91

15.8K 430 36
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

🌈kainuwa writers association 

(united we stand and succed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)

   Dedicated to
Hauwa A usman
      Jiddarh

Page 111

Lokacin dasu nablah da yan'uwanta suka isa gidan ummi .
"cike da murna da farinciki ummi ta tarbesu da faram Faram bata nuna musu wata alamar komai ba.
ta karbesu cikin aminci da mutuntaka tare da  umartan  laraba ta kawo musu kayan motsa baki first. Tunda laraba taga nablah da yan'uwanta take murna da jin dadin sake ganinta sbd tasan Komai daya daita da matsayinta agidan.
Cikin mintina kalilina akacika musu gabansu  da kayan motsa baki iri iri wanda wani abun ma kwata kwata basu taba cin Karo da irinshi ba arayuwarsu .
kafin daga baya aka sake kawo musu abincin da abin sha  shima aka cika gabansu da kayan abinci kusan kala uku kasancewar ummi tashiryawa  zuwansu that's why akayi komai cikin girma da girmamawa.
wanda daman kusan halin ummi Kennan akwaita da karrama bako kowani iri ne koda kuwa banata bane .

Sosai suka zage suka ci abincin Amman ban da nablah  wacce Sam kunyar ummi ta hanata sakewa ballantana ta saki jiki taci.
Har sai da ummi ta lura da hkn tace tasaki jikinta taci abinci kmr wata bakuwa sannan fa nabla ta Dan soma tsakura. haidar da anan da sarkin naci junior duk suna parlour 'n wanda wannan Karon kwata kwata basu wani mannewa nablah ba .
suna jikin ummi sbd yanzu Sun saba sosai da da kowa gidan ummi da zeenat har laraba ma Suna yarda daita.
HakanKuwa ya taba xuciyar nablah ganin yaranta basu damu daita ba sai harkokinsu suke suna yan tsalle tsallensu acikin parlour'n.
Yayinda  uwar gayya zeenat tana daki kwance duk  da tasan wainar da'ake toyawa akasa Amman bata sauko ba domin tasan  bai wuce dawowar nablah bane  kmr yadda deeni ya sheda mata shekaran jiya .
Tana daki anabata kulawar data dace.
kwarai taso zuwa sugaisa da yan'uwan nablah sai dai Bata samu damar fitowa ba sbd gyaran jikin da'ake mata alokacin Amman haniyar da'ake acikin gidan yana dan zuwa kunneta Kadan kadan.

ganin yadda yaran suka zuwa inda nablah take km suka ki yarda da kowa acikin jama'ar da suka zo yasa ummi ta turasu tana nuna musu nablah oya kuje gurin momy ku gaisa tare da turasu junior yasoma zuwa sannan sauran yanuwansa suka bishi ahankali km suka shigemata suna dan surutunsu na yara da kyar da dabara suka yarda aka daukesu shima sai da nuratu ta fidda sweet ajakarta ta mika musu.

Karfe hudu daidai byn yan'uwan nablah sunyi sallar la'asar suka soma shirin tafiya.
suka tambayi zeenat ganin tunda suka zo gidan basu ji duriyarta ba.
bakuma su san takaimaimai inda muhallin yake ba, domin suna son su damka amanar nablah a hannuta.
ummi tace ayya gashi  Ko tana nan sai dai bata jin dadi . Kwarai suka so zuwa ganin jikin zeenat amman ummi takiyarda da hkn ta dinga kame kame sbd batason suga halin datake ciki.
haka dai suka Hakura
sukayi mata adduar samu sauki suka damka amanar nablah hannu ummi .

sosai suka kara yiwa nablah fada akan hakuri da juriya arayuwar aure.
da girmama na gaba daita .
ummi tayi musu shatara ta arziki da Yi musu kyauta  ban girma wanda ke tsayawa azuciya mutun domin kowanne ackinsu sai data bata turmin atamfar super exclusive da turaruka design masu mugun kamshi cikin wanda aka zo mata dasu daga india hk sukayita murna suna godiya suka wuce .

Jikin Nablah a matukar sanyaye ta tmbyi ummi inda aunty zeenat take  tace tana dakin sama.
tare da baba balkisu suka nufi har dakin  dubota .
Tun hawowarsu step din taji faduwar gabanta ta tsannanta bakinsu dauke da sallama sukashiga dakin .
hango zeenat sukayi rigingine da jikin gadon dakin hannuta rike da cup tana shan kayan hadin gyaran da'ake mata tana yatsina fuska sbd rashin jin dadinsa datake ji abakinta.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now