98

13.9K 377 3
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

     Dedicated to
Hauwa A Usman
       Jiddarh

Page  118

Zaman makoki akayi na tsawon kwanaki uku sannan kowa ya watse yakama gabansa, gidan ya saura daga shi sai ahlin gidan da yaran gidan .
sai  yan tsirarun mutanen dake zuwa gaisuwa daga wajen estate din.
duk yadda mutun yakai da Daurin rai da kafiya da rashin tausayi da imani idan yakalli yadda zeenat ta dawo acikin wannan Dan kankanin lokacin wallahil axim sai yayi mugu mugun tausaya mata.
,km sai ya xubda  mata hawayen tausayi .
,tayi wata irin muguwar rama daita sbd tashin hankali datake ciki.
  sosai tayi dakiya irin wacce ake so mutun yayi yayinda damuwa irin wannan tasameshi.domin
ta dakewa zuciyarta taki yarda tayi kuka a idanun mutane.
sai kukan zuci datake ta fama dashi wanda yafi ciwo da radadi km shine yayi mugun tasiri ajikinta har ya ramar daita.

Byn mutane sun watse kowa ya dauke kafarsa agidansu hatta ummi takoma gidanta ,gabadaya jikin zeenat a matukar sanyaye ta dan dosana a bakin gadon nata ta zauna hawayen da Suka dan Ziraro mata tashiga gogewa da hannunta wasu na sake zubowa wanda sai yanzu kukan rashin diyarta ke zuwa mata .
gabadaya yau tazo mata da abubuwa da yawa masu raunata zuciya.
babban jigon ginshikin da take dubawa wanda a iya tsawon rayuwarta bata taba  tsamman zuwansa ba km yazo mata yatafi .
Hakika taso kasancewa da diyarta su rayu da juna cikin kulawarta. gashi km tarasata acikin lokacin datafi bukatarta.
take ta tabbatarwa kanta da hkn ma nufin  Allah ne ubangiji talikai km ta gode bisa  hukuncinsa gareta, abinda  take nema shekara da shekaru tasamu km tarasa tausayin kanta ya mamaye zuciyarta batasan yaushe ne xuciyarta zata samu yanci da salamar rayuwa ba.
, abinda ya faru ashekarun baya lokaci daya ya sake bijiro mata ya mamaye ilahirin zuciyarta tunaninta.
  ta kauce hanyar Allah da manzonsa km ta gyara kuskurenta na shekarun baya dasuka gabata..
ummi ta fado mata arai Allah sarki umminah tasoma zance Zuci uwata jigon rayuwata kiyi hakuri da hukuncin ubangiji garemu ummi .
hk Allah yaso xeenat dinki takasance kin soni kin nunamin gatan da bakowa yake samun irinsa ba.
kin rike zumuncin Allah ,har wani lokacin ina tmbyr kaina da kaina shin wani irin soyayya surukarta km umminah take Min?
Take ta mike tsaye jikinta babu kwari tasoma zagaye bedroom din nata ,tana tunani tilon diyarta data rasa cikin wannan lokacin.
  diyar data daurawa son duniya kasancewar itace duniyarta ....
sosai ta dauki lokaci tsaye tana kai kawo acikin dakin tana yiwa yarinyarta addua.
Kafin daga baya takarasa inda Jakunkunan kayanta wanda ummi tayo mata cike da kayan babys da hotunan yarinyar wanda suka dauka ranar suna.
Ta tsurawa hoton Amna ido tana kallon kyakkyawar yarinyarta wasu sabbin hawayen masu zafi da radadi Suka shiga silalowa bisa kuncinta nasoki tun sanda nasan da zamanki kwance cikin Marata ..
nasoki tun bansa wace iri bace ke acikin cikina ...
har zuwa sanda kika zo Duniya ina daura kwayar idanuna bisa kanki naji duk Duniya kece rayuwata..kece farincikina.. nasoki fiyye da komai da kowa dake cikin duniyar nan .... Amman Allah yafini sonki amna nah hawayenta ya jike hoton yarinyar dake kwance lullube cikin wani tsadadden showel fara ce tas tas daita kmr uwarta da ubanta .
kuka take sosai tana sambatun rasa tilon diyarta datayi .
