73

13.8K 347 2
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

      Dedicated to
*HAUWA A USMAN*
       (JIDDARH)



Page 93

Tare da aika mata  da wani irin kallo me cike da tsansar  jin haushin abinda ta aika .
ba zeenat dake tsaye  rike da kuncinta  ba hatta ummi hankalinta Yayi mugun tashi akan abinda deeni Yayi .
" domin bata tunanin  deeni zai iya koda zagin zeenat bane akan nablah agabanta .
ballanantana mari, ba daya ba har biyu ajire ..

wani irin kallo zeenat ke bin nablah dake kamale ajikin mijinta km wanda   tafi so fiyye  komai dake 'cikin duniyar nan .
Ahankali tasoma yin kasa kasa  'cikin slow motion ta zauna jagwab akan kujera datashi tana cigaba da kallonsu zuciyata Na mata wani irin zafi da radadi .
kishin mijinta ne kawai ke cin ranta da kirjinta take zuciyarta tashiga  harbawa da surin maseefa ..ta rantse idanunta gam dan bata kaunar sake daura idanunta kanshi dake like da juna tamkar wasu miji da mata ..

Yayinda nablah dake jikin deeni  tasoma kokarin fexgewa Daga jikinsa Amman yaki sakinta sai kallon zeenat yake da rikitattun idanunshi. domin  ita kanta nablah  wani irin razananniyar  tsora ne yashigeta tashiga tunani kardai da abinda take tunani ke shirin faruwa ?
Kennan gaske ne deeni ya fada tarkon sonta ko yaya?
  Matarshi fa ya mara agabanta akan 'cikin jikinta wanda tasan bashine mutumin dayayi mata ba idan kuwa hk ta faru bata San yadda zatayi da rayuwarta ba nan wani kuka me karfi ya kufce mata ..

Ahankali deeni ya dauke idanunshi akan zeenat batare da ya kalli inda ummi ke tsaye tana aiko masa da kallon mamaki ba yayi hanyar step da nablah a barin jikinshi ..har suka wuce zeenat batasamu bude idanunta ba sai ma wasu Hawayen takaicin rayuwa suka samu nasarar biyo kuncinta gabadaya komai ya tsaya mata cak.

To me hkn yake nufi?

Me take shirin Gani km yau a gidanta Daga dawowarta ?

Allah Allah ka duba min al'amarina ....
Ka tausayawa rayuwata kamin maganin maseefar dake shirin kusantoni da al'amarina gabadaya kada kabari wata maseefa tashiga tsakanina da mijina .Hk  ta dinga  fada  a 'cikin ranta ummi ta matso sosai kusa daita tana goge mata hawayen dake silalowa a kuncinta batare da tace mata  komai ba .
Domin  ita kanta taji mugun  zafin marin da deeni Yayi mata a gaban nablah,  amman tasan abinda zatayi ..

Har sanda deeni yakaita dakinta  kuka nablah take Na fitar hankali sbd  gabadaya a tsorace take da ganin yanayin  zeenat da ummi.
  'cikin natsuwa  yakarasa ya  zaunar daita akan gadonta hade da janyo karamar stood din dake gefen bedside dinta ya zauna ya kamo hannuwanta dukka'cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali tare da  tsurawa beauty face dinta rikitattun idanunshi yana kallonta.
zuciyarsa Na masa  wani iri tsalle tamkar zata tarwatse ta fasa kirjinsa ta fito.
muryarsa a sarke ya Kira sunanta ,ta dago shanyayyun idanunta ta zuba 'cikin nashi  kukan ya isa hk ....Ko wani guri Na miki ciwo ne?

Ta girgiza masa Kanta batare da tace komai ba.
Ok  ki natsu yanzu kibar kukan nan hk  kinsa bake kadai bace damuwarki zata iya shafar lafiyar bby nah .
still shr tayi taki cewa komai yayinda km aranshi ya dinga jin zafin hasarar da zeenat taso yi masa.

meyasa zeenat bata tausayin takala da rabarsa  ?

Meyyasa take kyamar talaka da nisanta kanta Daga gareshi ?

Meyasa  girman Kai da kudi ke fusgarta da yawa.. har ta dinga manta kalar tarbiyar da umminsa tabata?
shi yasan  Sam wannan ba kalar  tarbiyar umminsa bane sannan km ba halin mahaifiyarta  ta dauko ba mace me tsananin hakuri da son mutane .
Shi ya rasa Ina tasoma wannan halin nata Na girman Kai da Kin talaka da nuna kowa bakomai bane  wanda ko acikin family itace lidar kowa . gabadaya zuwa  yanzu halayenta sun sake  canzawa fiyye da kowani lokacin  Wanda  can da Bai santa da hkn ba Amman yasan hakan ma  yana da nasara da sababbin kawayen datayi .
Naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana jin a ranshi komai zai faru sai dai ya faru Amman wlh  kan 'cikin jikin  nablah sai dai   sirrin boye ya fito filli kowa yasan abinda ake ciki .
....Ya kamo fuskarta da hannuwashi duka yana kallon 'cikin kwayar idanunta ya dinga jin aranshi  da yana da iko akan kanshi, da dauketa kawai  zai yi gabadaya Daga kasar ,zuwa wata kasa daban su cigaba da rayuwarsu hankali kwance 'cikin natsuwa yashiga tunanin rayuwar da sukayi a sabon gidansa ,rayuwa me cike da jin dadi da natsuwa wanda wani lokaci har manta yake da matsalar komai ....
bakinsa ya Kai daidai  kan lip's dinta zai tsotsa tayi saurin  kawar da fuskantar tana yatsinawa  tare da  zubawa plate din abincnta data dibo ajiye da niyar ci  idanunta ahankali ya maida idanunshi zuwa Inda take kallo din .
ya tashi ya  dauko mata plate din  abincin  ya daura  kan tsood din daya tashi ya zauna a gefenta ,kici abinci please...Babu wani westing time  tasoma  ci dan  wani irin yunwa take ji tun tea data Sha agidan glass ne ke cikinta.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now