page 1

7K 183 1
                                    

###SOYAYYA KO SHA'AWA###

Bismillahir rahmanur rahim.
Ya Allah yadda na fara littafin nan lafiya Allah kasa in gama shi lafiya don albarkar annabi.

Godiya ga mai dambu kaunar ki daban take.

Mallakar Jamila (maman amir)

Wattpad:@jami1020
******************
Baka jin karar komai a hanya sai kukan mashin da mota anan na hango wata yarinya mai tsananin kyau kamar ita tayi kanta saboda kyawunta fara ce ita ba doguwa ba ita ba gajeriya ba ana iya kiranta da matsakaiciya mai doguwar fuska Ga bakin ta Dan karami hancinta siriri duk da Tana sanye da hijabi hakan bai hana a hango tudun gashinta da ta tufke shi a kanta Tana ta faman tafiya a gefen hanya wasu motocin suna tayi mata horn saboda Tana hawa kan titi Amman ita bata San ma ina kafarta take takawa ba saboda tsabar tunanin da ta shiga ta yadda za tayi ta samu kudin da za asiyowa babanta magani saboda yadda yake fama da ciwon hawan jini .
A haka dai har Allah ya kawo ta cikin in unguwarsu nan naga ta tsaya a wani gidan kasa da ya sha siminti ta waje Amman fa daga ganin siminti ya ji miki don duk ya kwararrabe.tun daga soro
ta fara jin tarin mahaifin nata an shinfida masa taburma anan tsakar gida da sallama ta shigo ciki jikinta a sanyaye tana tausayawa mahaifin nata da irin halin da suke ciki don tun daga kwanciyar mahaifin nata ciwo komai ya tsaya a gidan karatun ta ma ya tsaya abincin ma da kyar suke samu su ci.

Aleena Aleena ta ji Maman ta na kwala mata kira yanzu ke bazaki dai na yawan tunanin nan ba saboda Allah ke ma so kike hawan jini ya kama ki kamar mahaifin ki duk abinda ya sami nawa kaddara ce daga ubangiji madaukakin sarki kuma ba ka bawa bai Isa ya tsallake ta ba saboda haka mu barwa Allah komai shi zai mana maganin komai suna cikin magana sai ga wata yarinya da shekarunta ba zasu wuce 7 ba ta shigo aguje tana cewa wallahi mama yau yan can gidan zasu tare Na gansu far are masu kyau kamar larabawa har da wani namiji Dan saurayi mai kyau kamar India amman fuskarsa a turbu ne baya magana da kowa yana sanye da far in gilashi ummm yana sunan sa naji Maman shi takirashi Amman sun an da wahala Maman ta ce oh ni yanzu afnan ba zaki dinga rage surutu ba sai kace wata aku bakya ganin yadda yayarki magana ma da kyar take yinta sai ke aku bakin magana oh ni Khadija Allah ya bani Yara anan daya miskila daya kuma aku to Allah ya raya min Ku don albarkar annabi mahaifin su dai duk da yana jin jiki bai hana shi yi. Murmushi yana godewa Allah da ya ba shi iyali masu hankali da nutsuwa duk da halin da suka tsinci Kansu Na talauci sai dai a yadda yake fahimta aleena daurewa kawai takeyi domin da ta kadaita shine nan zata shiga tunani ya Na mutukar son yarinyar shi duk da Allah ya yo ta miskila yana adduar Allah ya bata miji nagari ya ba shi lafiya kuma it a kuma Maman su da suke kira ummi addua take Allah yasa mutaanen kirki ne suka tare a gidan.

To fa Ku biyoni don jin suwaye wadannan mutane yan gayu inji afnan

*******************
07038185042

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now