67

12.7K 340 2
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO


Page 87

Hannuwanshi duka ta damko  'cikin nata  sosai ' tana sakin wani sabon kuka me cin rai tare da cewa idan kuwa kayi min hk deeni bansan irin farinciki da zanyi ba arayuwata  ,jikinta har rawa yake gurin fadar hk tacigaba mgn rabuwa da wannan 'cikin shine muradina a halin yanzu. Ni kaina wlh sai yanzu Na tabbatar da 'cikin jikina km duk hanyar da zanbi gurin salwantar dashi wlh zanbi tashiga jijiga hannushi dake 'cikin nashi Tana wani irin kuka me cike daban tausayi .

Jin abinda tace yasa gabadaya  gumi yasoma tsatsafowa ajikinshi takoina  tsabar tashin hankali da tsinci kanshi ciki .
,  dan ko numfashi ma da kyar ya dinga fitarwa ahankali ahankali yana kallon  'cikin idanunta abinda ya dade  shekara da shekaru yana nema shine yanzu Allah Ya amsa addu'ar sa yabashi ake kokarin  , za'a zubar ......
  .da kyar yasamu ya tattaro dan abinda yake son ce mata .

Karki damu tunda har  nace zan taimaka miki zanyi ne . sai dai mu bari muga zuwan doctor .. Nagode.. Nagode.. Nagode..deeni  bazan taba manta taimakonka gareni ba  ,ta sake fashewa da wani matsanancin kukan ..

Cike da sanyin jiki da tausayin kanshi ya Zare hannuwanshi dake  'cikin nata ya Ciro daya Daga 'cikin  wayoyinsa   ya turawa doctor saira sakon  test ..kana ya janyota jikinshi ya rungumeta tsam  yana shafa bayanta kusan minti biyu suka dauka ahaka sannan ya dagota cike da kulawa da tausayawa ya tsura mata rikitattun idanunshi is Ok kukan ya isa hk kinji.
  " ta daga masa kanta kawai tare da cigaba da kukanta domin ita kadai tasan  irin radadin da zuciyata  ke ji a game da 'cikin jikinta .
,ranshi a matukar bace yacigaba da kallon yadda take wani irin kuka Wanda yasan hkn zai iya shafar lafiyarta da dan dake  cikinta .
  "dan hk ya furzar da wani iska me gauraye da huci kana yace haba..meyasa kika fiyye fitina  da wahala ne?

Nace miki  kiyi shr hk zan San abin yi ko so kike nazare hannun 'cikin lamarin 'cikin jikinki ?

Tayi saurin girgirza masa kai.
Ok ki bar kukan nan hk bana son jin sautinsa kwata kwata .
,nan ta sake girgirza masa kai alamun taji .

Kina jin yunwa ?

Tana jin yunwar Amman ta girgirza masa kai alamun bata ji .

Byn kmr minti goma shabiyar  sai Ga doctor saira tashigo  office din hannuta rike da wasu  file files tana yiwa nablah sannu da jiki .

, nablah ta daga shanyayyun idanunta Tana dubanta tare daga  mata kanta alamun da sauki kana ta zarce zuwa mazauninta Tana jiran isowarsu

DEENI bai tsaya jiran saukowar nablah  ba. Ya sanya mata hijab dinta  ya nade hannun suit dinsa ya dauke cak.. ya rungumeta ajikinshi yana kallon 'cikin  kwayar idanunta  ji yayi tamkar ya tsotsi pinky lips dinta da suka sake yin ja .
, ahankali yakarasa Inda doctor take zaune  ya zaunar Daita kan kujera yana sake gyara mata zaman hijab din  kanta sannan shima ya zauna..

Yana maida hankalinsa sosai kan doctor saira .sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ya soma dacewa doctor wani taimako nake son kiyi min akan cikin jikin yarinyar nan dan Allah  idan har zai yiwu Ina son a cire mata 'cikin jikinta ....

Doctor saira tayi shr Tana sauraronsa har  sanda  ya dasa ayar mgnrsa , sannan tace gsky mu  hospital din nan bama abortion domin doka ce me karfi idan aka kama mutun da laifin aikata hakan.
nablah najin hk  ta zamo kasa da sauri Tana marairaice fuska da murya ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka soma ambaliya suna tureneniyya gurin fitowa  ta hade hannuwanta duka  guri daya tasoma rokon doctor

,dan girman Allah doctor ki taima min ki cire min 'cikin jikina, dan girman mahammadu rasulillahi s.a.w  ki agazawa rayuwata ki rabani dashi , idan ba hk ba wlh mahaifina zai kashe Ni takarasa fadar hk Tana sakin wani irin kuka me sotsa rai gefe daya km  jikinta ya sake daukar kirrrrrrma tasoma rarrafowa Inda doctor ke Zaune.
A dan hassale DEENI yace wai meyye hk kike yi ?
bakiga magana Mukeyi  daita ba ta yadda za'a rabaki da 'cikin jikinki ba. wlh idan kikasa wasa sai kin haifi 'cikin jikinki da izinin Allah.
ta juyo da sauri ta rarrafo zuwa gurinsa ,tana kuka dan girman Allah kada kamin hk  DEENI.... karigada kayi Niyya taimaka min dan girman Allah kada kafasa ..

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now