page 8

1.4K 88 1
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahamanur Rahim

Lallai idan Allah ya barka maka mahaifiya a raye ba karamin ni'ima da gata yayi maka ba sai Kayi kokari ka kyautata ma ta kafin Allah ya dauke kayan shi

Allah Kayi gafara Ga mahaifiyata don albarkar annabi

Masu kirana da yi mini text da sauran masoyana dukkan Ku ina miko gaisuwa ta gareku

Adda ramla mai dambu bazan fa man ta da ke ba

Mallakar Jamila(Maman Amir)

Wattpad jami1020
*****************
   P8
Not edited

  Cikekken asalin su aleena shine mahaifin su Abba sunan shi malam nura abubukar yan asalin jahar kano ne a wata unguwa da ake kira hotoro mahaifinsa Malam abubakar malami ne dattijon kirki masani akan harkar addinin musulunci yana da kawaici da sanin ya kamata hakan ya janyo duk unguwar ana mutukar girmama shi yana da mata biyu uwargidan ita ce ladidi  bata da kirki ko kadan ga son abin duniya hakuri kawai makam yakeyi da ita a sakamakon haka ya kara aure yaran ta uku biyu maza daya mace babban sunansa Auwal na biyun sani sai mace ana kiranta daAsma'u duk kan su ba suyi yo halin uwarsu ladidi ba,

Sai Matar sa ta biyun mai suna Aisha ita ce Amarya  ya ranta biyu babban yaron ta shine baban aleena wato Malam nura sai kaninsa Ahmed duk ka yaran Malam abubukar sun task cikin hazaka da ilmi amman duk nura wato baban aleena ya fish kokari da farin jinin jama'a karatun su ya tsaya ne iya secondary school ba Wanda ya cigaba suna fada harkar kasuwanci India Allah yasa wa su nura da Ahmad albarka sosai don da yaran shago ne har kuma dai ubangidansu ya yaye su aka sallame su da kudin mai tsoka nan suka hada suka bude nasu shagon Wanda abin bai yi wa ladidi dadi ba kwatakwata don ta so ace yaranta ne a matsayin su

Haka rayuwa yayi ta cigaba ya zamtu nura ne take daukar nauyin gidan ma gaba daya don tunda yayyin sa sukayi aure basa wani kula da gidan sai dai suce abubuwa sunyi yasa suma ta Kansu sukeyi rashin taimaka iyayen su da basayi zai abin nasu ya ke tayin kasa har ya zamtu su din ma sai nura ya taimaka musu shine ya zama jigo a gidan hakan kuwa yana yi wa Malam abubukar dadi shiyasa take yawan yi mishi addua da sama sa albarka(yan uwa ya kamata murinka neman albarka iyaye da taimaka musu ko da da Abu ne Dan kalilan baka san da me Allah zai saka maka ba don kai ma wata rana zaka Haifa zakasu kuma aji kanka a tausaya mama)

A haka har Allah ya hada sa da Zainab soyayyay mai karfi ta kullu a tsakanin su akaje aka nema masa aurenta a unguwar gandu dake nan cikin kano bayan sunyi aure Allah ya azurta shi da Yara biyu dukka mata  aleena da afnan  yaran Suna samun gata sosai a wajen iyayensu aleena Tana zuwa private school tun kafin a haifi afnan Allah ya bata kwakwalwa da anyi karatu da dauke karatum nan malaman makarantar Suns sonta da ko wata gasa za ayi da wata makaranta aleena suke zama daliba suna ta so suyi kawance da ita ta ki yarda don aleena miskilar yarinya ce ba ta da yaran surutu sannan ka tsafta abinda ma yafi Jan hankalin daliban suyi kawance da ita shine kyakyawa sosai ajin farko sai kace aljana fara ce gas kamar yadda na fada a baya

Lokacin da ta gama primary lokacin aka haifi afnan tayi murna sosai don ta sami yar uwa ita ma za tace Tana da kanwa

To abin ya farune lokacin aleena tana aji biyar na sakandiri suna shirin zana jarabawar tafiya aji shidda shekarunta goma sha hudu aka wayi gari shagon malam nura ya kama da wuta kuma alokacin kwana biyu ke nan da ya dauki duk ka kudinsa ya kara saro kaya yasa a shagon ko da aka zo aka gaya masa da yaje shagon ya gani komai ya cinye ba abu daya da za a dauka ya yi amfani kawai sai ya zube a wajen ya suma aka tafi da shi asibiti ummi Ku wa kuka kawai takeyi tana fadar innalillahi wa inna ilaihir rajiun

Sai da suka kwashe wajen wata daya a asibiti sannan aka sallamo su kuma duk abinnan kaninsa ahmadu shi ke kula da komai sauran yanuwan su kawai ba abinda ya shafe su bai fi suje su duba shi sai daya a sati biyu.

