51

9.5K 312 2
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO

Page 71

Karfe takwas daidai nablah ta sake fitowa main  parlour din domin xuba musu abinci   suna zaune  su dukkansu , har deeni suna hira.
takaraso har dining area .
jikinta a sanyaye   tasoma xubawa ummi da zeenat har  ma da safeena Abinci Amman taki xubawa deeni dake zaune yana chatting a wayarsa ..asalima ko  kallon inda yake zaune batayi  ba ballanantana tasan da zamansa .

,Shima bai wani damu da ganin yadda  ta shareeshi ba .
,Sai ma gyara zamansa da yayi sosai  "yana son yaga iya gudun ruwanta.

,tagama duk wani  abinda take  ta juya ahankali  da niyar barin parlour.
tayi taku daya zuwa biyu taji an fincikota ta baya .
, ahankali  ta juyo a sanyaye dan ganin ko waye ya rikota hk.
, aiko juyowarta keda wuya.
  taji saukar mari tasssss akan fuskarta .
zeenat ce da wannan aiki  nablah tasa hannuta ta dafe  kuncinta daidai inda taji saukar marin tare da tsare   zeenat  din da shanyayun idanunta tana kallonta dasu...
take   Hawaye suka shiga sintiri a kuncinta sharrrrrrr tamkar an bude pompo ... Ba nablah da,aka mara ba hatta ummi da safeena Sai da saukar marin  Yasa suka ji shock  jikinsu  ......deeni  dake hakemce agurin  ko gezo baiyi ba ,sai ma very gud da yace a zuciyarsa ... hankalinsa kwance yacigaba da operating din  phone dinsa cike da jin dadin abinda Zeenat tayi mata..

ke.... ashe Yar iskace bansani ban sani ba?
,mijin nawa ne yazama abun wulakantawa da bazantarwa a  gurinki .tsabar kin rainani .

  dan ubanki shi bai isa ki zuba masa abincin bane ko me kike nufi?
Takarasa mgnrta tana may sake  ciro hannunta  zata kara mata wani marin... ummi tadakar daita . Kull karki sake ki km marin Yar,mutane .

Aiki tazo yi fa, ba bauta ba.
Wannan Ai  wulakanci ne da tsagwaron  rainin wayo zalla  ?
Me ma yayi zafi dayakai har  da duka?
da bata zuba masa abinci ba  ke aikin me kike  ?

,kinji min rainin  arziki kawai Naga mijinki ne bana ba .. can km ummi ta sausauta murya
A,a Zeenat  nifa banason irin Haka .
abinda kasan idan an maka bazakaji dadi ba to karka soma yiwa wani.

ran zeenat ya kai kololuwar gurin  baci  har wani duhu duhu take Gani tsabar takaicin abinda ummi tayi mata a gaban may aikinta..
dan hk cike da  fushi tace  wlh ummi duk ke kike daurewa  yarinyar nan  gidin yin iskancin duk datagama .
Tare da   yiwa mutane kallon Gani Gani  da rainin hankali, wlh tun wuri idan tasan ba zata  iya yin  aiki dani ba ,taka gabanta .
inda km tacigaba dayin irin  wayan nan iskancin  wallahil azim zan gyara mata zama acikin gidan dan bazan dauki rainin hankali ba  .Ta juya fuuuuuu tasoma kokari barin parlour .

Nablah dake tsaye har lokacin  jikinta Banda rawa rawa bbu abinda yake ,yayinda Hawaye dake  idanunta ke cigaba da silalowa.
Cike da tausayin kanta  tasa byn hannuta  tana goge Hawayen  wasu Na sake zubowa.
ummi da ranta ya gama baci matukar  ,tace yi hakuri kijin nablah .
" nablah ta girgirza mata  kanta kawai batare da  amsa ba .

Zo ki zauna kici abinci inji cewar ummi da kyar  nablah ke daga kafafunta da suka gama sagewa tsabar takaici da tashin hankali datake ciki . safeena ta Mike ahankali tare kamo hannun nablah 'cikin nata  tana bata hakuri ,ta zaunar daita tare da turo mata plate din abincinta datasoma ci gabanta tana sake bata baki ,ummi ma hakuri taita bata.
,duk wannan abin da suke mata baya gabanta hk  km bai wani birgeta ba .
Dan gabadaya Hankalinta baya jikinta .. tunaninta  ya tattara ne akan  yadda zatabar gidan ta hutawa rayuwata.

,akan wani dalilin zata zauna a maidaita tamkar  baiwar Ai talauci ba hauka bane km ba,a akan aka soma zuwa aikatau ba  ,duk yadda safeena tayi daita akan  taci abinci .
kasawa ci tayi Banda bakinciki bbu abinda ke dawainiyya zuciyarta .  Ta ya'ya mijinta Na mata rainin wayo ita km ta dinga wulakanta ta..sbd me...Ta tmbyi zuciyata ..take zuciyarta ta bata amsa da ,sbd ke talaka ce ....

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now