💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
*wannan shafin sadaukarwa gareki ke kadai domin ,Kin cancanci fiyye da hkn a gurina Hauwa'u A usman jidda marubuciyar kadddara tah, gaisuwa tare da fatan alkhari a duk Inda kike , Nagode kwarai da gaske bisa kaunarki gareni , nima Ina kyawun sonki dajinki har 'cikin raina irin sosai din nan*
Page 88
Rayuwar deeni gabadaya ta canza 'cikin Yan kwanakin da basu wace asharin da wani abu ba.
,rabon shi daya samu kanshi 'cikin natsuwa da farinciki irin hk a zuciyarsa har ya manta .
matsuwa Yayi yaga yadda 'cikin jikin nablah zai bayya ya tona asirin kansa .
domin hkn shine cikar burinsa.
" sbd shi ahalin yanzu idan akwai abinda yafi so da kauna bai wuce 'cikin dake jikin nablah ba .
wato burin rayuwarsa ..... Gama wayarsa kennan da matarsa ya Mike tsaye zuwa dakin da nablah take .Jingine take akan makeken gadonsa yayinda Wani irin zazzafan zazzabi me zafi da tsuma gangar jiki , yasamu nasarar cafketa .
sakamakon ruwan saman da ake kwana da yini ana shekawa a garin Lagos wanda ya hade mata da yanayin gurin tare da sanyi gidan glass.
" cikin rawar jiki ta Kai hannuta ta dan janyo tautausar blanket dinsa dake nade a gefe daya me cike dadadden kamshi turarensa Wanda yacika mata hanci takoina Yayi Kane Kane acikin zuciyarta.
ta lullube sansar jikinta dashi .
wani irin numfashin take fitarwa ahankali me gyaraye da zafi zafi zazzabi .
.
" yayinda, ta cikin blanket din ta kudindine jikinta guri daya sosai take rawar sanyi hakoranta har karkarwa suke da junansu, har zuwa sanda deeni yashigo dakin ya tadda ita 'cikin wannan halin.Kai tsaye gurinta ya nufa da sauri ya haye gadon hade da zamo da blancket din data rufa jikinta dash.
Yayi shr tare da tsura mata rikitattun idanunshi kawai yana kallon yanayin datake ciki .
da kyar tasamu tasanya hannuta ta fexgo bargon dayake rike dashi ta sake maidashi jikinta tana cigaba rawar sanyi .
Kana ta sunsukayar da kanta.
'cikin sarkewar muryarya tace masa Ina wuni... batare da ya amsa ba Yacigaba da kallonta kawai .dan ba gaisuwarta yafi bukata ba ...
ganin yanayinta yasa shi
cewa.baki da lfy ne ?
Shr tayi masa itama taki ce masa komai tamkar yadda Yayi mata sannan taki dago idanunta .
ya motso sosai kusa daita har yana jin hucin zafin zazzabi jikinta, gabadaya tana jin yadda gigice ya rude ajikinta Amman taki dago idanunta ta dubi yanayinsa ..
yace talk to me now please what's wrong with you ?
Wasu zafafan hawaye suka cicciko idanuta kawai ta tsinci kanta da gyada masa kanta. Alamun bada da lfy ..
,take yaji zuciyarsa tayi wani irin matsanancin bugawa da karfe har yasamu kanshi da dafe tsaitin zuciyarsa da hannuwanshi duka yana cigaba da kallonta .
Yayinda gefe daya km ya daura alhakin ciwon nata akanshi .
Domin da baije ya bata sama da awanni yana hira da zeenat dinsa ba.
, may be da yanzu bbu wani abinda zai sameta .runtse rikitattun idanunshi Yayi sosai yana jin zafi sosai har 'cikin zuciyarsa , tare saukowa Daga kan gadon batare da ya sake ce mata komai ba .
" jikinsa a sanyaye ya fitce daga dakin zuciyarsa cike da tsananin tausanyinta Wanda yanzu ya zamemsa jiki .
Fitar shi da kmr minti shabiyar ya sake shigowa dakin hannushi rike da Whit lailon da ruwan roba.
, ya sake hawowa kan bed din ya km yaye bargon Wanda zuwa lokacin tuni ta kwanta ya tada ita zaune km still jikinta rawar sanyi yake .
ya ballo magani da ruwa .
" yayi mata alamun ta bude bakinta Amman taki sai miko masa tafin hannunta datayi .
yasaka mata maganin tare da jan yantsun hannuta sai dataji wani iri ajikinta sannan ta saka maganin abakinta Tasha ruwa.
tana kokari koma ta kwanta yayi saurin tarota jikinshi , muryarta Na rawa tace please...kabarni kar ka takura min dan Allah ...

YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan