dan ji turancin small small
Annur ya karasa dariya yace lallai kam haka ne,
Haka dai yayi ta samun Annur da hira wani lokacin ya amsa masa wani lokacin Kuma ya ce eh ki a'a,yana Kuma mamakin kansa ya shine a adaidaita sahu har Kuma yana hira da mai Dan sahun abinda bai ta'ba yi ba a rayuwar sa.har da suka isa wajen motar sa.
Amman Sai me ba mota ba labarin ta,
Ya tsaya ya waiga ya waiga Bai ga motar sa ba a wajen,ya Dan juya wajen mai Dan sahun yace ai kamar an muka bar mota ta ko?

Mai Dan sahun ya danna wani ashar yace wallahi wani mai sa'a ya tafi da ita,wayyo Allah dama ni ne na Sami sa'ar nan da na ji da'di a rayuwata,wayyo Allah har da hawayen sa Sai kace motar sa aka sace😂.

Annur ya koma cikin adaidaita sahu ya zauna don zafi ya ishe shi,mai Dan sahun ya dawo ya zauna wajen yana ta share kwallah
Annur yace "to kaime aka yi maka na kuku kamar Kai aka daukewa mota mtssss ya ja tsaki"

Ba dole nayi Kuka ba tunda bani na samu garabasan nan ba

Hmmmm to yanzu Sai ka Kai ni gidan sanata Alhaji,Sai na baka kudin aikin da kayi min ko

A razane ya kallo Annur yace haba ko da naji Mana ashe Kai Dan gidan sanata Alhaji ne shiyasa Mana naga baka wani damu ba da rashin motar ka,Sai ta wani sunkuya yasa hannun sa biyu ya hau sarawa Annur yana cewa cau-cau-cau oga,Yan zu kuwa zan Kai ka don ba Wanda bai San gidan ba a fad'in kano

Annur dai yayi tagumi don surutun ya ishe shi ,
Suns isa gidan yace masa to Ina zuwa bari na turo a kawo maka ko,to ba wani abu oga godiya nake.

Yana shiga yace wa baba maigadin Kai biyoni nan ka karbi saki ka kaiwa mai adaidaita sahu a waje,Dan tsohon yace to ya I bayansa.

Mai Dan sahun yana jira Sai yaga budewar gate maigadin ya fito da rafa ta dubu dubu ya mika masa

Ai Sai yayi wani tsalla ya dire kasa yace wallahi yau na tashi aiki,maigadin zai juya ya tsayar dashi yace tsaya ka Sami rabonka Kai ma baba ya cire guda daya ya bashi yayi godiya ya koma cikin gidan tare da rufe kofa.
Yau Allah ya ha'da ni da arziki an bani wani abu daga cikin hakkina tunda dai kudin mu ake data,sannan yayi gaba.

Annur ya zauna yana planning yadda zai yi ya shawo kan yarinyar da iyayen ta gaba daya da Kuma irin abinda zai nata idan yaje wajenta.
**************

07038185042

Comment
. comment

Share,vote and follow me on my wattpad.

Tanks to you all my fans 😘😘😘😘🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now