53

11.5K 343 4
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO

Page 73

Duk yawan  ruwan da ummi ta dinga watsawa nablah bata farka ba asalima ko motsawa batayi ba .

hankalin ummi yakai kololuwa gurin tashi batasan lokacin data isa Inda nablah ke kwance ba ta rugumota  gabadaya ajikinta tana jijigata tare da kiran sunanta.
nablah.. nablah please nablah kitashi still shr km  bubu wata alamar numfashi a tare daita ummi ta tsorata da ganin halin da yarinyar mutane take ciki .
"agigice ta dauki wayarta tasoma neman layin DEENI kira daya ya dauka yana first lov..... ummi ta fashe da wani irin matsanancin kuka  sannan tace kai wato kana can kana lamarinka kabar yarinyar mutune 'cikin halin ha,ulai to wlh kazo Dan ubanka dan ka kashe yarinyar mutane sannan ta ajiye wayar batare da ma ta katse ba tacigaba da jijiga nablah tana kuka da kiran sunanta  .

Ba'a yi cikakken min shabiyar ba sai Ga deeni ya iso tare da  doctor din dake duba maikanta gidan Allah Yasa  bbu kowa a gidan Zeenat ta tafi makaranta yayinda safeena sun fita tare da laraba zuwa just right .

  a rikece  ya karasa shigowa dakin   idanushi kyam...  akan nablah dake kwance sa da zuciyarsa ta buga ya juyo da sauri   yana tmbyr ummi wani
halin take ciki .
ummi ta dubeshi tare da  watsa masa wata uwar  Harara  shi kansa  bazai iya cewa ga  irin rudani daya shiga ba sanda ,yashigo dakin  yaga  halin da yarinyar mutane take  ciki ba .

banda ambaton sunan Allah bbu abinda yake a kasa  zuciyarsa  ya kasa  cewa komai Sai nuni da yayiwa likita  data soma yin abinda yakawota.

domin  ji yake  Ina ma kasa ta tsage ta bude yashige ciki  ya huta da wannan abun kunya daya aikata.
hakika bakaramin aika aika ya aikatawa yarinyar ba.
gyaran muryar da doctor  din Tayi ne  ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya afka Na wuncin gadi .

Dan Allah kataima kai kamin ita xuwa  dakin kasa nasamu damar dubata inji cewar doctor .

deeni dake tsaye tamkar an dasashi  Sai lokacin ya dawo 'cikin natsuwarsa.
  Take suka sake  hada ido da ummi kallon kallo suke yiwa juna.
'Ahankali' yayi nodding kanshi kasa tsabar kunyar data rufeshi   da taimakon ummi doctor tasamu tasoma duba nablah .
still idanun ummi Na DEENI ta kafeshi  da idanunta tana mamakin abinda ...

doctor ta dago   Tana  duban  ummi tace gsky madam wannan abu yayi tsanani dayawa gashi Ni yanzu banida kayan aiki a hannuna km Na duba nan  bansamu abubuwa dazan mata amfani dashi ba.
amman Mafi sauki Ku tafi hospital mafi kusa daku .
deeni ya tsareta da idanushi   yana mata wani irin duba Na tabin hankalin kana  a hassale yace  ke wace irin stupid doctor ce dabata san kan  aikinta ba.
I think  doctors suna yawo da kayan aikinsu  ne shine ke zaki zowa mutane empty hands mtssss yaja tsaki ummi  nagama jin abinda doctor tace .
ta kira direbanta tana kokarin daukar nablah . cak deeni Yasa hannushi  ya dauki nablah cike da sauri ya nufi motarsa daita daidai lokacin da  ummi takarasa fito ta kira sunanshi deeni .... ya tsaya yana jiran jin abinda zatace.. kai min ita 'bayan
mota da hanzari yakaita byn motar ummi ya kwantar daita ummi tashiga da sauri deeni ya ma zagayo ya bude gidan gaba zai shiga .
a fusace ummi ta dakatar dashi  don't try to enter into this car becouse I don't want see you in it.
,a rude deeni  ya kyame tamkar Wanda akayiwa wanka da ruwan sanyi  yana  kallon ummi jin kalmar data fito daga bakinta tuni jikinsa ya kama rawa rawa ya sauke   Idanunshi kan fuskar nablah dake kwance tamkar wata  matacciya '.
cikin rawa murya yace ummi... ummi batare zamu tafi  ba   deeni ya fadi hakan 'cike da tashin hankali yayinda idanunshi suka gama canza kala tamkar garwashi  ...Kule
What are you wanting for   driver me to  bankole hospital inji cewar ummi deeni ya bude baki zai sake yin mgn kennan   Kule  ya figi motar  da gudu yana danna hon  da karfin gaske har securities din dake bakin get din  estate  suka Mike tsaye cirko cirko ..

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now