49

10.8K 295 2
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO


*Assalamu alaikum warahmatul  Allah  Ina wa duk masoya wannan labari Na auren sirri fatan alkhari .yayinda duk wani   korafe korafenku  yake isowa gareni kai tsaye batare da bata lokaci ba say day yana da kyau mu kula mu gane wani  abu shi manufar  rubuta labari karan kanshi ba wai dan nishatarwa bane da biyyyewa son ranmu . Muna yi ne dan fadakarwa da wa,azantarwa Ga al,ummu ta hanyar da mutun zai samu damar ya gyara kuskurensa .da km Wanda yake da akidar aikata mummunar aiki nasan dawaya masu kawo korafinsu masoya bagudo ne, domin kuwa kaunace Silar damuwarku har takai ga korafinku ya iso har inda nake .bazan iya misalta  muku tarin kaunata gareku ba. amman ina son Kusan wani abu kuna 'cikin  zuciyar  bagudo . Bagudo ni'feyi ju km inshallahu Muna taren tare har abada*🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻 

Page  69

Kai tsaye dakinsa ya nufa ya fada   kan royal bed dinshi ya kwanta flat yana fidda numfashi ahankali.  yayinda  , kyawawan idanunshi  suka gama  rikidewa  tamkar garwashi tsabar tashin hankali dayake ciki.
why ...why ummi why did you want's to do this to me?
,meyasa zakiyi min Haka ummi  ?
Meyasa kike   kokarin son cusawa zuciyarta abinda bata so ?

,bana son yarinyar nan , Bana kaunar  ganinta asalima Na tsani  kusancina  daita   domin hakan na jifani 'cikin tsananin  tunani da rasa natsuwata.
" bazan iya bijere miki ba ummi ,to meyasa  kike so ki tursasani yin AUREN SIRRI da  kaskantacciya macce?

tsawon lokaci ya dauka yana kwance idanunshi na kallon celing dakin  gabadaya  tunaninsa a halin  yanzu ya ta,allaka ne akan abinda ummi take son ya aikata .
   ,yana son umminsa bayason  abinda zai disashe farincikinta ballanantana har  yakai shi Ga bijirewa
umarnita.bacin ran umminsa ,babban tashin hankalisa ne,a gareshi   bancin   haka da Babu  abinda  zai kaishi auran wannan yarinyar may idanuwa tamkar Na mage  .
" mtssss yaja tsaki a ranshi Dan   duk wannan zance dayake yi  yana yinsa ne a zuci .

ahankali ya runtse rikitattun idanunshi banda yana jin bacci Sai Dan yana bukatar maido da natsuwatsa dake kokarin  barin gangar jikinsa .

Bangaren nablah kuwa  gabadaya duk wata  surar dake  jikinta  ta sauya , ta  murje ta sake yin kyau daita  Sai dai  walwalarta da kuzarinta sunka ragu.
sakamakon  matsi da takurar da Zeenat din ke yawan yi mata, Wanda ita kanta  tarasa dalilin hakan .
km kwata kwata  bata dauki takurar da Zeenat din kemata  amatsayin wani aibu ba .

Baya  ga tunaninta Haka wasu daga 'cikin masu arziki da manyan masu hannu da shuni  sukeyiwa marasa shi km  marasa galihu irinta .

Duk da  yawan  takurar da Zeenat din ke mata hakan    bai hanata  samun farinciki da walwala daga gurinsu laraba da safeena ba . Dan haka  ta tattara Zeenat takurarta ta watsar a gefe tacigaba da abinda yakawota  iyakarta daita aiki Wanda tasan dolenta ne Tayi shi Dan abinda tazo yi kennan .

Ranar Saturday ' nablah  na zaune ita da safeena a main parlour din gidan  sanye take 'cikin doguwar rigar material may ratsin pink and  popul yayinda  jikinta ke  rufe  da dan karamin  hijab  kmr koda yaushe.

babu kwaliyar komai a fuskarta kasancewarta ba ma,aboyaciyar son kwalliya bace da kalekalen zamani,  sai Dan Whit lip's din data  shafawa lebenta.

,rashin kwalliyarta   bai hana ainihin   sihirtaccen kyawunta fitowa ba.haka ma kayataccen fatar jikinta choculate  colour ta kwance luf.  luf..koda take sanye 'cikin ' hijab  kyawunta  bai boyuwa ba..
Sai dai fuskarta Tayi fayau ..wanda  ya nuna  alamun rama atattare daita km  hakan ya sake fidda asalin siffar halittata kyawun jikinta .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now