page 30

1.1K 66 31
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Zauren jarumai writers associated

Allah ka yafewa mahaifiya ta ka jikanta da rahama kasa aljanna ce makomar su.

Allah ka bawa mahaifina lafiya ka saukaka masa ya Allah.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P30

Aleena tana kwance kan 'yar katifar ta,  tana tunanin duk abinda yake faruwa a tsakanin su da ashafaq, take tambayar kanta da ko dai ashfaq sona yake yi ne? don yadda yake nuna kishi da damuwa akai na faaa hmmm anya kuwa ? sai wani bangare na zuciyar ta yace ta ya za ayi ashfaq ya so ni, ni da ba kowan kowa ba, bani da aji ko kyawun da zai so ni fa hmmm ka da ki yaudari kan ki aleena, kawai kiyi addu'a Allah ya baki miji nagari,  wanda zai so ki a yadda kike da kuma talaucin gidan ku.to amman fa ashfaq  fa ya kyautatama na fa wallahi ji yadda yake dawainiya da abbana ta wajen lafiyar sa da gidan ma kan shi gaba daya, gaskiya ya kamata na fara kyautata masa fa, na nuna masa nima farin cikin da yasa mu da family dina yes in sha Allah daga gobe zan fara yi masa biyayya zan fara kyautata masa in sha Allah har zuwa lokacin da zai yi aure ya bar gidan gaba daya.

Sai kuma gaban ta ya fadi jin ta ambaci aure ke nan anan gaba zai yi aure ya bar gidan, na shiga uku to wa zai aura ne wacece matar ta sa? Sai ran ta ya baci, ta ja wani irin tsaki da har sai da afnan da take barci  ta dan juya jin wani sauti na daban.gaskiya ni ba zan so yayi aure ba yanzu ta zumburo bakin ta kamar akwai wanda yake kallon ta, saboda me ba kya so yayi auren yanzu? Zuciyar ta ke tambayar ta ni dai ba yanzu ba, dama zai bani dama da na samo masa yarinya kyakykyawa mai hankali da sanin ya kamata 'yar gidan masu kudi ita ma irin sa, nima na kyautata masa.to ke ba ga kinan ba  sai ki aure shi ba kawai to ai ba ya so na kuma ba zai ma taba so na ba ni na sani hmmmm ki dai yi tunani dai in dai ke kina son sa ai shi ke nan ko? Hmm su aleena manya duk hirar nan da takeyi acikin zuciyar ta takeyi fa.ni dai na ce ikon Allah na cigaba da recording.

Sai ta tuno lokacin da ta gaya masa cewa tana da saurayi Aliyu kuma shi za ta aura, yadda ran shi ya baci da yadda ya biyota a guje har suka fado daga bene sai ta fashe da dariya, don sai yanzu abin ma ya rinka bata dariya, hhhhh
*******

Washe gari da safe ne kowa ya halara a falo tun da akayi sallar asubah ana ta faman zuba hirar yaushe gamo, family din dai da ka gansu kasan suna cikin farin ciki da annashuwa da murnar dawowar  dad din na, sun kuma saba da idan yayi tafiya ya dan dade, to washe garin ranar da ya dawo dukkan su zasu hadu a falo suyi ta hira gwanin sha'awa.

Amira har yanzu kuwa mom ta na kan tashin ki da safe yin girkin?dad yake tambayar amira,  lah dad ai namanta ban gaya maka ba, uhumm ina jinki nima na samu wata sister sunan ta aleena, dad tana da kirki sosai gata mai kyau dad, makotan mu ne fa, wallahi dad ina son ta sosai saboda she is simple and she know what she is doing.

Tare muke girki ma da safe da rana in ta zo tun da safe sai da yamma zata tafi shima don tana zuwa islamiyya ne.tun da ta sako maganar aleena mutane biyu a falon suka mai da hankali kan abinda take fada, shi ashfaq yana jin dadi amman yana wani basarwa kamar hirar aleena da take yi ba ta da wani muhimmanci a wajensa,  a daya a bangaren kuwa amatullah sai harara take ta watsowa amira tana Allah wadare da maganar da amira takeyi salon shima dad ya fara son aleena mtsssss ta ja wani mugun tsaki ta tashi ta bar falon.

