35

9K 293 3
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 55

Cikin wani irin  yanayi   wanda kwata kwata  ummi bata taba ganinsa ciki ba ya mike tsaye tamkar may koyan magana ya bude bakinsa yanawa ummi  sallama.
    "firt lov ni zan wuce gida yasoma taku cikin   isa da kasaita don barin dakin.
, cikin sanyi murya ummi takira sunanshi DEENI.....Dan tsayawa yayi Tare da juyowa suna fuskarta juna da ummi idanunta ,ta xuba mishi kawai  Tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake  sauyawa  cikin Dan  kankanin  lokaci   .

Yasa tace Ka tsaya kaci abinci Dan da alamun kana tattare da  wunya ,inyaso  zuwa anjima Sai ka wuce gida ko...shr  kawai yayi  yana kallon umminsa.

hakika  umminsa tafi kowa sanin koshi waye Ta fannin halayyarsa  da abinda ke tattare dashi.

Sai dai ,shi sam baiji zai iya sawa cikinsa komai  a halin dayake ciki  damuwarsa dayake tattare dashi  , kadai ya ishe sa" ba Sai yaci wani abu  , yafison  yaje gida kawai domin  yana bukatar sake nazari akan maganarsa da ummi.
' Dan haka   ya Dan narkar da fuskarsa  alamun baya da bukatar cin wani abu  .
  "bata rai ummi tayi ganin yadda yayi ,sannan ta Mike tsaye ta nufi hanyar kitchen .
  kabani  nan da minti goma yanzu , zan gama hada maka abinda zakaci kaji sojana ta fadi haka tana karasa shiga kitchen.
  yasan halin ummi sarai tamkar wuyan cikinsa  muddin tace Ga abinda take so ,to kuwa bata  muradin mutsu ko wani  jayyaya " Dan haka jikinsa a sanyaye ya juya zuwa ga hanyar step .

'Ahankali yashiga dakinsa" tsit ko Ina  ba  motsin komai "inda sabo ya rigada yasaba da rashin son hayaniya. daman shi mutun ne .
  "ba mai san hayani ba ballanantana km a part dinsa" komai yana nan tsab kmr yadda Ya bari  tamkar yana rayuwa a cikin dakin "wanda yasan wannan  duk cikin kulawar    umminsa ne sbd macce mai tsananin tsafta  da kyankyami .
  " kai tsaye bedroom dinsa ya wuce  ,yasoma  cire kayan jikinsa yaja towel ya daura Tare da shigewa bathroom ya sakarwa jikinsa shower yana fitowa Bai wani tsaya shafa mai ba .
 
ya bude wordrob dinsa.
nan ma komai tsabtsab iske komai  Sai kamshi turarensa dake tashi a gurin ,  wani irin sanyi da dadi  yaji a ransa.
  " take kadan daga cikin damuwar dake tattare  dashi ta ragu .
'ahankali yasa hannu ya zaro jallabiya  coffee colour ya zira a jikinsa ba karamin kyau ta maisa ba .

fitowa yayi daga  dakin nasa ya wuce kai tsaye ainihin main parlour din gidan ,ummi ya iske zaune ita da Zeenat suna magana kasa kasa.
"  duk da Bai san abinda   suke Tautaunawa  ba ,amman  jikinsa yabashi   maganar shi suke yi   .
Dan haka "kallo daya yayi musu ya dauke  idanushin akansu' batare da yace komai ba ,direct to dinning area ya wuce , yana jin yadda kamshi abinci ke tashi ta koina a gurin da dukkanin alamun umminsa tagama shirya masa abinci kmr yadda tace.
, ya zauna ba dan yana bukace da son cin wani abu  ba Sai Dan faranta ran umminsa.

shr yayi Tare da runtse idanushin yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri 'ahankali ya kamo lip's dinshi na kasa yana dan cizawa sannu sannu.

  Maganar da  Ummi keyi da Zeenat kuwa , bawata magana bace, illa fada da take sake yi mata akan abinda tayi Tare da bata shawarar  hanyoyin da zatabi gurin  shawo kan  mijinta cikin sauki .
, sosai jikin Zeenat din yayi sanyi likis..
ita kanta tasan" inda ummi bata kasance er,uwa,ce Ga mahaifiyarta ba ,hakika   yaci ace yadda Ta zubar da cikin jikinta ummi  tasa danta yakarasa tsinke igiyoyi aurensa akanta.
amman Sai gashi  hakan bata faru ba .
Sai ma nusar daita da take akan yadda zata sake mallakarsa a tafin  hannuta.
Ummi dabance acikin mutane km zuciyarta may kyau ce ba kmr ta irin sauran mutane  ba km Allah yayi ta may tsananin zumunci ce .
  ummi   takarasa zanceta " da maza tashi kije ki kula da mijinki.
  "km cire wannan tsoron nasa danake hangowa   acikin kwayar idanuki.
Da kyar  Zeenat tasamu ta mike Tana may  dagawa  Ummi  kai alamun taji .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now