💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 60
'Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne kesata yin haka.
,haske taga ya garwaye parlour gabadaya 'koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba.
wani irin kamshi ne mai azababen dadi yake kusantota ,har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tukarowa parlour zuwa indasuke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah .
har zuwa sanda mamallakin kamshin ya karasa yashigowa, gabadaya parlour ya canza wani irin cent na daban", take gabanta yashiga dukan uku uku gashi tana san dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan azababen kamshi Amman takasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi ballanantana tasan kowaye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon kanta dake Duke akasa har lokacin.
Ta kafe teas din parlour da ido ".Ta kasan idanunta ta hango wando jeans. wanda hakan ya tabbatar mata da mammallakin kamshi turaren nan namiji ne .
"duk da bataga komai nashi , baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi.
'ahankali yake takowa zuwa inda ummi take zaune .Muryar ummi taji tana cewa ka fito son ?
tun da zu muke Jira ... matarka tace wanka kake yi ,'ahankali ya juyo ga mahaifiyarsa yana kallonta sannan yadanyi murmushi gefen baki .
hannunsa yasa ya dauki remut ya canza channel zuwa ta kallon Ball sannan ya Mike kwance kan three site hade da cewa gani first lov anything for you my beautiful mum...
Ummi ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace sannan tace kai ko Allah ya shirya min kai ...tare da kai hannuta kai kan tilon dan nata ta shafa tautausar sumar kansa tana jin wani irin sanyi a ranta .Muryata A dake takira sunansa ' deeni.....
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba ...
"maganar mai aiki da mukayi dakai za'a kawo ,to orready ma she's here.. ta iso sauran muji meyye ra:ayinka nidai na amince daita hundred percent ..kasa kasa yayi da muryasa wanda daman can haka yanayin maganarsa take ..
Kuma yadda yayi magana ummi ce kawai zata iya jin meyace ..tana ina .......?
abinda kunne nablah ya ji kennan.
gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune ...'ahankali ya juyo tare da kallon inda ummi tayi mishi nuni da hannuta. idanunshi ya runtse gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi " yace first lov... kice ta Mike naganta ..
tsoro da fargaba tare da frigice ne suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki" tashi daya taji jikinta yakama rawa gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma tunanin abinda ya kawota wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki ...
sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta da karanto duk addu'ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro " take taji wata natsuwa tazota mata aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .
'Ahankali ummi takira sunata nablah Mike tsaye man ya ganki , batare da wata gardama ba,ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace .Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma hannuwata suna sarkafe da juna tana cigaba da wasa dasu " yayinda ta cikin hijab dinta kuwa uhmmmm tashin hankali kennan 'dan kuwa jikinta sharkaf yake da gumi tsabar frigici datake ciki ,duk da tsanyi AC dake aiki a parlour hakan bai hana gumi tsassafowa ilahirin jikinta ba .
idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shr,n da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar kallon mutumin dataji an Kira da suna DEENI . take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya .......

KAMU SEDANG MEMBACA
AUREN SIRRI COMPLETE
Misteri / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan