page 23

1.2K 70 8
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Daga jarumai writers association

Allah ka jikan mahaifiyata kayi gafara gareta ka yafe mata kurakurenta ka kuma haskaka kabarin ta kasa tana cikin ni'imar ka ya Allah

Allah ka bawa mahaifina lafiya  ka sa ka masa da alkhairi duniya da lahira

Allah ka raya mini yarana ka basu ilmi mai amfani ka kuma ba su lafiya ya yaye mana wannan zazzabi da ya addabi mutane

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P23

Yana isa kofar gidan ya tsaya yayi sallama ya kara yin sallama ummi ta ce wa afnan ta je ta duba ta gani wanwne don ta ji muryar kamar ta ashfaq afnan ta fita aguje tana isa taga ashfaq tace la mai kyau ina kwana lafiya lau kina lafiya lafiya to maza ki je ki cewa ummin mu gani na zo to mai kyau amman kwalliyar nan ta yi maka kyau fa hahhhh shima sai yayi dariya to nagode oya jeki gaya mata gani na zo sai ta shige gida a guje


Ta sami ummi  a falo ummi ga mai kyau ya zo yace in gaya miki yana kofar gida to alhamdulillahbarka da ma shi muke ta jira abban su ka ji ga shi nan ma ya zo alhamdulillah in ji abba ta dauko hijab ta saka tace to je kice masa ya shigo kin ji 'yar albarka to ummi ta fita taje ta same shi  a tsaye ummi ta ce ka shigo mai kyau to kawata muje kiyi min ja gora  a'a  ka shiga ciki mana no no ki fara shiga na bi bayan ki kin ga ni kunyar su  ummi da abba nake ji to me yasa kake jin kunyar su ai ke ba zaki gane ba ne da na gaya miki to ni dai na san me ma ake cewa wanda ya auri 'yar gidan wasu sai yayi subutar baki yace siriki yauwa to shi nasan yana jin kunyar iyayen yarinyar ko to naga kai kuma baka auri ko ba da ma ace zaka auri ya aleena ne to da sai nace kana jin kunyar su abba ko ta fada tana dan ya mutsa fuskar da salon tunani to in na ce zan auri ya aleena to zaku bani ita ai kawai sai ta kama tsalle tana ta  cewa wallahi da kun haifo yara masu kyau don Allah mai kyau ka auri ya aleena afnan mu shiga ciki kinji ni kar na biye ta taki don hirar ki ba ta tsayawa kamar amira ta kyalkyale da dariya to muje suna shiga ciki yana tunani a zuciyar sa irin katobarar da yayi da yace wai zasu bashi aleena ya aura kar fa taje ta gayawa iyayen ta hooo ho hoo me na aikata ke nan

Nan suka kara sa cikin gidan yayi sallama ummi ta amsa tare da cewa ka shigo ciki mana sai kace bako ashfaq ya dan yi murmushi yace na gode ummin mu ina kwana ya jikin abban da sauki sannan ya juya wajen abban yana gaishe shi ya kuma yi masa ya jiki yace da sauki to Allah ya kara lafiya amin ashfaq yana fada ya na dan kama kirjin sa da yake yi masa ciwo to ashfaq bari na kawo maka abin kari irin namu bansani ba ko zaka iya cin ci mar mu lah ummin mu wallahi a koshe nake aleena ta cika mana ciki da abinci alhamdulillah amman  a wajen ki ta koyi girki lo ummin mu ummi ta sa dariya cikin farin ciki jin an ya bi 'diyar ta  to ummin in kun gama zamu iya tafiya da abba din eh ya kammala tun dazu kai kawai yake jira to ba komai nima na dan tsaya yin wani abu ne  kuyi hakuri a haba ba komai to nagode muje ko abba.

Ummi ta taimaka masa ya tashi tsaye ashfaq ya karbe shi daga jikin ummin ya jingi na sa a jikin sa to sai mun dawo ummi to Allah ya bada sa'a  ya kuma kiyaye hanya yasa a dace amin suka fita daga gidan ya bude wa abba bayan mota don ya samu ya dan mike da kyau yauwa nagode Allah ha shi maka albarka amin abba ya zagaya ya koma mazaunin driver ya ta da motar sai asibiti.

Suna shiga direct ya wuce da shi office din sa ya zaunar da shi ya bude frige din sa ya dauko masa maltina da peak milk ya hada masa a cikin cup ya mika masa abba ka dan sha wannan kai haba ashfaq har da hidima kuma bayan hidimar da ka ke kokarin yi mini haba abba don na baka abu kasha shine na hidima ko wani ne ma zan iya bashi balle kuma kai da na dauke ka kamar mahaifi na ga ka makocin mu abba ko yaji dadi har cikin ran sa yadda ashfaq yake girmama shi

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now