38

9K 304 1
                                    

💗💗💗💗💗
   AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 58

Rungume take a faffadan  kirjinsa har lokacin " yayinda  hawayen  tausayin kanta ke  cigaba da bin kuncinta"  danasani  tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya  ne ke damun zuciya .
  'hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata " zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya ...fa.
  yau ita zeenat da kanta ake kokarin  son sanya  mijin yi karo mata kishiya... Kishirya.. ta sake  maimaita  hakan akasan ranta  abinda tafi mugun  tsana  a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya ..

  kirjinta ke mata radadi da nauyi  tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta... wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke  sake tasomata fiyye da yadda take ji a da.
  tsanar  sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin.

Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma  sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma  rabata da sansar jikinshi gabadaya.

, Tare da zuba mata rikitattun idanushi kawai  Dan shi sam kwata kwata bai iya wani abu wai  rarrashi ba   . ballanantana har ya tsaya wani bata lokacinsa gurin  rarrashinta .

,a dake taji sautin muryasa   ',malama kiyiwa mutane shr duk  kinbi kin cika min kunne da wannan bazan kukan naki  mara ma'ana  ..

ko uban   wani ne ya  aikeki wulakanta cikin  da Allah yabaki tun farko .

  Wlh idan kikasa damuwarki  tashafi lafiyar  mahaifiyata   akan maganar kishiya ..nan zan baki mamaki ..
   kishiya ...bama daya zanyi ba  har biyu idan nagama sai nayi .
   "inyaso  ki mutu sai ki kashe kanki kmr yadda kika ce  ,sha sha kawai  ya fadi hakan yana may  da jan mugun tsaki... mtssss  .

take jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma jin maganar bama kishiya daya ba  har idan yaso zaiyi ..
  "ai ...batasan sanda ta zube  kasa ba.
  Tana kuka Tana  girgiza masa kai dan  gabadaya  kasa magana tayi sai jujjuya  kai kawai  take tana zubda kwalla.

Wata uwar  ,harara ya watsa  mata  hade da binta da wani irin bazan kallo wanda yasan hantar cikinta kadawa wayyo hrt karka min haka dan girman Allah karka min kishi....sai km Tayi shr Tana cigaba da kuka.... bakinsa Ya tabi tare da  cewa meyya haka oya Mike ..  Mike ni kibar  min dakin kinsa fa ni bana son damuwa .

Yana gama fadar haka ya haura saman gadonsa ya dau towel daman km abinda ya fito dauka kennan .

bathroom ya sake koma   ya sakarwa kansa ruwa tare da dauro alwala sannan ya fito kugunsa daure da towel .

mamaki ganinta   yayi   har lokacin bata bar dakin ba Tana nan durkushe tamkar yadda yabarta  ,ganin yanayinsa da km yadda yake kallonta da rikitattun idanushi masu matukar  birkita mata kwalkwaluwa ,da hana zuciyarta sukuni .
yasa  ta mike tsaye da sauri jiki  har rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,a sukwane ta  tabar masa dakinsa  Dan tasan halinsa maseefar sa, bakaramin aikinsa bane ya shuka  mata rashin mutunci idan ma taci sa'a Bai hada mata da mugun duka ba tunda daman ya mata  gargadi kar sake ganinta    bedroom ba  .

Fitarta daga dakin  yayi daidai da sauke  naunauyen ajiyar zuciyar da yayi..
, yayinda wani gefe na zucitarsa na Dan tausayawa mata  game da halin   rayuwar data jefe kanta ciki.

hakika shi yasan  tana   wahalar da zuciyarta ne kawai akan  batun   kishiya .
Dan kishiya ba fashi sai ta zauna daita.

'ahankali ya sake  sauke  wani naunauyen ajiyar zuciya tare laso lip's dinshi na kasa ...
" cikin sauri ya shiga shirya  kansa cikin wasu hadaddun kananan kaya masu matukar kyau da daukar hankali shirt  ce  ashi  colour mai gajeren hannu  sanye a jikinsa sai  wando blue  jeans  wanda suka yi matukar karbar surar jikinsa.
' koda yake shi din may matukar kyau ne km kowani irin kaya ya sanyawa jikinsa    sai sun  amshi karbi shi.
, cikin sanyin nan nasa da takunsa na kasaita  yakarasa gaban mirrow  ya dauki turarensa mai matukar  kamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi.
  ' sannan ya gabatar da sallah byn ya idar sallah ne ya sauko parlour kasa cike da isa .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now