24

9.6K 343 7
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
    💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 44

Jini tagani har da gudaji gudaji  a pent dinta. Wanda hakan yayi sanadin tsugunwarta kasa da sauri .

tsugunwarta keda wuya taji tamkar ankara mata wani ciwon ne akan wanda take ji.

kmr Jira jini yake ta tsugunna yashiga zubowa " Ga wani  irin azababen ciwon  data ke  ji a kasan mararta kmr zata mutu.

murkususu take sosai tana yarfe hannu.
ta dinga nishi sama sama duk iya duriyar da take  dan kar DEENI ya farka ,bai hana Hawaye silalowa daga idanunta ba .

Da  azaba tayi azaba kawai say tasa kuka.

Cikin bacci deeni ya dinga jin sautin kukanta  'ahankali 'yashiga lalubar inda take kwance da hannushi .yayinda idanunshi ke rufe ,yaji bai ji alamunta ba ya sake motsowa gaba still bbu ita da sauri ya mike zaune yana bin takin da kallo" km har zuwa lokacin baidana  jin gujin kukanta ba.

Hankalinsa ya tashe  ya zabura ya mike tsaye   yayi hanyar bathroom din dan tanan kunnenshi ke jiyomishi  sautin  kukanta  .

say day  yana daura hannushi akan handle din kofar yaji kofar gam  a garkame .
ga km alamun  Tana cikin bathroom din  dan lokacin yana jiyo  sautin kukanta Sosai.

A razane  deeni ya hau buga fakor da karfi yana kiran sunanta zeenat...... Zeenat.. amman  shr taki amsawa sai kuka take .

meke damunki zeenat ki taimaka bude min kofar  please ... Duk yabi ya rude ya gigice yacigaba da buga fakor yana kokarin ballata .

Ganin irin azabar da take sha wacce ita tajanyowa kanta gashi  idanunta har sun soma rufewa shi km yana cigaba da jijiga kofar hade da kiran sunanta yasa ta rarrafa da kyar ta bude masa yana ganinta haka ya gigice ya shiga  tmbyrta
 
Ita km tana murkususu dafe da mararta 'ahankali ta dinga nuna masa kasa inda jinin ke kwance dan gabadaya idanushin akanta  suke  shiyasa sam bai yi saurin gane abinda ke wakana ba .

Kallan yadda jinin ke tsiyaya akasa ya kara tayar masa da hankali .

Sai murkususu take tana wayyo Allahna Yaya mutuwa zanyi dan Allah kayafe min abinda nayi ....na...
Na ...say km tayi shr sakamakon wani yunkurin ciwo  daya tasomata  say Ga wani jini ya sake ballewa ..Ta Miko masa hannuta, kafin yakaraso gareta har ta suma .

A gigice yakaraso  ya rungumota jikinsa.
Tare da  kunnan popping yashiga shafa  mata ruwa ajiki da fuskarta.
  , ahankali yaga ta  sauke ajiyar zuciya.

A rude yake cewa "
Kingani ko zeenat.

kinga abinda kika jawo min ko .

shiya nace muje hospital duk yabi ya kidime ya gigice  har yarasa me yakamata  yayi ,bbu komai kina sane kike kokarin jawo min   asarar bby'na ko.
Amman
, bbu komai .

Say kalmar bbu komai yake faman" maimaitawa .Bai yi aune ba yaji saukar hawaye a fuskarsa.

Ganin jinin  ma kmr sake  zubowa yake, yasa ya mike da  sauri  bbu inda baya kirma  jikinsa yakoma daki.

Jikinsa na rawa ya zira jallabiya ajikinsa ya dawo ya dauketa ya fita daita yasata abayan mota ya zagaya yashiga yatada motar  da gudun bala'i.

tun daga nisa yake dannan  hon kafin ya kawo get din estate din  hon dinsa hon ya karade koina . wanda hakan  yasa gabadaya securities din wajen suka zabura suka Mike tsaye  hankalinsu a tashe .
ganin motar oga deeni ce yasa mutun uku sukayi  hanzarta bude get din a guje ya figi motar ya fice daga gidan.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now