3

15.8K 538 4
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


Aysha A bagudo

Page 5-6

Zeenat na da kyau  sai dai ba can ba" fara ce Sol Amman batada dagon hanci wannan bai sa fuskarta muni ba" haka idanunta matsakaita ne ita mutun ce mai tsananin son kwalliya wanda ko alwala Tayi sai ta sake yin  wata sabuwar kwalliya, haka  nan ummi bata gajiya da siya mata kayan kwalliya iri iri  sannan bata ganin aibunta a duk lokacin da zata bata a gurin yin kwalliyar .
abinda kawai bata so kuma bata yarda dashi ba, shine a yimata dinkin da zai bayyana surar jikinta ,nan nefa tace bazata bada goyon baya gurin  bata kamasho yada zina ba , dan a cewarta shigar da yawancin ena'mata keyi a wannan zamani itace ke sake haifar da fashadi a doron kasa.
  zeenat akwaita  da saurin sabo da mutane sannan km tana da son kawaye ita da Maryam dan ko yanzu suka san mutun   ko km kuka  hadu dasu sanadin wata kawar, Shikenan sun zama kawaye  , shiyasa suka fi dukkan sauran en'uwansu   jama'a dan daga  waje ma zuwa ake gurinsu  sabanin sauran" kullum kaga ana rikinci a bakin get da sune , gurin shigo da baki   most especially ma na school dinsu. abinda ummi tafi tsana kennan daga gareta yawan tara kawaye gata da matukar son gayu ,da son kallace kallacen film muddin tana gida kuwa bata da aikin yi sai na kallo ,daga wannan Chennal zuwa wata ,sai dai duk da wannan halin nata Allah yabata illimi sosai both arabic & school.

Daidai misali   Allah yayi mata farin jinin samari masu sonta daga waje ma biyota akeyi, sai dai bata fita dan ma ummi taki yarda tafara zance da wuri sai data kai ss2 kuma duk masu zuwa gurinta da aure suke sonta "amman matsalar dai daya ce family dinsu basa yarda da macce Tayi  auren  wajen Amman sukan bar namiji.
  kana duk masu son nata bataji son su har cikin  ranta 'har wani lokacin ummi kesata gaba da fada "tace maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kirasa kowa kizo kina nema yawan yi mata fadan da ummi keyi ne yasa ta tsaida kamil dan gwaggonta"  yayar mahaifinta  da suke uwa guda uba guda .
  shima bakowa yasan suna tare dashi ba , dan bata gama tantancewa aurensa ba" kuma shi bai fiyye  zama a garin  ba  yana aiki ne a abuja  ". haka kawai taji idan bata samu  wanda yafi ba  , zata iya aurensa dan shima ba laifi .

