63

9.6K 300 0
                                    

💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO


Page 83

Ganin yadda Ya fige motar da gudu maseefa  Yasa kukanta ya Karu sosai, hankalinta yayi matukar mugun tashi tsoro tattare da fargaba ne sukayi nasarar   lullube duk wani  ilahirin jikinta, abubuwan da yake mata sun fara isarta Amman tarasa yadda za'tayi dashi.

takaicin hk Yasa ta kife kanta bisa cinyoyinta tana sake resgar kukanta mai cin rai da  suma zuciyar ma'abocin sauraro .

Daidai jankode first get taji  ya Dan sausauta gudun motar tare da daukar hanyar Aja.
" tafiya kadan  sukayi  ya soma alamun tsayawa  ya gangara gefen titi yayi park din motarsa, tare da  zuba mata rikitattun idanunshi kawai yana kallonta  da sauraran yadda take risgar kuka da iyakacin karfinta.

jin kukan nata yake har 'cikin zuciyarsa yayinda gefe daya km ya dinga ji  tamkar ana diga masa ruwan dalma ne a kirjinshi , yana jin yadda sound din kukan nata ke fita da karfi har da shesheka .

runtse rikitattun idanunshi yayi tare da dafe daidai saitin zuciyarsa da tafin hannushi sakamakon yadda yake jin  zuciyarsa na bugawa da karfe ...

bai jin zai iya yi mata mgn a yadda yake jin kansa Dan hk yabarta tayi kukanta mai isarta sannan ahankali  yaji  tasoma yin  shr  tana jan numfashi da kyar da sauke ajiyar zuciya.

Jin ta daina kukan Yasa shi bude rikitattun idanunshi, ya  ya Ciro hanky agaban aljihun rigarsa ya goge fuskashi wanda ya jike da gumi sharkaf tsabar tashin hankali daya tsinci kanshi ciki .

Ahankali ta dago kanta ta maida gefen titi tana kallon motocin dake giftawa time to time ...

gyara  zamansa yayi da kyau yana fuskantarta ahankali ya Dan motso   kusa daita tamkar zai shige cikin jikinta  Yasa hannunsa duka ya mtaso daita yana mai  juyo da fuskarta yana kallon kwaryar idanunta batare da yace mata komai ba . kawai taji  ya hau  goge mata Hawayen dake   fuskarta, yana cigaba da  kallonta hade da yin  nazarinta..


Sannan ya hade tafin hannushi cikin nata .yana kokarin fixgota jikinshi taki yarda ta makale jikinta da kujerar tasoma kokarin cire hannuta cikin nashi ,Yayi saurin sake damke hannu nata cikin nashi sosai ta yadda bazata iya kwacewa ba.

wani irin zafi yaji ,jikin nata ya sake dauka fiyye da sanda suka baro gida  ,km yana jin yadda da zafin  ke fita yana  shiga jikinsa tare da ratsa kowane shashi Na jikinshi  .
ya kai hannushi gefen wuyanta "nan ma zafi yaji  tamkar garwashin wuta hankalinsa yayi maseefar  sake tashi sosai .
, wani  irin abu ya dinga ji   mai kama da so.. yana masa yawo a sansar  ajikinsa tare  da kokarin kawowa zuciyarsa farmaki take duk wani kuzari dake jikinshi ya nema ya rasa ..tmby ya jihowa zuciyarsa da ruhinsa kar dai yakamu da soyayyar yarinyar ne, batare da yashirya yin hakan ba ?
Kai hkn ma ba zai taba yuwa ba , take km wani part Na zuciyarsa yashiga  karyata hakan .

yasan ya taba son auren zeenat .. km koda ummi ta hanashi aurenta alokaci, bai tsinci kanshi 'cikin wannan tashin hankali dayake ciki ba ..

Wani irin sanyi yake ji ajikinshi tamkar ana masa wanka da ruwan sanyi akan yarinyar duk wani buga da zuciyarsa zatayi ,tana yi akan yarinyar , mamaki ne fal yacika zuciyarsa to me hakan yake nufi dashi km ?
Ya tmbyi kanshi .
Wayyo Allah ahankali yashiga furta hasbunallahu wani'imal wakil yana yi yana sake  nanatawa

da kyar yasamu ya dinga fizgo  numfashi yana fitarwa ,ahankali ahankali  da sauri ya saki hannuta dake sarkafe da bashi  yayi  reverse ya dauki  hanya zuwa 'cikin gari ..

Tafiya sukeyi tamkar wasu kurame bbu may cewa Dan ,uwansa qala.kwanensu da abinda ke damun ,shi  yana wata duniyar tunanin yadda yake jin yarinyar akasan zuciyarsa gabadaya Gani Yayi tana neman mamayeshi da komai nashi .
,yayinda ita km haushin kasancewarta tare dashi guri daya  Yasa tarasa walwalarta da sukuni...

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now