page 5

1.7K 102 0
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka gafartawa mahaifiyata ka kuma bawa mahaifina lafiya da duk marasa lafiya.

  Allah ka shirya mana yaran mu da zuri'ar mu ka karemu daga sharrin duniya.
  
   Sakon gaisuwata ga adda ramla, Maman shureim da Maman aleena.
   
Mallakar Jamila(Maman amir)
     
Wattpad@jami1020
*****************

         P5
Ashfaq yana kawowa amir duka yayi sauri ya durkusa ya sami Kujera ta ya za ayi kace min Wannan yarinyar Mara tarbiya dirty girl itace zata zama Amarya ta wait ma let me ask you when did I told that am going to get marriage uhhh yana fada yana huci amir kam sai kyalkyala dariya yake yi ya ba shi amsa da gashi yanzu kana gayamini ya gatsine fuska haushi ya cika ashfaq yace wai kasan me yarinyar tayi mini in a serious mood sai jikin amir yayi sanyi yace doctor muje gida tukun sai muyi magana yanzu ana tayi mana horn a baya mtsss ya cigaba da tuki

Har suka isa unguwar su da ke Jan bulo dai dai wajen wani makeken gate naga sun tsayar da motar sunyi horn nan maigadi yafito yana ganin motar a guje ya kara sa yana ran kwafawa yana ranku ya dade barkan Ku da zuwa yau dai ashfaq ko kala bai ce masa ba balle ya dan ba shi yar kyautar da yake yi masa duk lokacin da yazo sai amir ne kawai ya amsa masa ya dawo ya bude musu wawakeken gate din tun a harabar farfajiyar nasan cewa Wannan gidan manyan mutane ne daga can bangaren na hango parking space cike da motoci kala kala sai kace wajen sai da motoci a tsakiyar gidan akwai wani katon round da aka kawata shi da flowers gwanin ban sha'awa  sai fidda kamshi sukeyi gidan part biyu ne kowanne kuma yana da nashi BQ  a gefe nan na tuno fa ashe gidan Senate ne wato Senate Auwal jibril kura mahaifi ga amir

Nan suka sha round suka je wajen parking space sukayi parking sai kawai ya kife kansa a sitiyari amir yayi shuru duk da Wannan ba Abu ne sabo ba a wajen ashfaq Amman na yau yafi na kullum in ma yana miskilancin na shi wani lokacin yana Dan murmishi ya dan saukar da muryar sa yace doctor what is happening to you can you imagine yau wata mahaukaciyar yarinya ce ta mareni har sai biyu a fuskata nan dariya ta tasowa amir ya dan danne yace garin yaya ya akayi mahaukaciya har ta zo wajenka ta mareka he was trying not to laugh mtsss ba wai mahaukaciyar gaske ba fa mtsss ya kara Jan tsaki nan ya kwashe yadda sukayi da aleena ya gayamasa ai kuwa me amir zai yi in ba dariya ba ya rinks kyalkyakewa da dariya  gaskiya yarinyar nan ta ciri tuta tab ta dubi  santalelen saurayi Wanda yan mata ke rubibinsa da San ya kula su amma ta mare shi hahhhhh...wayyo cikina to kai kuma kawai sai katsaya ka kasa daukar mataki kyalkyal kyal ya kara kwashewa da dariya ashfaq kawai tsayawa yayi yana kallonsa  karshe kawai ya rufe shi da duka shi kuwa yayi wuf ya fito daga cikin motar shima ya biyo shi suka rinka zaga  gidan maigadi yana zaune yana kallon su yana murmushi abotar su na burge shi sosai dai dai lokacin hajiya Umma tafito zata rakawata kawarta da tazo duba ta tsaya Tana kallonsu tana dariya ta tabbata amir ne ya tsokani ashfaq amir yana ganin su yayi kansu ya boye a bayan umma yana ki ceceni Umma yaron ki zai min duka Umma tana dariya tace a gwara yayi  maka dukan am sure cewa kai ka tsoka ne shi
 
Shi ko ashfaq yanajin abinda Umma tace sai yayi murmushi yace umma kyale shi zamu hadu ne tace  Ku shiga ciki kaji doctor ina zuwa suka shiga tana jin dadin yadda suke abota
****************

Washegari ummi ta shirya zata je wajen hajiya Khadija ta rike hannun afnan sai ga ahmadu kanin mahaifin su aleena ya shigo don duba yayan nasa afnan tana ganin shi saki hannun ummi tayi wajen kawun nasu aguje ya sungumeta yana juyi da ita tana ta dariya ya ajiyeta ta kawu ina wuni lfy lau yar kawu ya dauko biscuit a aljihu ya bata ta karba tana tsalle tana godiya mamansu ina zuwa haka wallahi zan shiga nan makotan mu ne yanzu zan fito in sha Allah to ba laifi sai kun dawo suka wuce shi kuma ya shiga wajen yayansa.

Ummi ta kwankwasa gate din gidan su ashfaq maigadi ya bude ya ya dai hajiya na zo wajen hajiya Khadija ne ta San da zuwanki ne eh to shike nan wuce suna shiga ummi tayi tsaye tana kollon gidan yadda ya tsaru tun a waje ina ga kuma an shiga ciki ganin ta rasa in da za ta dosa sai maigadin yace muje hajiya ya kaita har bakin komar shiga falon sannan ya dawo bayan ya danna bell dukkan su suna zaune falo ba Wanda ya tashi acikin su can sai ashfaq ya sauko kasa dai dai lokacin da ummi ta kara kasadar danna bell din ya kalle su yaga ba wacce tayi motsi kowacce sai basarwa takeyi yace ba kwaji ne fuska a hade sai dayar da tafi zakewa cikin su biyun don dama Allah Allah take ashfaq ya sauko don ta ganshi taji dadi aranta tace ya ashfaq naga ga Amina a zaune itace karama ita ya kamata aje ta bude kofar Amman tunda Kayi magana bari naje na bude mtss yayi tsaki ya nufi kofar a zuciyar sa yace wahalallu kwayi Ku gama ya barta a wajen ya bude kofar ummi tana ganin an bude ta dan matsa kadan ashfaq ya kalleta yace sannu shigo mana fuskar sa ba yabo ba fallasa dama afnan na bayan ummi

Ummi ta jawo hannun afnan ya dan matsa suka shigo sannan ya rufe kofar yace bismillah Ku zauna dai dai nan afnan ta ganshi ai sai ta saki hannun ummi tayi Kansas aguje tana cewa mai kyau ummi ga mai kyau da nake baki labariummi tana murmushi shi kuwa sai yayi sauri ya dauke ta yace a kema ai mai kyau din ce ni fushi nake da ke fa tace to me nayi maka ta fada tana dariya yana dan dariya yace na Baku sweet kinki karba ai sai ta zaro ido tace Kayi hakuri nagayama ka ummi zata dake ni in na karba haka na yaya aleenata fada a shagwabance yayi murmushi sai ya juya wajen yan matan nan guda biyu yace daya a cikin Ku taje ta kirawo mom tayi bakuwa fuska a hade kamar ba yanzu ya gama murmushi ba nan da nan suka rinka yar rige rigen zuwa saboda ya ashfaq ya sasu aiki sun tafiya ya juyo wajen afnan da murmushi yace to kawata bani labari afnan ta fashe da dariya ummi kuwa a zuciyar ta race kai Wannan yaron ya ci sunan sa mai kyau akwai kuma kamun kai ya jiyo wajenta yace ummin mu ina wuni
***********
07038185042
Comment
Comment

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now