Jiki da jini wata safiya  ummi ta tashi da ciwon ciki , wasa wasa  tun tana daurewa har abun yafi karfinta gabadaya tafita haiyacinta'  hankalin zeenat yayi mugun tashi dan bazata manta yawan labarin da ummi ke yawan bata na mahaifiyarta  da irin wahalar da batasha  kafin mutuwarta ,ciki har da  cewa mata Tayi ta bude ido ta zabi miji wanda zai san mutuncinta kar taje gurin ruwan idonta ta kwashi gaibu ,shiyasa take massefar jin tsoron haihuwa da mutuwa dan ta kudircewa ranta, ta amince da mutuwa tunda tasan muddin kwanakinta suka Kare Shikenan "amman ita kam bazata yarda da haihuwa ba ganinta garata tasha wahala daya .
wunin ranar da ciwo ummi ta wuni can kuma tasamu sauki    dare nayi ciwo ya sake dawo zeenat taso zuwa ta sanar da DEENi Amman ummi taki .
washegari DEENi yashigo da shirin fita aiki  dan bai san bata da lafiya ba koda yashigo dakin yayi matukar girgiza da ganinta kwance cikin bargo da kyar take iya magana a rude yakaraso inda take  ya  tambayar ba lafiya ne ? Ummi tace eh tun jiya  yace meyasa  baki sa an tashe ni ba ,ya kalli inda zeenat ke rukube kusa da ummi duk tazama wata  kalar tausayi.
ke....Wace irin" sakariyace da baza ki iya zuwa kisanar min ba da kyar ummi ta iya bude baki ,tace ni na hanata  ya furzar da huci ta bakinsa hade da cire hular kansa yayi wurgi dashi gefe ,take ya Ciro waya cikin aljihun bayan wandonsa yakira family doctor dinsu wanda side dinsu kawai yake dubawa.
mintina kadan sai gashi likinta dayake bai da Nisa dasu cikin sauri yashiga duba ummi sosai har drip aka sawa ummi a ranar DEENi kasa fita yayi koina byn likinta ya wuce ne, ya kirasu ya Mahmoud ya sanar masu da ummi fa ba lfy , idanunta ta zuba mashi tana kallon bakinsa yadda yake maganar ne  tamkar wata mace shi yafi daukar hankalinta,
ba taba jin DEENi ya birgeta  ba irin na yau.
duk wunin  ranar  kusan shi yayiwa ummi komai  hatta magani da abinci a baki yabata sai gurin la'asar su Yaya Mahmood sukazo tare da matansu    sai zuwansu ne ma yasa mutane cikin estate din suka sani   dan DEENi bai sanar da kowa ba, shi dai ta mahaifiyarsa kawai yake.
Ai kafin kace me tuni side din ummi yacika da jama'a, haka  suka dinga shigowa duba ummi har dare DEENi na tare da ummi yana bata kulawa. duk yayi wani iri cikin lokaci kadan yafita haiyacinsa zeenat na zaune a gefe guda tana jiyo hirarsu rokonsa ummi take akan yayi aure ahankali takira sunansa NASURULDEEN ....abinda  yasake tada ma DEENi hankali kennan yaushe rabon dayaji ummi  takira complete name dinsa , tacigaba ban rasa  komai  na rayuwar duniya ba inada tarin dukiya da kadaroro  wanda ni kaina basan iyakarsu ba ,burina da muradina ahalin  yanzu bai wuce inga aurenka ba,  Amman na fuskanci kafi son sai na mutu sannan zakayi aure . Jikin DEENi ya dauki rawa hankalinsa ya sake tashi matuka ta sake kiransa cikin tattausar  muryar hade da rarrashi DEENi banida kowa daga kai sai zeenat sai kuma dan uwana wanda yake wata uwa duniya ,idan bakayi aure ka taramin jikoki masu albarka ba mezakayi min naji dadi , ina ji ajikina sai na mutu zakayi aure a rude yace first lov ki daina cewa haka  zanyi inshallahu kina raye Tayi murmushin karfin hali tace kullun haka kake cewa, ni tuni na fidda raina ka tashi katafi Allah ya maka albarka ... Amman yarinyar nan zeenat na rokeka dan Allah ko ban tashi ba kada kabari ta koma hannun mahaifinta, na damka  amanarta a hannunka ,bata da kowa duk duniyar nan daga ni sai kai ,karikemin ita a hannunka har zuwa lokacin da zata samu miji . DEENi yakamo tafin hannun ummi cikin nasa ahankali yasoma magana muryasa cike da rauni da fargaba, yace haba  first lov ki daina maganar mutuwa nan kece zaki aurar daita  da hannuki kuma kina raye inshallahu ta girgiza kai ita kadai tasan abinda take ji cikin muryarta irinta marasa lfy tace Shikenan tashi kaje ka kwanta , hankalinsa a tashe ya fice daga dakin..
zeenat ta mike daga inda take idanunta na zubda hawaye  ta taimaka mata suka kwanta tana kuka kasa kasa ummi tace lfy zeenat  ummi . .... ummi..... cikin sheshekar kuka tace banason naji kina cewa zaki mutu kibarni dan Allah ,ummi   tace nafa da kar na fada mutuwa ta zamemin dole  sai dai idan ajalina bai zo ba . zeenat ta saki kuka hade da  kamkameta ummi a jikinta , tacigaba  da  kuka mai cin rai hade  da cewa ummi bazaki mutu ba inshallahu da kanki zaki aurar dani ni ga duk wanda kike so  da kyar bacci ya dauketa yayinda ummi Tayi nisa a bacci .

