72

13.3K 373 3
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO


~DEDICATED TO~
*HAUWA A USMAN*
     _JIDDARH_

Page 92

Wanka tayi Zuciyarta cike da tunaninsa  ...

Ta fito fuskarta a d'aure tana  ciccin magani, wanda kafin fitowarta oready deeni ya gama shirinsa tsab  ita kad'ai yake jira ..muryasa a sanyaye yace Kin hanzarta fa yau zamu koma gida domin jirginsu  first love Na gab da sauka..

Take taji Gabanta Yayi mugun faduwa hankalinta ya tashi matuka da jin abinda yace ,ahankali km  zuciyarta tashiga harbawa da sauri da sauri .
cike da sanyi jiki tasoma Shiryawa itama  'cikin wata  doguwar rigar redymedy zuciyarta Na sake narkewa akan tausayin kanta .

Ta zauna  tare da  tsura masa shanyayyun idanunta .
dan murmushi ya sakar mata, tare da  kashe mata idonsa d'aya yace " lafiya Mrs Deeni naga duk Kin hargitse ? 
Rasa yadda zatayi ne yasa  cikin shagwab'a tace " ni yunwa nake ji, kitchen ya nufa ya had'o mata tea mai kauri, har ya dawo ya zauna a gefen ta, hannunsa rik'e da cup din tea amma bata sani ba,a kan bed site ya aje tea d'in .
zuba mata lulu eyes d'inshi yayi had'e da hura mata iska a face dinta

Naunauyen Ajiyar zuciya mai k'arfi ta sauke, bata ce masa komai ta zuba masa shanyayyun  idanunta, ganin ganin da suke yiwa juna yana neman sanya masa kasala ne ya sanshi kawar da kansa gefe, ya mik'e tsaye daga kan gadon zai fita tayi saurin rik'o hannushi juyowa Yayi da kanshi ya sake  tsareta da rikitattun idanunshi yana kallon fuskarta batare da yace mata komai ba .
cike da sanyin jiki , muryata har d'an rawa tayi gurin cewa please let me stay  here ka barni anan na nacigaba da zama  tsoron komawa gidanka nike ....

Sort hannunta dake kan damtsen hannushi yabi da wani irin kallo batare da yace komai ba
", da sauri ta sakeshi ganin hannuta yake kallo  ta sunkuyar da kanta kasa a hankali ya koma ya zauna kusa da'ita sosai akan gado wani irin murmushi tayi wanda suka  bayyana fararen hak'oranta da wushiryarta saboda tunaninta zai barta anan din ne kamar yadda ta buk'ata, cikin wata irin murya mai karyawa namiji gab'ob'in jiki tace "  thank you so much Dear,  tsuntsun soyayya ...sai da numfashin sa yakusan d'aukewa saboda yadda tayi maganar...da kyar ya iya controlling d'in kanshi ya dukar da kanshi kawai yana gyara gaban rigarsa hakan nan taji tana 'cikin farin ciki da jin dad'i  cup d'in ta dauka batare da ta cire idanunta akanshi ba zata kurbi hot tea din daidai ya d'ago kanshi da sauri Ya rik'e cup d'in hannuta  yace"is so hot.. wani irin uncontrollable smile take masa tana kallon fuskarshi da sauri ya karb'i cup d'in daga hannuta yana juya tea d'in da wani cup saboda Yayi tsanyi ,yana tunanin a ranshi sunan data kirashi dashi ahankali ya furta sunan akasan ranshi tsuntsun soyayya.

To me wannan sunan yake nufi ?
,  yadda yake mata ne ya sata afkawa 'cikin duniyar  tunanin kodai deeni ya fara sonta ne da gaske kmr yadda take tunani ?

Take ta Kawar da wannan tunanin  ganin hkn ba me yiwuwa bane atsakaninsu .. ta d'an juyo ahankali 'cikin sanyin jiki  ta kalli fuskarshi shima  ita yake kallo ganin yadda ta rik'e kuncinta ta zuba masa shanyayyun idanunta da sauri Ya d'auke kanshi Ya cigaba da juya tea a hankali ya d'ebo a spoon ya Kai bakinshi yasha jin babu zafi,  Ya juyo yayi facing d'inta sosai ya debo a spoon yakai daidai  tsaitin bakinta wani irin murmushi tayi ta nuna kanta tare da cewa u won't to feed me Deeni ..?

Gyad'a mata kanshi Yayi kawai batare da ya iya ce mata komai ba .. wani irin  tattausanshen murmushi ya kufce mata  ya bayyana sosai akan fuskarta hannuta d'aya ta daura akan kafad'arsa domin son shagaltar dashi sai da numfashinsa ya kusan tsayawa lumshe rikitattun idanunshi Yayi sannan ya bud'e. murmushi tayi tare da turo masa dan  karamin tsukaken bakinta alamun yabata da kyar jikinsa a sanyaye yasamu Yayi controlling din kanshi ya Kai spoon d'in dake cike da tea bakinta yana mamakin yadda ta dawo masa ta kara sakin jikinta dashi hadiye tea tayi tare da lumshe idanunta dan ji tayi tamkar ba tea ta Sha ba ..

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now