page 28

1K 77 11
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Zauran jarumai writers association

Allah ka kara wa annabi daraja da daukaka.

Allah ka jikan mahaifiyata da 'yanuwana da suka rasu, Allah ka yafe musu kurakuren su muma in ta mu tazo kasa mu cika da imani.

Allah ka bawa mahaifina lafiya ka sauwake masa ya Allah.

Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani.

Wannan page na kune yan jarumai writers association Allah ya bar mu tare.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P28

Not edited

"Ni dai kar ka sauke min kwandon bala'i ai bani nakar zomon ba..." Amir ya fada mishi, yayi mishi wani kallon bani sakona kawai na tafi don yasan idan ya bata lokaci tana iya tafiyar ta ta kyale shi, shi kuma ita ya ke so ya bawa sakon ta kai wa abban su(a zuciya ta nace ko dai da wata manufa ka ke so lalle ka aleena ce za ta kai sakon don iyayen ta su fara zargin ko akwai wani abu a tsakanin su😜)

Amir yana dariya har da cewa wayyo Allah dadi ya dauko leda biyu ya bashi, da sauri ya wufce ledar yayi gaban don ya hango aleena ta bude kofar gate din har ta fita. da dan gudun sa ya karasa wajen ta tana dab da zata shiga gida ya tare ta yana hakki.

"Kina da taurin kai da gardama" "kai kuma kana da shiga sha'anin da bai shafe ka ba "

"Duk akayi miki magana sai kin ba da amsa ko to wallahi na kusa rufe bakin tsiwar nan sai naga yadda zakiyi"

Hahhhh"ai kuwa duk ranar da kasa hannu kace zaka rufe baki na sai na gantsara ma ka cizon da har sai yayi jini"

Ya sa dariya ganin ba ta fahimci me yake nufi ba.

To na ji yanzu dai ga wannan ki shiga da shi cikin gida, "na menene kuma" na dubiya ne

Babbar magana ni ai rashin lafiyar da nayi ai ba babba ba ce balle ka kawo mini kayan dubiya, to an gaya miki ke na bawa ni ba ke na akan me ma zan baki? Kinsan mutum yana yin kyauta ne saboda abu abubuwa uku kamar haka: ko dai saboda tana matsayin sister shi , ko kuma tayi masa wani abu na kyautatawa da yaji dadi har ya yaba ya bata kyauta, ko kuma tana matsayin budurwar shi wato wacce yake so. To amman bari na tambaye ki acikin wadannan abubuwan da na lissafo ke a ganin ki wanne sahu kika fada? zata bashi amsa ke nan ya sa 'dan yatsan shi a bakin sa alama tayi shuru sannan yace "ni ban ce ki ban amsa yanzu ba ki bari sai wata rana zan tambaye ki ki bani amsa, yanzu wannan kayan abba zaki kai wa kice ina kara yi masa sannu da jiki"

Sai kunya ta kamata kuma ashe fa wannan mutumin da take tayiwa tsiwaa tana gwasale shi ne fa wanda ya taimakawa abban ta ya kai shi asibiti.sai ta sa hannu ta karba har da risinawar ta tace mishi " mun gode Allah ya saka da alkhairi ya biya bukatu ya kareka daga daga miyagun mutane ya baka mace ta gari"

Bai ma san lokacin da ya sakar mata ledar ba saboda sauyawar da tayi na lokaci d'daya ya masifar ba shi mamaki har ta wuce cikin gida, to me ya canza ta haka ohhh maganar abban ta wato dai abban ta shine weak point din ta sai yayi tsalle ya dire kasa Allah na gode ma, sai kuma ya waiga ko ina da ya tabbatar babu mai kallon sa sai ya wani sha kunu ya nufi cikin gidan.
********

Da gudu ta kara cikin gidan tare da yin sallama har da nishinta saboda yadda ledojin suka yi mata nauyi a hannun ta.

