84

11.8K 414 41
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA  A BAGUDO

     Dedicated to
Hauwa A usaman
         Jiddar

🌈Kainuwa writers association

Page 104

Jin furuncin zeenat dake shiga cikin kunneta yasa tasoma yin Kasa kasa daga  jikin deeni kadan ya rage bata zame ba yayi sautin tarota Amman ki yarda ta tsaya bisa kafafunta dole tasa,shima ya bita yana sake rungumeta ajikinshi
yaranta gabadaya suka sake yowa kanta suka kamkameta suna kuka .
ummi najin abinda zeenat ke faman fada tana kuruwa da zunduma ihu..... gabanta ya yanke yayi wani irin mummunar faduwa ta karasa fitowa waje da saurin maseefa.wanda har hankalin jama'ar dake cikin estate din yafara yowa kansu dan wasu daga cikinsu MA har Sun fara lekowa ta balcony suna kallonsu.
Idanun ummi suka sauka akan deeni dake durkushe rungume da nablah ajikinshi ....
kallo daya zaka masa Kasan hankalinsa a matukar tashe yake .
Sanann km take zaka gane yana cikin tsaka ME wuya.
ahankali ya dago rikitattun idanunshi ya zubawa ummi yana kallon da mamaki A saman fuskarshi .
suka hada ido da ummi wace yanayinTa kawai mutun zai kalla ya gane irin kallar tashin hankalin datake ciki.
Kallonta yacigaba dayi yana zafi cikin zuciyatsa da gangar jikinsa Wato Tana kallon zeenat ke shirin Yi masa aika aika agida batare data ta tsawarta mata ba ....
ya runtse rikitattun idanunshi yana me jin tsantsar takaicin abinda umminsa kema masa ahalin yanzu..
dakewa kawai ummi tayi tamkar bataji duk abinda ke faruwa ba tare da Nemo jarumta ta sanyawa jikinta ta dauke idanunta akan deeni kana muryarta na shaking tace zee..zeenat lafiya meke faruwa ne?

A haukace  muryar zeenat na rawa jikinta na wani irin tsuma tace ummi wannan yarinyace ta km yin ciki a gidan nan har na tsawon wata shida  ummi idan da ance kb NE to yanzu cikin  uban waye ajikinta ? Tunda dai kb yabar gidan nan.....

banda kuka babu abinda nablah da yaranta ke faman yi .
yaran kuwa sai faman tsallara  kuka suke ganin uwar su afrigice tana kuka yayinda deeni dake rungume daita yasake kamkameta tsam ajikinsa yana shafa bayanta da tafin hannushi gabadaya ji yayi sararin samaniyya da inda yake durkushe na jujjuyawa dashi.yarasa wace irin masseefa da tashin hankali ke tattare da zeenat ....
Yarasa wani irin kishin hauka gareta .
sanadinta yarasa abubuwa dayawa. Yarasa kulawar mahaifiyarsa da soyayyarta yarasa farincikinsa yarasa jin dadin duniya duk wani farincikinsa kokari take taga tadagushe masa . yayinda  kwata kwata batada wani amfani agareshi yarasa abinda take nufi dashin ? Farincikinsa ta haifa masa ya'ya takasa wanda yasamu  km tana neman ganin bynsu tare da sabautasu ummi na zaune tana kallo ta daure mata Gindi .
yaya ake son yayi darayuwarsa ?
Tsuma kawai yake jikinsa na kirrrma yana jin tamkar ya Mike ya sabauta mata jiki da mahaukacin duka ko zai ragewa kanshi takaicinta....

itako nablah gabanta ne ya sake yin wani irin matsanancin faduwa da karfi .
Wani irin bugawa kirjinta keyi da sauri da sauri yayinda zuciyarta ke suya da harbawa...ganin kuka bazai fishsheta ba yasa  ta tasaka  iyakacin karfinta ta fexge jikinta daga jikin deeni .......

jikinta na kirrrrrma ta dubi zeenat ta furta kalmar ciki.

Ciki fa kika aunty ? Meye hadina da ciki km ahalin yanzu?
takarasa mgnr tana kuka ta girgiza Kai.

Eh munafukar Allah ciki ne dake km wallahi sai Kin sanar Dani uban da dayake dirka miki ciki  a gidan nan batare da saninmu ba .

deeni ya Mike tsaye da kyar jikinsa a sanyaye Tare da cire long sleeve din dake sanye ajikinshi ya sanyawa nablah.
har ya saka mata rigar hankalinta bai jikinta burinta kawai taji duk abinda ke fitowa daga bakin zeenat yazamto karyane ba gaskiya ba.ya tareta sosai da fadadden kirjinshi ta yadda bbu me ganinta kana
yasoma aikawa escort dinsa da derebobinsa da securities din da suka dan taso domin ganin tashin hankalin dake faruwa.
da wani irin kallon kasa kasa me kama da tsayuwar uwar me suke masa agurin tare da nuna musu hanyar biiiiiiii da yatsansa ...... dan kwata kwata takaicin wulakancin abinda zeenat tayi masa ya hanasa furta daidai da kalma daya ce .......
aiko take suka  juya gabadayansu km bbu wanda ya sake juyowa acikinsu..
hankali nablah a matukar Tashe ta nufi
Gurin  wannan takardar da zeenat ta jefar ta dauka jikinta na kirrrrma Tasoma karantawa  tabbas sunanta ne rubuce cikin farar takardar dauke da ciki  har na tsawon 6 months.
innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai nablah ke maimaitawa  ta juyo da sauri tana duban deeni dake tsaye still yana kareta daita da jikinshi.. tsuru tayi masa da ido kawai tana kallonsa hawaye na tsiyaya daga idanunta kafin daga baya ta juya tana kallon zeenta da ummi wasu tsiraran hawaye Masu dumi suka shiga kokuwar biyo kuncinta ta dawo tamkar wata mutun mutumi atsaye a gurin.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now