Ko da suka dawo gidan abubuwan duk sun cunkushe babu kudin da za a dinka wasu larurar da su abincima ya zama sai gagare su sai sukayi shawara da ummi asiyar da gidan da suke ciki sai a siyi wani ragowar kuwa sai ya gwada sai da wani abun to haka kuwa akayi suka sami gida a unguwar tudun Yola gidan ma duk ya rube suka Dan mi shi gyara suka shiga cikin sa to amman har yanzu Abba ba cikekkiyar lafiyar da zai iya fita ya yi sana a dan ragowar kudin nasu ya kare Ga kudin magani Ga kuma abinci karshe dai dole aleena suka daina zuwa makaranta kawu ahmadu  shi ke kula da komai karshe dai da aka kai Abba asibiti aka rubuta musu wasu maganun nuna nasu tsada har dole suka zauna a guda suka zubawa sarautar Allah ido mal abubukar yakanzo ya duba shi to shima tsufa ya zo da kyar yake akawa

Ita kuwa aleena abin ya tsaya mata a arai Ga rashin lafiyar Abban su Ga rashin zuwa school don Allah yayi ta da son makaranta da ta zauna ba tunanin da takeyi sai ita kuwa me zatayi ta samowa Abban su kudin magani a haka har Allah ya kawo hajiya Khadija wato mom
***********

Aleena tana gudu ashfaq yana bin ta a guje abin yana kara bata masa rai ganin ya kasa kamata don bama karamin gudu takeyi ba ya kai hannu ke nan zai damketa ai sai yayi tuntube da wani dutse hakan ya sashi run tsirawa har ya tade kafar ta ta fadi kasa wanwar shima ya kwanta warwar kusa da ita jikin su yana gugar na juna suna ta nishin wahala tunda duk kan su ba su sa ba da haka ba wajen second 20 aleena yayi sau rin mikewa ya jawo hijabinta shima ya mike tsaye ya jawota jikin shi ya daga hannu zai kifa mata mari ta rike hannun ta kai bakin ta ta gartsa masa cizo saboda tsabar zafin da yaji bai San lokacin da yasa kafa yayi bol da ita tasa kara  kuma dagota ya shaki wuyan ta ya tsaya yana kallon fuskarta monti daya yace ke wai wacce irin yarinya ce ke fitinanniya duk ya yadda na so nayi hakuri sai kin kara ingizani  tunda nake ban taba haduwa da yarinya irinki marar tarbuya ba iyayenki nasu ko ya miki tarbiyya ba aleena ta dago ranta ya kara baci na farko ya rugumeta sannan yana cewa bata da tarbiya iyayenta nasu ko ya mata tarbiyya tabb gashi rikon da yayi mata ba na wasa bane tayi tayi ta kwashe ta kasa sai shakar numfashin juna sukeyi sai kawai idea ta zo mata yana can yana kallonta tasa kafa ta daki gaban sa wayyo Allah ta kasheni ya sake ta ya rike gaban sa dukka da hannu biyu ya durkusa kasa ita ko ganin ya sake ta ta kwasa a guje ta sha kwana ta fada gidan su tabar shi a duke a kasa

Daga baya yaji ana tayi masa horn a baya ya kasa ta shi mai horn din ya gani ya fito yazo wajensa haba bawan Allah ya zaka zo tsikiyar titi ka tsugunna ai bakyau haka da sai ka koma gefe mana ashfaq dai da ya tabbatar muryar amir ce ba kuma kamshin sa sai ya dago da kansa dalla Malam in ba zaka taimakamin ba ka matsa ka bani waje amir yayi surrender ya gwalo ido yace ashfaq sai kyalkyalkyal .... Ya rinka dariya har da rike ciki yana dukawa kasa
****************

07038185042

Comment
Comment
****

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now