10

11.7K 436 2
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 19-20

Shiyasa kaga bazan iya kai" kaina gareta ba  da sunan Ina sonta , bare tamin salo .

Nan km yayi ta zazzagawa Fk maseefa hade da  cewa ai  shi yaja masa duk  wulakancin da'aka masa .

Fk yace kwantar da hankalinka   kabarni daita kawai ,nasan zata yarda ma ,.
kawai dai itama so take ta nuna mana ,itama macece , nasan jan aji ne kawai na mata Amman ita din wa dazatace bata sonka ,Ina rai inshallahu  zamuyi nasara.

Cikin fushi da jin haushi deeni Yace in taki yarda ka kyaleta kawai , yarinya sai kace wata  gold sai wani yawo akamin da hankali akanta, yaja tsaki hade da kashe wayar batare daya sake jin abinda fk zai ce ba .

Kwana deeni yayi da tunanin hade  da zullumi halin da zai tsinci kansa idan  yarinyar nan taki yarda dashi, duk shi Gani yake ba sonta yake ba. zai dai yi aure ne kawai saboda umarnin umminsa, bugu da Kari ma, bazai iya kaskantar da kansa wajen mace ba ballanantana har ya kai shi ga furta kalmar so.

Har zuwa wayewar garin ya cigaban mamakinta  ganinta yake , tamkar yau aka haifeta, sannan har zuwa yanzu kallon karamar yarinya yake mata,  ashe tasan abinda take yi ,uhmmmm  uhmmmm ahankali ya dinga sauke ajiyar zuciya, wai zatayi tunani akai ya sake tunawa da kalmar data fadawa fk to da ko da uban wa zatayi tunani ya furta hakan a kasan rashi .

kwance take akan bed din ummi  Amman ba bacci takeyi ba ,hannuta rike da wani  English novel  mai suna ,mumy why sanye take cikin kananan kaya, pencil  jeans da riga iya gwiwa a natse take karatunta dan tana jin dadi labarin yarinyar ciki litattafin ta birgeta kwaira ,ta yadda take kokarin kwatarwa kanta enci saboda mahaifiyarta ta hanata auren saurayin da take son ..
Cikin isa da kasaita  yashigo dakin , tana jin motsen bude kofa Amman tashare dan batason abinda zai  katse mata karatunta .

Jin kamshin turarensa yasa ta dan dago idanunta suka sauka akansa , ganinsa yasa  ta dan mike daga kwanciyar datayi, tasha jinin jikinta   bata san meke sata jin yawan  faduwar gaba ba, a duk sanda taga yaya DEENi .
ta gaidashi batare daya kalli inda take ba , ya amsa mata a ciki ,km  cikin isa da takama sannan  a takaice , tamkar dai yadda yasaba dan baya son duk abinda zai  sa magana tayi tsawo atsakaninsu .
sai dai ita kam tsintar kanta  tayi da  zuba masa idanunta, tana binsa da  wani irin mayyen kallo , cikakken namiji ne sosai mai ji da kansa , ko a tafiyarsa zaka shida haka.  gabadaya bbu wata  alamun ragwanta atare dashi .kana ganinsa zakaji ya birgeka ,daman aikin da yakace shi kennan wato  jami'in tsaro .

Har suka gaisa da ummi dake tsaye fitowarta kennan daga bathroom  ya juya da niyar barin dakin,  idanun Zeenat na kansa tamkar zata ya dawo ya zauna kada ya fita saboda tsoron masu farautarsa ,takasa dauke idanunta daga kallonsa take taji wani irin masefaffen kishinsa ya diram mata zuciyarta ta dinga rawa bata idanunta a kansa ba sai data daina ganinsa  .

Ummi tabita da kallo tausayi  tace inkin gama kallon nashi sai   ki tashi ki hado masa abinsa ko kawai soyayya aka iya ba'asan tattali ba , Zeenat ta dan turo baki tace ni dai ummi kwanan bansa abinda na miki ba  komai nayi sai kin min fada, ki dinga ganin laifina , nifa bashi nake kallo ba , ummi tace eh ai nasan bashi kike kallo ba kuruwarsa kike kallo jairar yarinya kawai ni tashi ban guri  .

Washegari

Zeenat tarasa dawa zatayi    zance yaya DEENi taji dadi kuma yaba shawara tamkar yadda zuciyarta ta aminta dashi  ,ganinta duk wanda ta nufa da maganar baza tasamu goyon baya ba ,kmr dai yadda ummi tayi ,
Maryam ce ta fado mata a rai ,dan haka tashirya taje har part din su.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now