39

9.5K 270 3
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO

Page 59

Al'amarin gidan kuwa gabadaya ya sake canzawa  tun daga kan mutane dake rayuwa  a cikin gidan har zuwa Ga gidan  karan kansa  .
Dan gabadaya DEENI ya gyara kowa Ina a gidan inda ya sake fadada girman  dakunan dake kasa  tare da kawatasu da ado  .
Wanda  ,a halin yanzu  yakoma  amfani da dakin sama da kasa .kallo daya zakawa gidan ya birgeka km  kasan ya fita daban da sauran gidanjen dake cikin  estate din.

Ummi bata Kira number Salmah ba sai byn data sallami shafa da kwana biyu sannan takirata

Ranar da shafa ta tarkata tabar gidan ranar  itama Zeenat   tashi da zumar dawowa dakinta na kasa wanda DEENI ya cire mata ,dan haka bata tsaya wani bata lokaci ba tasa laraba tayi mata komai ,tare da abubuwan ta masu mahimmanci sai abinda baza'a rasa ba tabari a dakin sama .itama takoma amfani da daki biyu a cikin gidan.

Matashiyar budurwa ce Tare da yayarta  tsaye  abakin titi .
suna jiran mota ' sun dauki sama da rabin awa tsaye  a haka suna jiran abin hawa amman kowace mota tazo wucewa"  cike take tap da mutane .
,sakamakon cunkoson  ababen hawa da aka tashi dashi a garin Lagos.

, aunty me zai hana muhau machine ne   , kinsa fa inda zamu da Nisa  sosai .
  , saboda ke da zaki dawo .
  Dan naga yanayin garin yau sai a slow inji  cewar  nablah.....

, aunty Salmah  ta dan juyo ta kalli gefen inda  sisinta  ke tsaye   tare da cewa  'shikenan nablah  muhau machine din kawai Dan nima bana son dadewa .

gaba  kadan suka  karasa  wajen yan machina,
    malam dan Allah lawansi bustop zaka kai mu, inji cewar aunty Salmah.
mai okada ya  gyara tsayuwar machine dinsa ta yadda za su samu damar hawa ..

Kin hawa aunty salma tayi sai ma tmbyr mai okada take da  nawa zamu bayar tukun.

  , Atakaice dai  muna kai mutun daya  a naira dari mutun biyu dari da hamsi aunty Salma tace  Shikenan ke nablah  fara hawa.
" dayake kaidar Aunty salmah kennan.
muddin da kanneta zata hau machine bata yarda tafara zama a farko, sai dai tace su hau gaba ita km  ta zauna a  baya.

   'Ahankali Suka dane machine"
dai dai bakin  filling station din dake   lawansi, suka sauka aunty Salmah ta bude jakarta tabawa Dan okada kudinsa .

tafiya   suka soma yi zuwa inda zasu shiga motar da zata kai su surelere .

Suna tafi suna hirarsu abin sha'awa   har suka isa wajen shiga motar Masha.

, daidai Bakin get din da zai kai ka ilori Street suka sauka , tafiya kadan sukayi suka isa inda zasu .

aunty Salma tasa hannu ta tura get din gidan wanda  koda yaushe  haka yake a bude, .

Da sallamarsu suka karasa bakin net din latifa  .  Aunty Salmah na kwalara mata Kira latifa latifa..  Amman shiru ba amsa yayinda   kofar ma take  a kulle .
Tsayuwar Minti goma sukayi  kafin daga  baya suka jiyo sautin  muryar latifa .
ku biyo  ta nan kofar  kitchen,an kulle nan ne sbd yara .
" zagayawa  sukayi ta kofar kitchen  suka  shiga.

Latifa   naganin su tasaki murmushi ,kai kai gsky dai Salmah kunyi latti wlh    kin kuwa san nisan unguwar da zaku kuwa ?

aunty Salma tayi dariya  wlh kinsa halin mutumin naki  hukuma ne sai da rarrashi .
duk shi ya bata mana lokaci , gashi Bai fita da wuri  ba.

, to shikenan sai kuxo Ku tafi   tun rana batayi ba .        "ai ma hajiyar takirani  tun sassafe tamin kwantance yadda zamuje can din " da ,na so mu wuce ta mushi ne saboda akwai mota mai zuwa  can direct  sai dai kinsa jakar nablah na nan shiyasa dole sai  munbiyo tanan din .                     
 
Latifa tace ok  ina zuwa ku shiga daga ciki  bari na amso sako  dana aika  .  

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now