54

12.6K 330 6
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO


Page 74

'sannu ahankali  nablah ta dinga samun sauki sakamakon irin kulawar da ummi  ke mata ..

Allah sarki ummi bawar Allah duk wani abu datasan ya dace tayiwa nablah ,amatsayinta Na Virgin  wacce  akayiwa shigar sauri . wanda ita kanta nablah batasan dalilin dayasa ummi take mata hankan ba .
dan bakaramin kulawa ummi take  bata ba dangane da aika aikan da DEENI yayi mata  .
dan yanzu bbu inda bata takawa da kafafunta   .

Wanda  hatta kb ba'a barshi a baya ba wajen zuwa duba nablah .
Tare da kayan dubiya daidai karfinshi .Ya Mika mata  ledar dayazo mata dashi may ruwan yellow da ratsin baki baki  ajiki .

'Ahankali' nablah Tasa hannuta ta karba hade dayi masa  godiya  jin dadi.
koda bata bude ledar ba idanunta sun gama gane mata abinda kB yazo mata dashi
,kankana ce da ayaba sai abarba a 'cikin ledar.

Yayinda  hakan  yayiwa nablah dadi Sosai har a 'cikin  zuciyarta, hakan km har 'cikin ranta taji kb ya birgeta matuka.
dan Haka ta sake sakin jikinta dashi sosa suna tashan hirarsu 'cikin Nishadi da annashuwa .

'cikin Haka deeni ya dawo daga office on expected ya gansu tsaye abunsu hankali kwance   suna  sheka dariya.

yayinda kb ke tsaye da kodadden wandon Jeans da rigar polo ,tsab dashi  .
Dan Shima gayen  bbu laifi   yana da  nashi kyau daidai gwargwado ..
sai dai ina ..kwata kwata Bai  kamo kafar DEENI  da  komai Na rayuwar duniya ba.

wani irin buguwa kirjinshi yayi da karfi gaske kanshi yayi  masa nauyi tamkar zai tarwatse sakamakon ganin nablah da kB da Yayi tsaye suna wa juna murmushi.

Mamaki da tashin hankali ne suka caki zuciyarsa a lokaci daya.
Ahankali yacigaba da takowa 'cikin takunsa nan nasa may cike  da kasaita.
da jin shi wani ne.

Ta kasan idanushi yake kare musu kallo tsab tare da sake  mamakin yaushe ne  shakuwa  may karfi irin hk Yashiga tsakaninsu batare da da sanin ba .

har yazo kusa da Inda suke tsaye, basu lura dashi ba.
  " Sai daya zo daf  da shige su ne nablah ta ganshi .sbd fuskarta dake facing dinsa .
tsam.. Tasha   jinin jikinta da irin kallon kasan idon dayake aiko musu dashi.
Dan Haka batare da wata damuwa ba.
Ta dan matsa gefe  kadan  domin bashi hanyar wucewa.
dan dama  tsaye take abakin kofar da zai Kai mutun ainihin main parlour din gidan.

har yashige  ciki idanunshi basu daina hango masa ita Tare da wani nmj   tsaye   Wanda bashi bane.

kai tsaye dakinsa ya nufa ya bude fridge ya ciro ruwan   faro  may tsanyi .
yakafa robar abakinsa yasoma Sha  bai ajiye ba Sai daya shanye ruwan  Tare da yin flinging  da robar gefe.
  ya sauke naunauyen ajiye zuciya  .
yaje ya kunna AC da TV kana  ya zauna  kan kujera  yana fidda  numfashi sama sama gabadaya duk wani farinciki daya dawo dashi gidan"  ya nema ya rasa.

zaune Kai yake  akan kujera yana aikin jijiga kafafunsa a kasa tare da xunduma kanshi 'cikin  tunani na  gaira ba dalili .

Shr yayi tare da   xubawa TV parlour,sa , idanu kawai .
Wanda idan ba tsayawa mutun yayi   masa   kallon tsab .
zaka iya dauka a zahirance abinda  da'ake gabatarwa a TV yake kallo ...sai dai abun ba hk bane .
Idanunshi ne kawai  akan TV Amman hankalisa gabadaya  da tunaninsa  yana waje inda ya baro nablah tare da wani   .wani may wanki gidansa...

A zuciye ya furzar da wata iska may zafi yana jin haushin kansa da kansa .
taya  zai zauna akaron banza kawai yana tunani yarinyar da Bai da tabbas din cigaba da rayuwa daita .... amman duk da Haka abinda yaki bacewa a idanushi .... to me hakan yake nufi ?
meyasa naji  bbu dadi sanda na ganta tare da kb" yaje howa zuciyarsa tmby ?

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now