50

12.6K 338 3
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO

*Waannan shafin sadaukarwa ne gareku masoyan arziki   tare da yi muku  fatan alkhari  a duk inda kuke kaunar dake tsakaninmu daga Allah ne ,Ina rokon Allah s.w.a ya barmu taren Tare  har abada sannan ya hada  fuskokinmu a jannatul firdaus Ameen*

*Mrs splendid*
*Maryam tijjani Adam*
*Safeena mukhtar getso*
*Maryam kalgo*
*Adaweeyyah*
*MMN hafeez*
*Murja*
*Fateema abuje bagudo*
*Aina,u gadan kaya*
*MMN Aliyu*
*MMN illima*
*Faiza bsbs*
*MMN sadik*

*Ina Mika godiyata gareku all auren sirri fans sakonninku yana isowa gareni kai tsaye Ina  jin dadi yadda kuke Nuna min kauna Ina addu'ar Allah Yasa kar  soyayyarsa nan ta tsaya iya social media kawai  tazarce har illa Masha Alla  kyawun tare inshallahu*




Page 70


Mikewa Tayi 'cikin sanyi jiki taje tayo alwala tasoma gabatar da sallar magriba , baita ta  Mike daga kan praymat dinta   ba har sai da Tayi sallar isha'i.

  Kwance take lamo akan gadonta ita daya Tayi shr  hannuta rike da   karamin litattafin garkuwar muslinci, hisnul muslim. 'tana dubawa ahankali  Amadadin abin da take karantawa ya dinga shiga kwalkwaluwarta sai ma wani tunani ne yazo mata .
Sosai ta afka 'cikin damuwa yayinda  tunanin  duniya ya taru yayi  mata yawa .

Tunanin gida da mamanta da  mahaifinta har ma da ah'linta,  duk shi yafi damun xuciyarta ,ko a wani yanayi en gidansu suke cigaba da rayuwarsu ?

Ko  wani hali mahaifinta yashiga lokacin daya dawo gida ya  iske bata nan ?

Allah shine masani ...ta fadi hakan 'cikin zuciyarta 'tana may langwabar da kanta gefe .
  " take nadamar rashin bin umarnin mahaifnta yashigeta, gashi takawo kanta cikin tsaka may  inda ba,asan darajarta da mutuncinta ba" to meyye amfanin zuwanta  neman kudin shiga Jami,a alhalin mahaifinta Bai yarda da hakan ba.

Anya kuwa batayi kuskure   a rayuwarta ba ?
Anya kuwa   ko kudin tasamu zasu mata albarka datake son cigaba da karatunta dashi ?

Ta Dade kwance 'tana tunanin rayuwarta  ganin bbu sarki sai Allah Yasa tabawa zuciyarta hakuri ......Tare da Mike  ahankali tayiwa kofar dakinta key sannan  tashige bathroom with that thinking tayi  wanka
shape shape Tare da dauro alwala gabadaya.

tafito 'tana goge jikinta da dan karamin  towel din dake daure ajikinta Wanda Bai Ida gama rufe  mata jikinta  ba sosai. Dan kana kallon wasu surorin jikinta a bayyane .
,sai data gama gogge koina a jikinta  sannan  daga karshe taje ta maida towel din  jikin kofar bayi.
Ta dawo gaban mirrow ta tsaya 'tasoma kokarin tufke yalwantaccen sumar kanta gefe" Wanda tsabar yawansa   yasa da kyar take iya  tattarosu  ,Tare da tufkesu gefe daya  domin   tasamu damar  yin bacci Sosai dan wani lokacin idan ta tufke gashin a tsakiyar kanta bata tasamun natsuwar yin bacci Sosai.

A Ranar DEENI Bai samu damar sanar da umminsa komai a game da  aurensa da aka daura da nablah ba.
sbd haushin   yarinyar da yake tawainiyya da zuciyarsa km hakan yasamu nasaba ne  da ganin da yayi mata Tare da kabir mai wankinsu  .

Ko yanzu da yake zaune a dakinsa bbu komai ajikinsa facce  dan karamin wando short niker iya cinyarsa  .
  "koina ka kalla ajikinshi gashi ne kwance  sai sheki da daukar hankali suke Tare da  birgerwa  tsabar kyawun halitta da Allah (s.w.a) yayi masa , kwantaccen gashin jikinsa suna kwance luf.luf..ta koina abin  Sha,awa yayinda kan  nipply dinsa dake manne Dass da kirjinshi zagaye da gargasan  gashi , sai yazamo tamkar wani ado ne  akawa nipply din .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now