Ta tarar da abban ta a zaune a tsakar gidan su da ya sha gyara yayi tas da shi ta rungume shi tare da nuna tsantsar farin ciki a fuskar ta "abba na sannu sannu da dawowa abba ina mutukar farin ciki da zuwan wannan rana abba da aka samu wanda ya zo ya tallafa mana ya kai ka asibiti....kafin ta kara sa ummi ta tare ta ai ke dai bari aleena baki san yadda nake ji a cikin zuciya ta ba wallahi ina jin wani irin dadi har cikin tsakar kai na rabon da nayi farin ciki haka tun kafin abin nan ya sami abban ku, wannan yaro ashfaq ya kawo haske cikin rayuwar mu babu abinda zamu ce sai dai muce Allah ya saka masa da alkhairi

Ya kai abban ku asibiti an yi masa gwaje gwaje da yawa ya kuma siyo masa magunguna gasu nan da yawa kalli daga fara shan su har abban ku jikin sa ya fara karfi, kuma ke baki sani ba ummin su ba ki ga yadda ya rinka bani girma ba yana kaffa kaffa dani har ya janyo su ma ma'aikatan suka fara bani girma, komai ya ce sannu abba Allah ya warware mana ya baka lafiya kaji abba yana ta kuma sussun kuyar da kai kamar yana jin kunya ta fa.sai duk suka sa dariya har da aleena ita ma har da 'kya'kyacewa, sai iyayen suka kalli juna ganin farin cikin da 'yar su ta keyi.

Afnan ta shigo cikin gidan ta ga suna ta dariya sai itama ta kama dariya ta zauna a cikin su kusa da aleena , aleena tace tl ke kuma dariyar me kike haka dafa shigowar ki? ah to naga dukkan ku kuna ta dariya shi yasa nima nake dariya nasan wani abin dadin ya faru, sai su ka kuma sa dariya dukkan su.

Au ummi ga shi mai kyau din afnan ya bani yace wai na kawowa abba yana kuma kara yi masa sannu da jiki, kai masha Allah wannan yaron dan albarka ne inji ummi har da wata wahala haka to Allah ya saka masa da alkahiri ya ba mu ikon kyauta ta masa muma wata rana idan ranar mu ta zo, amin abba ya amsa nan suka cigaba da hirar su cikin farin ciki da walwala da jin dadi.
********†

Ah lover boy ka dawo ne daga rakiyar da ka bari nima ai na raka ka kaga daga nan sai na shigar da kai na wajen ta ko😛

Ashfaq yasa dariya kawai tun da ya gano tsokanar sa kawai amir yake yi ba wani abu ba, cikin nishadi ya zo ya janyo kujera ya zauna a cikin su fuskar sa da gan ta kasan yana jin dadi , ya kalli amira yace lil sis je ki ki kawo min abinci na nan na ci yanzun nan ta ce to, ta tashi ta wuce tana mamakin yadda lokaci daya soyayya na son canza ya ashfaq din ta hmmm lallai kuwa

Tana wucewa amir yace malam ya zaka zo muna tsaka da hira ka kama ka tashar mun lil sis daga nan kai kaje ka gama shigar da kan ka nima ka kyale ni na kafa gwamnati na mana gaskiya ka ta shi ka ciga cikin gida, don yanzu she is no more a child ina so na shigar da kai na da wuri don ayi bikin mu tana ga ma school, tun da dai kai har yanzu baka samu wacce ka ke so ba ko ? Ya fada yana 'yar dariya , shi ma dariyar ashfaq yayi yace kai dai ka sani abinda kake son ji dai a bakina ba zaka ji shi ba yanzu kuma wallahi ba in da zan je anan din zan ci abincin in na gama kwa ci gaba da hirar ta ku ta yarinta hhhh .

Dadin ta dai kai ma ka fara hirar yarintar yanzu ba wai ni kadai na ke yi ba.suna cikin hirar ne amira ta dawo dauke da plate din abinci a kai ya ashfaq gashi bari na shiga ciki

"Ke dawo dawo ki zauna ka da kisa wannan murumin ta makureni yace ni na koreki ta kyalkyale da dariya ha ba dai ya ashfaq ya za ayi yace haka eh mana ba ki ga yadda yake cika yake batsewa ba wai na takura ma don na zauna anan wai na hana shi hira.

Dukkan su suka sa dariya su mamaki suke yadda wai yau shine yake ta hira haka lallai kuwa abin al'ajabi ba ta karewa

Suna hira yana cin abinci har ya kusa gama wa suka ji karar bude gate dukkan su suka zubawa gate din ido sakamakin wata galleliyar mota blak da suja gani ta shigo cikin gidan tayi parking.a guje mai gadi ya zo ya bude masa kofa wani kyakyawan mutum ya fito waje, fari ne kal da ja kalle shi kaga dan fulani zai kai kimanin shekara 50 da doriya

Dukkan su ka mike a tsaye sai kuma suka kwasa aguje kowa yana so ya riha dan uwan shi zuwa ga wannan mutumin.
******

07038185042

Comment

Comment

Pls share vote and follow me in my wattpad.

Sirry na jina kwana biyu nayi wata 'yar tafiya ne.

Love you all

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now