26

8.8K 311 7
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO

Page 46

Two weeks later

Gabadaya jikin zeenat yasoma samun
Canjin yanayi.
, Wani irinjin kasala kasala bacci bacci take ji ajikinta koda taci abinci ko wani abu zataji ya tsaya mata a kirji .

Cikin bacci zeenat Taji kmr wani abu ya tsaya mata a kirjinta kmr yadda  tasaba dan haka tasa hannuta daidai tsaitin inda take jin abun ya tsaya mata Ta dan soma  shashafawa sai taji abin yayi kasa .
Sake ,juye tayi tashige cikin kirjin deeni   sbd tafi jin  jin dadin baccinta ajikinsa,

AHankali Deeni ya lalubo wayar dake gefen dayake ya duba time yaga uku ta wuce da wasu en mintina dan haka ya zare zeenat daga jikinsa   ya kwantar daita sannan ya  Mike ya sauko  daga kan bed daga shi  sai boxer iya cinyarsa da white single ya dan tsaya yana kallon yanayinta sannan ya wuce dakinsa.

wanka yayi da alwala yazo ya tadda ikimar sallah" byn ya idar bai tashi daga gurin ba .
Yana zaune   yana ta addu'oinsa dayasa ba  har sanda ya jiyo kiran sallah a masallaci dake cikin estate din tukun ya Mike ya sake shiga bayi .

Kiran sallar asuba ne ya tada zeenat da kyar Ta Mike tayi bayinta wankan tsarki tayo tare da alwala .

Byn Ta idar da sallah Ta shafe jikinta da lotion pure white gold kmr yadda tasaba  kullum tare da feshe ilahirin jikinta da turaruka masu matukar sanyi  da dadi kamshi .

Duk wannan shirin da take tana yine  tana shiga bayi zubda miyo dake taruwa a bakinta wanda tarasa na Mene dan ita sam bata kawowa ranta komai a game da miyon datake zubarwa"  ganin tun last week taje Ta nemo tablet dinta da kanta ,km tana amfani dashi yadda aka sheda mata tun farko  .

Kwanciya tayi tare da runtse idanunta tana tunanin ko yaushe deeni yabar dakin

kirjinta taji ya sarke mata guri daya can km tasoma ganin juwa juwa cikin ya kulle .
Jin haka yasa  ,tayi tunanin kodan jiya bata ci abinci bane" ga oga deeni  km ya kwana aikin service.
yasa Ta Mike ta dauki wayarta ta Kira number moris dan yanzu tana da waya a hannuta  tace ta dafo mata indomi da tea amman tabari indomi tayi yaji sosai aciki  tabawa rahma takawo mata .

Hakance takasance dan ko cikakken minti ashirin ba'ayi ba Sai ga rahma Tayi nouking kofar zeenat .

Tabada izinin shigowa.
Rahma ta karaso har cikin dakin tana gaisheta tare da  ajiye plate din indomi ,akan bedside ta juya tabar dakin bata jima da fita ba ta dawo da cup din tea.

AHankali   ta Mike  ta ,dauki plate din  tasoma ci abinci say dataga plate din tas.
Sannan  ta daura da tea mai kwari.
".   ta dan jingina bayan da jikin gadonta , aiko kmr cikinta jira yake taci abinci ,yasoma yamusawa yana juyawa  da gudu tayi bayi tashiga  amayar  duk abincin data ci .

Cikin haka deeni yashigo dakin da shrinsa na fita aiki.
tsaye yake yana binta  da kallon mamaki ,yaushe km haka ta fara faruwa ya tmbyi kansa .
AHankali ya maida kofar dakin  Ya rufe yakarasa shigowa dakin sosai yana  kallonta . Waje yasamu ya zauna yanacigaba da dubanta
Har sanda yaga tana kokarin fitowa daga bayi. 

Jikinta a mace ta rarrafo jikin gado  ta jigina bayanta tana cigaba da maida numfashi  .

Mikewa yayi  ya dawo  kusa daita yana kallonta  ya dafata zai  yi magana
Yaga Ta Mike da sauri tayi bayi ta tsugunna tana  kararo amai kmr zata sume .
take jikinsa yabashi abinda kedamun ba mamaki Allah ya amsa addu'ar kwallonsa yashiga ya sake shiga raga  .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now