💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗Bismillahirahmanurrahim
Aysha A bagudo
Page 1-2
Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta ,a silent place, saboda bata cika hayaniya mutane ba , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku" unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin yan yahoo boy'z domin mafi yawancisu sunfi sha'awar zama acikinta. rayuwar mutane unguwar abin sha'awa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje .
PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE
Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy, Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .
Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki bila adade.
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu .kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai mazan kanta.
ya tattara kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu hjy shema'u wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya goma Sha biyu, mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine saboda taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata .haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu .Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurin juya dukiyarsa ,ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya, yayiwa sauran yan'uwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed ne babba sai ita sai farida , kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren .
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa acikinta .
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.

DU LIEST GERADE
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan