Page 9

1.3K 77 0
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka gafartawa mahaifiya tare da Nafisa sa'ad bakori ya Allah ka haskaka kabarin su da sauran musulmai baki daya

Allah ya ba ki lafiya mai dambu

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad jami1020
***************

P9
Not edited

Aleena tana shiga gida ta da hannu ta rufe kofar gidan nasu har da sa sakata ta tsaya ta dan daidaita nutsuwarta sannan tayi sallama ta shiga cikin gidan ummi ta tarar atsakar gidan ta saki baki tana kallonta ke lafiya kike aleena meya faru da ke haka ta ya mutsa fuska har da hawayenta tana cewa ummi faduwa nayi a cikin kwata shine duk jiki na ya baci da kwata tana maganar tana hijabin ta tana kara jin haushin yadda Wannan mutumin yasa ta yiwa iyayenta karya don Wannan shine karya ta farko da tayiwa iyayenta to Allah ya kyauta ya kiyaye gaba sai ki kula saboda gaba ki cire kayan naki kusa wasu ki wuce islamiyyar ta zaro ido in wuce kuma ummi yaushe har na cire har nayi wanka sannan na wuce ai na makara wallahi a zuciyarta ko tace karan hauka ne ya cijeta da zata fita yanzu taje ta kara huduwa da basamudan nan

Bayan ta gama cire kayan dukka taje tayi wanka duk sai kyankyamin jikinta takeyi ta shafa mai yasa wasu kayan ta fita ta wanke wadancan ta dawo ta zauna tayi shuru tana tunani ta shiga uku fa kar dai basamudan nan a unguwar nan yake ya takuramin yace sai ya rama to ni da na buge shi a wajen nan karfa ko nayi masa lahani fa oh na shiga uku meya faru kike cewa kin shiga uku ki gayamin gaskiya aleena bansan ki da karya ba

Sai kawai ta fashe da kuka ta dawo kusa da ummin tana gayamata abinda ya faru a hankali don ka da su tayar da Abba da yake barci yanzu me ke nan kikayi aleena ke fa mace ce ta ya za ayi ki biyawa namiji har kice Sai kin rama abu karfin ki da na shi ba daya bane ba fa to ni dai ba ruwa na daga yau ba ke babu shi in kin ganshi a hanya ko kula shi kar kiyi ko da ya takaleki kuwa kinji abinda nace ko naji ummi kiyi hakuri bazan sake ba bakomai ya wuce

Yauwa Allah yayi miki albarka amin Kinsan gobe zaki fara zuwa wajen aikin ko karfe shidda za ki rinka tafiya saboda ke zaki rinkayi musu abincin to ummi Allah ya nuna mana don Allah ki kiyaye aleena suk da nasan baki da matsala kar kiyi abinda zaki zubar wa da kanki mutumci ki zubar mana da mutunci kinji in sha Allah ummi karki damu to tashi kije ki hada miyar ce tunda ba batun zuwa Islamiyya hhhhh to ummi ita ma tayi murmushi.
********

Wai ba zaka taimakamin ba ne ba ka tsaya kana ta faman yimin dariya are you mad like that girl Sai amir ya tsayar da dariyar ta shi ya ce wait me ya faru ko yau ma kun hadu da ita ne yana gumtse dariyar sa mtsss yayi tsaki yana kokarin mikewa Amman dukka hannayen sa suna dafe da gaban sa Sai lokacin amir ya lura da haka yayi sauri ya kara sa mikar da shi in serious tongue ya ce meya faru da wajen duka na fa tayi a wajen kamar zai yi kuka ya fada kaiii  is she mad ya za ayi ta dake ka a wajen batasan tana ita kashe ka ba ne yarike suka koma wajen motar amir ya bude masa gaba sannan ya koma ya zauna ya fara tuki don su kara sa gidan su ashfaq din yana jinjina al'amarin nan tsakanin aminin sa da yarinyar nan.

Bayan maigadi ya bude musu gate sun shiga yaje wajen parking space tayi parking ya kashe motar ya fito ya budewa ashfaq kofa ya fito yace to kai doctor dole fa ka saki hannun ka don ba zai yiwu mu shiga da kai a haka ba kana rike da wajen nan yayi tsaki kai ba ka San yadda wajen nan yake min zafi bane in muka je wajen kofar Sai na saki hannun OK

Suna isa kuwa ya saki hannun amman fa yana jin azaba yana fada a zuciyar sa da kin kashe ni fa iyyii mad girl mtsss ya kara Jan tsaki aka bude kofar suka shiga ciki da sallama Amina ta da ihu ya ashfaq me ya sameka haka Sai kuka saboda ba karamin so take masa ba shi kuma yaki ya gane ko in ce yana sane yake basarwa amira da ke kitchen ma ta fito mom ma ta sauko kasa saboda ihun da Amina tayi ashfaq ko tsaki yayi ganin ta tara masa mutane aka da salin alin zai wuce zuwa dakinsa amira ta ce ya ashfaq what happened ya harare ta ganin haka amir ma ya harare shi har da mintsinin shi akan me zai wa amira haka mom ta zuba mishi ido yace mom ba komai fa kawai faduwa nayi ne a kasa kwatami ta dai zuba mishi ido ba tare da race komai ba

Ta kalli amir to Ku wu ce mana kuje Ku wanke jikin Ku haka nan OK mom amir ya fada ya rike ashfaq suka hau dama zuwa dakinsa shi kuma zai  shiga toilet amir yace Malam tsaya na wanke hannu na tukun nan bayan yaje ya wanke hannun yace da ashfaq bari naje na dauka motar ka Sai na siyo ma magani ko OK kawai ya iya cewa ya shige toilet

Ya sauko kasa ya leka kitchen ya ga amira yace lil sis yau me ake dafa mana ne Sai kun zo ci sannan zaku gani albishirin ka ya amir goro to mom ta samo min yar uwa da zata rinka ta yani girki wow Amman dai tana da tsafta ko sosai ma gata very beautiful sai ma ka ganta yace good yanzu bari na Dan fita ina zuwa yanzu zan dawo in sha Allah zan karbo masa magani don yanzu yana iya lanjare mana ta da dariya ai wallahi ya ashfaq ya fiye ragwanta sai kace mace ya ma kamata kiyi aure mu huta da dawainiyarka sai yayi shuru ya tsira ma ta ido yana mata wani iron kallo tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa don bata iya jure iron kallon nan da take mata ta kan rasa gane me irin wannan kallon take nufi me yake nufi da ita gashi bata da wata shakikiyar kawar da ta amince mata da data gaya mata ta fassara mata ganin ta sauke kanta kasa said ya saki murmushi mai fitar da sauti yace ya dai lil sis ya kikayi shuru it a dai bata ce komai ba idanta na kasa bari dai naje na dawo kinji ki kula da kanki kasa ki kone wajen girki kiyi mana asara ya sa kai ya fita ya barta cikin tunani mom bari naje na karbo masa magani pain relief take fada da ya Isa falon OK son sai ka dawo

07038185042
***********
Comment
Comment

 

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now