Duk suka bi ta da kallo,  dad yace "lafiya kuwa me aka yiwa amatullah haka ta tashi cikin fushi? ko kin mata wani abu ne amira nasan halinki ni bansan me ya sa bakwa jituwa ba kuna 'yan uwa kuna girma maimakon abu ya ragu amman sai karuwa yakeyi"

To kai ma dai ka fada su suka sani ai ina idan sukayi aure ai sayi hankali ko? To Allah ya kyauta,wai wacece aleenan amiran ne ko ita ce wacce kika bani labarin su jiya? Eh ita ce fa ban ko gama baka bama mukayi barci sai suka sa dariya dukkan su, suma yaran nasu suka bisu da ta su dariyar.

Nan mon ta cigaba da bashi labarin su aleena har zuwa kai abba asibiti da ashfaq yayi.dad ya kalli ashfaq yace kayi kokari my son haka aje son mutum ya kasance cikin taimakon marasa karfi idan yana da hali, Allah ya shi maka albarka ta baka mace tagari amin mom ta amsa.

Yauwa son ya maganar da mukayi ne ta maganar aure kasan dai na baka enough time ko? Ashfaq ya sunkiyar da kansa kasa nasani dad but in sha Allah wannan karan bazan baka kunya ba, ina kan searching har yanzu.dad yasa dariya searching kuma au har yanzu baka samu ba ke nan balle har ku daidai ta har ta kai maganar aure ko,to ba matsala ina ga  mom wannan yaron naki sadaka zan ba da shi kawai a huta.

Amira ta sa dariya sadaka kuma dad lallai su ya ashfaq anyi kwantai hahhhh ahfaq ya daure fuska yace ke ina wasa da ke ne daga ana yimin magana sai ki wani sa dariya ya wani tsare gida don kada ma ta kara tsokanar sa don yasan iyayen nasa ita zasu goyawa baya. Ai gaskiya ta fada idan ka yi zuciya ka
kawo mana matar aure nan da wata daya, suka kara sa dariya har da shima sai da yayi murmushi kawai.

Ya dan gyara zama dad mom dama ina son magana da ku, to muna sauraran ka hmmm dama dama maganar makotan mun nan ne suwa ke nan inji mom, gidan su afnan mana mom, ok gidan su aleena to ina jin ka meya faru kuma,  dama mom naga za akoma school ne kuma kinsan yaran gidan basa zuwa school saboda halin da suke ciki kuma naga ya kamata ace suna zuwa makaranta musamman ma babbar, ikon Allah yanzu aleenan ce ba zaka iya kiran sunan ta ba,ko sunan ne yake yimaka wahala? Mom ta ke tambayarsa da salon tsokana  don ita tana zargin kamar yaron nata son aleena yake yi amman dai za tayi shuru taga iya gudun ruwan sa.

Ba haka bane ba mom kawai dai ina manta sunan ne kawai, to yanzu kace aleena muji so that gama ba zaka manta sunan ba kai ka fada ma kamar sau uku muji ya gwalo ido yace mom yes da gaske nake yi oyya muna jinka don sai ka fada fa ashfaq yayi shuru yana tunanin yadda zai fadi sunan ba wai bai iya bane amman kawai zuciyar shi ce take wani irin bugawa to amman ya zaiyi dole ya fada yasan mom wani lokacin in ta kafe akan magana daya ta fa kafe kenan ok to zan fada uhuumm bakin sa na rawa ya fara fadar sunan  dad kam zuba masa ido kawai yayi yana karantar yanayin 'dan na sa sai ya kalli mom suna hada ido suka yiwa juna signal mom tayi murmushi,  tace to mun ji cigaba da maganar ka,ya dafe kirjin sa wajen zuciyar sa yace  in short dai gani nayi kamar ya kamata suma mu sa su a makaranta sai su rinka tafiya da amira ko,  ko ya kuka gani?
*******************

07038185042

Comment
Comment

Am so sorry for the short page

Har yanzu banyi settling ba, amman soon , zaku jini in sha Allah.

Tanks to all my fans

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now