Shi kuwa DEENi tunda ya koma dakinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye  sai zariya yake daga farkon dakin zuwa karshe kafin daga baya ya nemi gurin ya zauna.
  yayi tagumi da duka hannuwansa yayi zurfi cikin tunanin yadda zai yi lallai ya zama dole ya nemo mata  domin cikawa umminsa burinta. sai dai shi matsalar sa bai san ta ina zai fara ba ? Bai taba yin buduwar ba ballanantana wata aba soyayya,  shi duk a tunaninsa raini hakan zai jawo masa idan  yaje yace yana son budurwar .
ya kamo gefen lips dinsa ya dan cizawa a hankali har daga karshe ya yanke shawara zai nemi fk da zance anan ya sulale ya kwanta rigingine idanunsa na kallon celling  dakin .
yayinda ya rungume hannushi a saman kirjinsa  yana aiyana irin type din maccen dayake son  ta mallakesa,kuma  wacce ya dace ya aura cikin sanyi ya runtse idanunsa gam  take yasoma zaiyano irin type dinsa kyakkyawa dogowa mai dirin jiki , choculate colour, mai dara daran idanu sannan educated mai wushiryar haka dai ya rinka yi har dare ya sula  bai samu wani  ishashen bacci ba. koda asuba kafin ya tafi masallaci sai  da ya fara shiga Bedroom din ummi ya sameta tana sallah ya sauke ajiyar zuciya sannan ya wuce ganinta tsaye tana sallah yasan Allah yakawo mata sauki .

A masallaci DEENi suka hadu da fk byn an idar da sallah "yajashi gefe guda da idanu fk yake binsa da kallo "abinda bai taba faruwa ba saboda DEENi  daya idar da sallah yayi yan addu'oinsa yake wuce wa  gida .
  fk ya dube sa da kyau yana nazarinsa  kafin daga baya yace lfy kuwa  naganka haka ? Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayarsa sannan DEENi yace ina fa lfy jiya  ummi kwana Tayi  ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba.
fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace baita kadai ba har big dady ma burinsa kennan  dan ko jiya sai daya min maganar nida kai  Amman tunda kai ummi ta damu  ta tsananta gara kayi  kawai kurabu lfy .
DEENi yace ai bakasan inda zan nemi matar ba nifa gabadaya en,mata family din nan basu min ba  sannan kuma sun min kankanta da aure  ,fk yace A'a bawani kankanta" mace na kankanta  da aure ne ?  kaine dai kawai  kake ganin haka ,ni   yanzu na yanke  shawarar  zan tsaida shemah kawai  tunda na dade ina sonta nida zakaji shawarata ma  da  zeenat ka aura  DEENi ya mishi wani irin kallon bakada hankali sannan yaja tsaki yace haba dai  zeenat , fk yacigaba yarinyar akwai hankali wlh ,ba kmr  wancan banzar ubannata ba, dayake duk sun tsani  halinsa.
    kaga kawai sai a hada bikinka  da nawa kawai  kaga zeenat batada matsalar, km ko bakomai ummi zata ji dadin Sosai da wannan hadin.
DEENi yace Amma ban taba jin koda alamar digon sonta ba, kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha tara  zuwa sha ashirin ne  fa. nafison mutual girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani akan bed ,amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ,ni ne zan koma renonta.
fk ya dubesa a kaikaice yace lallai yaran zamanin da   kasani Amman banda na yanzu, sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba,  kana rai nata ne kawai , sai kaga mararta ta daukeka tsab, DEENi yaja tsarki kai ban son iskanci shawara nake so, ba wani shirme ka  can na bazan    ba .
fk ya kada kafada yace well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari .
DEENi ya kalleshi  yana watsamasa harara "kaifa dan iskane dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali " sai kuma yayi kasa kasa da murya  yace kasan Allah ni fa ko a waje ba wai ina kallon mata bane, fk yace to katsaya akan zeenat din kawai, duk inda ake neman macce mai natsuwa yarinyar nan takai ,DEENi ya sake jan tsaki yace ai inda takaicin yake kennan sai kuma nakirata ince ina sonta ...ya fada yana tabe baki "hade  jin takaici da  haushin shawarar da fk yakawo masa " fk yace inda bazaka iya ba kabi ta sama , ma'ana kasamu big dady da maganar kawai, kasanar dashi kana sonta  nasan zai ji dadi Sosai .
DEENi  ya sake watsamasa wata harara yace dan Allah malam ka dameni , ina ganin fa kmr kafara samun tabin hankali , wa yace dakai   ina sonta "zan dai yi aure badan ina so ba ,ya juya yabar fk nan  tsaye   yana binsa da kallon mamaki sannan kuma yace ai kaine babban  mahaukacin   dan iskan kawai , sai iskanci fall ciki ,shi bai ga laifinsa da yace bazata ya saukarsa a bed sai nawa sai kuma ya kwashe da dariya .

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now