ahankali ta zauna tana cigaba da Kallon pics din daya byn daya kana ta ajiye hoton yarinyar bisa cinyarta tasoma bude kayan yarinyar daya byn daya tana kallo tana kuka me wuyar misaltawa bataji shigowarsa ba sai kamshi turarensa taji ya ziyarci hancinta.
ya dagare daga can nesa jikin kofa rungume da hannuwasa duka bisa kirjinsa yana kallonta sama da kasa cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
nan wata kwallar ta sake cikowa idanunta jikinta  na Bari ta hau sharewa lokaci daya wani matsanancin tausayinta da km sanyi rahmar so da kulawa datake masa Suka bugi zuciyarsa lallai ya tabbatawar kanshi yana matsanancin sonta raba zuciyarsa daita Abu ne ME dan Karen wahala domin kowani bangare yana dafin soyayya ta meida kanta kasa yakaraso ahankali ya  dafe da kafadarta da hannushi daya yana kallonta .
ta sake dago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zubesu cikin nasa wasu ruwan na  sake zubowa ahankali tana sharar kwalla lokaci daya zuciyarta na dawi mata da abubuwa da dama dacewar dasukayi da juna a soyayya da irin rayuwar jin dadin da suka Yi agidan aurensu kowa ya yarda shi farincikin dan'uwansa ne sanadin ta barbarewar rayuwarta zubda cikinta na  biyu hakika shine silar nesanta zukatansu  da juna da Jefa zuciyoyinsu  cikin kunci da angadarwa da wani shashin bakinciki gashi har yau bata daina girban abinda ta shuka ba .Tana wannan tunanin cikin hawaye shi km yake kare mata kallo cikin nashi suyar rai  .Da bai wuce na irin son dayake mata da km rasa diyarsa da yayi .
ya tsuguna kasa ya zauna gabanta yana rike da kafadarta yana kallonta.
hawaye tagani suna tsiyayowa daga ckin idanunshi batayi mamaki ganin hk ba domin tunda akayi rasuwar yake kuka wanda ta dauka na tsantsar tausayinta ne. sosai take hango tashin hankalinsa a tun rasuwar amna.
Tasan deeni na da matsanancin son ya'ya Amman bata dauka zai iya zubda hawayensa akan mutuwar karamar yarinya kmr amna ba. tashiga girgiza masa kai alamun ya daina kukan alhalin itama kukan take har da majina.
ta kai  hannuta tazata goge masa hawayen.
ya girgiza mata kai yana daukar hoton yarinyarsa yana kallo cike da matsanancin kaunarta.
wani irin kuka ne ya sake kufce masa domin tunda aka haifi yarinyar km ya daura idanunsa akanta yaji wata irin mugu kaunarta fiyye da komai da kowa dake cikin duniyarsa bai taba jin abinda yadaga masa hankali ya dakushe tunaninsa kmr rasa yarinyar da yayi ba
Yanasonta gashi  yarasata ciki kankani lokaci .
kuka suke sosai aka rasa wanda zai rarrashi wani cikin shi daita ..
ajiye hoton yayi yakamo hannuwan zeenat duka cikin nasa yanason ce mata wani abu Amman ya kasa mgn sbd kukan dayake, muryarta cike da matsanancin kuka tace ka daina kuka har yanzu abinda na shuka nike girba da hannuna na cancanci fiyye da hk daga mahaliccina.
ka daina tayani kukan zunubina yaya .
narasa komai nah . Da Fari narasa mahaifiya narasa dan'uwana wanda yayi sanadin rasa uwar danayi, nazo narasaka daga karshe narasa tilon diyata rasawa ta har abada takarasa fadar hk tana zubda wasu hawayen tausayin kanta ..
uhm zeenat kin rasa duk wayan abubuwan Amman kisani wallahilazim baki rasani ba..  Zeenat baki rasa nasuruddeeni ba sbd ina sonki   koma nace fiyye da wanda kike min.
baki cancanci kiyayya daga gareni ba  kuskurenki na baya ya Hana  Wannan son tasiri Amman wlh ina sonki duk da can baya Kin nemi hkn daga gareni kin rasa.
Amman wallahil aximi ina sonki zeenat.
da bana sonki da tun lokacin da kika nemi Saki daga gareni  wallahi da tuni an wuce gurin..

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now