💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
*Assalamu alaikum warahmatul Allah inawa dinbin masoya wannan littafin barka da sallah da fatan kunyi sallah lfy Allah ya karbi Ibadunmu da mukayu cikin Ramadan Allah Yasa muna cikin bayin da Allah ya, enta daga wuta zuwa jannatul firdaus Ameen ,kmr yadda nace zan cigaba da type din wannan labarin nawa byn sallah, to a yau ne alkawari Allah yacika Allah ya nuna mana lokaci ,hakika may hankali da tunani ne kadai zai Gane yadda duniya ke gudu, Allah Yasa mudace yabamu ikon cikawa da kyau da imani ,km Allah yabamu ikon aikata ayyukan alkhari*
Page 54
'Ahankali Deeni ya dauke rikitattun idanushin daga cikin idanun umminsa ya maidasu kan inna dake tsaye tana fama , babatu da sambatu iri iri 'km duk cikin taron mutane dake zaune a parlour bbu wanda yayi yunkurin dakatar daita daga maganganu da take .
zuciyar Deeni cinkushe da haushi hade da takaicin inna" bakinciki ganinta ke sake nunkuwa a kasan ransa yayinda yashiga da zuciyarsa wani irin zafi da suya zuciyarsa ke yi.
" so yake ya murje idanunshi Tare da cire kunyar jamar dake zaune a gurin, sannan ya zage kunjinsa ya zabga mata rashin mutunci fiyye da irin wanda ta iya .
,amman Ina...tuni idanun umminsa dake yawo a kansa" yasa ya kasa aiwatar da komai sakamakon gargadin dinsa datake ta hanyar kwayar idanunta .dan haka daya rasa yadda zaiyi ya fanshe tarin wulakancin inna gareshi,sai kawai ya shiga aikawa inna da wani irin mugun Kallo may hade da harara .
Wanda yasa ,ita kanta inna dake tsaye har lokacin sake jin haushin DEENI da takaicin irin kallon kaskancin da wulakancin dayake aiko mata dashi .
"Km hakan yayi sanadiyyar kara hassalata , dan haka a tsawace Tace ni daina kallona ,ka wani tsareni da wa'yan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , kana aikomin da kallon wulakancin to bada ni kake da wannan uwartaka ta zaune kake... ehee.. takarasa fadar haka tana may jan mugun tsaki a fili tare da soma kokari kamo hannun Zeenat .
Ke tashi mu tafi , can sashina ko kya samu ki maida jikinki ki murmure daga wannan bakar ramar da kikayi " inna tasoma kokarin mikar daita Zeenat tsaye .
Yayinda Zeenat din km taki mikewa Sai ma sake cure jikinta da tayi gurin guda alamun babu inda zata .,au bazaki mike mu tafi can gurina ba ,kinfi son ki zauna inda za'a dinga miki izaya da tsotse miki jinin jiki.
Dan zama da wannan mugun azalumin kadai ya,isa yasa jinin jikinki ya kafe batare kowa yasani ba "ni tashi mutafi .,juyin duniya nan inna tayi da Zeenat kan ta tashi su tafi can part dinta " amman kememe Zeenat taki tashi .
ganin haka yasa inna sake tunzura, ta cigaba da tsayuwarta tare da surfa masu maseefa iri iri km har lokacin bbu wanda yaiya cewa komaibig dady ne "ya dan dago idanushi yana duban sashin da inna ke tsaye Tana surfa maseefa ,ya xuba mata kawai domin shi kansa big Dady rasa me zai cewa inna yayi...
' kusan minti goma ya dauka Yana kallonta batare da yayi yunkurin dakatar daita ko ce mata wani abu ba ' kafin daga baya ' ya gyara zamansa Tare da numfasawa. cikin tsantsar ladabi da laushin murya yasoma magana, Dan Allah inna kiyi hakuri ki tafiyarki abinki "tunda yarinyar nan Ta nuna bazata biki ba.
, Say da inna ta tabe bakinta tukun sannan tace "yo Ai ka kace min nayi tafiyata man " tunda fadeela da danta sunfini daraja da kima a idanunku" duk irin wulakanta min jika da wannan banza yaron nata yayi baku Gani ba Sai na laifin zakugani .
,big dady sam Bai damu ko jin mamakin abinda inna tace ba, dan yasan kadan daga cikin aikinta. domin zata iya fadar fiyye da abinda yafi haka ma.

ESTÁS LEYENDO
AUREN SIRRI COMPLETE
Misterio / SuspensoMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan