💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARHPage 100
Nablah ki natsu ki dawo 'cikin haiyacinki muyi mgn 'cikin tsanake da fahimtar juna da farko kin amince da zaki bamu abinda zaki haifa wanda har muka sanyawa rayuwarmu son abinda ke cikinki.
" to meyyasa yanzu kika canza ra'ayinki alhalin duniya tagama sannin wayan nan ya'yan ya'yanmu ne nida matata ?Ilahirin jikinta da bakinta wara suke gurin cewa nidai kawai ji nake a halin yanzu bazan iya kyautar dasu ba.
. saboda kinsha wahala gurin haihuwarsu shiyasa bazaki iya badasu ko me ?
Kai tsaye taji ya 'aiko mata da tmbyr datasa ta tsura masa shanyayyun idanunta da suke cike da ruwan hawaye taki ce masa komai sai kallonsa kawai take ..
"jikin deeni Yayi sanyi sosai sbd ganin yadda yanayinta ya sauya . yarasa ta inda zai bullo mata.
ta kalleshi sosai Yayi matukar bata tausayi Amman har 'cikin zuciyarta bata jin zata amince tabashi yayanta kyauta .
" tacigaba da dubansa can km yace kina jina ko kiyi hakuri kibar mana yaran nan nida matata nayi miki alkwarin zan raba tarin dukiya biyu Na baki rabbi akansu kije kicigaba da rayuwarki .
Sosai ta sake tsareshi da shanyayyun idanunta tamkar zata cinyeshi tana mishi wani irin kallon rainin wayo.
hakan Yasa gabansa cigaba da faduwar dayake .
shima kallonta yake yana jira Daga gareta tare da mamakin canzawarta a'cikin zuciyarsa .
idan wani ya fada masa zata rikide ta dawo masa Haka wallahi zai rantse da Allah yace karya ne ranta a matukar bace tace Kai dukiya ta dama km take rudarka har kake jin Kai wani ne .
Amman ni bbu abinda za'a bani a duniyar nan da zai Saka Na iya kyautar da ya'yana har UKu ba daya ba.
ko mahaikaciya ce Ni bazan soma yin wannan dayin aikin ba ballanantana Ina 'cikin haiyacina, yakarasa fadar hk tana nuna brain dinta da yatsan hannuta.
kana tacigaba nidai Dan girma Allah Na rokeku daku barmin ya'ya Na Ina sansu nima a duk yadda suke.deeni ya runtse idanushi gam tare da furta ya Allah akasan zuciyarsa ....yasoma cizan lips dinsa da karfi .
gabadaya komai Na 'cikin duniyar nan yasoma tsaya masa Bai taba tunani sanadiyar yarinyar zai taba shiga 'cikin tashin hankali irin Haka ba.
ya dauka rashin son 'cikin jikinta datake tun farko zai tsaya a Haka ne .
Amman a kalmomin bakinta na yanzu komai ya sauya agareshi yagane shi din bakomai bane a duniya nan .
sannan ya soma fahimtar Bai isa yace zai ma kaddarsa wayo ba .
Yau din nan tazo masa da tarin abubuwa da daya farinciki dake tattare da tashin hankali mara misaltuwa .Shin yanzu ya zaiyi da kaddarar data fada masa ?
Ya'yan da zai fara samu a duniya sunzo masa da wani irin salo na daban .
yanzu mezai cewa danginsa da yan'uwa ?Hakika Komai yagama dagule masa ahankali ya juya saitin da zeenat take tsaye surusuru tana aikin barin jiki da marairaice wa .
yana aika mata da wani irin matsiyacin kallo me frigita zuciyar wanda akawa sannan muryarsa a fusace yace kinga ni ko ?
Kinga irin abinda sakacinki ya haifar mana ko ?
Me kike tunani zai faru gaba idan har taki amincewa tabada yaranta ?Zeenat da jikinta ke mugun kirrrrrrma ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka tana yarfe hannuwa .
yanzu dakin yi hakuri kin haifi wanda Allah yabaki da duk hk Bai faru ba.
da km baki samu 'cikin tsaka me wuya ba. Amman bbu komai duk 'cikin wannan lamarin ni akafi cuta yakarasa mgnrsa yana jin kunar rai acikin zuciyarsa yayinda kirjinsa ke wani irin buguwa da karfi .
Shi kanshi kuka yake son yi ko zai daina jin radadin azabar ciwon zuciyarsa keyi .banda kuka bbu abinda zeenat keyi ita kanta tasan ta cuci kanta da kanta.
Ta ruguza rayuwarsu sbd sakacinta da son zuciyarta ta Mike Daga inda take ahankali tana layi ta rungume ummi ajikinta tana matsanancin kuka.
Ummi kiyi hakuri a rayuwa nasan Na cutar daku Amman ko daidai rana daya ummi baki taba kina ba .
Sai ma sabuwar kulawa da kike bani hakika ke uwace guda har da rabi samun irin Ku ahalin yanzu zai yi wuya ummi kiyi hakuri abida nayi ki ya femin Na cutar dake domin ba irin tarbiyya da kika bani ba kennan ta sake tsanata kukanta.
ummi itama ta rungumeta sosai tana zubda hawayen tausayin diyarta arayuwa ta tsani abinda zai saka zeenat dinta zubd hawaye matukar tana da yadda zatayi.
kasa cewa komai tayi Sai aikin rarrashita datake tana shafa bayanta ..

YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan