64

11.9K 353 1
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

*Where are you murja come close this page is for you only i'm so existed for ur care, thank you so much ,Allah yabar kaunar dake tsakaninmu mara algus ,kin nuna min  karamci da aikin girma, bagudo taga karamcinki   km ta yaba Allah yakara arziki ,ke din ,daban kike  acikin mutane, bakowane mutun ne tamkar ki ba, you are so special*🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻


Page 84

Da sallama abakinsa  yashiga office din yayinda nablah ke biye dashi abaya tamkar wata sabuwar halitta ta daban sannan ta maida kofar office din ta rufe takarasa shigowa ciki sosai .
zaune suka iske doctor saira sanye cikin kayan aikinta Na cikakkiyar doctor idanunta manne da farin medical glass ..tana ganinsa ta fadada fuskarta da murmushi Tare da Dan   Mikewa  tsaye kadan  tana gaidashi tana mai  nuna masa gurin zama da hannuta.

,ya zauna yana may   amsa gaisuwarta fuskarshi ba yabo ba fallasa .
sannan tayiwa nablah dake rakube a gefe tsaye nuni da kujerar zama  .

Nablah ta zauna '  a daddare 'cike da  natsuwa tana karewa office din kallo sbd yau shine karo Na farko data ,taba shigowa irin wannan hospital din na masu hannu da shuni ,kai har ma  da  office din gabadaya.
Hk   kawai ta tsinci kanta da jin wata irin mummunar faduwar  gaba.

batare da wani bata lokaci ba deeni yashiga yiwa doctor saira   bayanin abinda ya ke tafe dashi ,akan so yake ta duba masa   lfyr yarinyar dayazo daita .

Doctor tayi murmushi  tana kallon shashin da nablah ke zaune kanta a sunkuye  tana wasa da yatsun hannuta tasoma tmbyrta abinda ke damunta 'cikin harshen turanci.

nablah tayi tsuru tsuru da idanu takasa cewa komai sai da doctor saira ta sake maimaita tmbyrta" sannan muryarta a sanyaye tace bbu abinda ke damuna fa . Km ni fa lfy lau nake babu inda kemin ciwo  .

Deeni ya juyo ahankali yana kallon Dan  karamin bakinta da take tsukeshi a duk sanda zatayi  mgn

A Dan fusace Yace ke banson iskanci ki sanar mata da abinda yake saki zafin jiki bawai ki tsaya kina wani  batawa mutane lokaci ba ..

A dake itama tace to bbu abinda yake damuna sai km  nayi karyar ciwo .

Yaja tsaki yana cizan gefen lip's dinshi    kana yacigaba da mgn.
" doctor karki sake tmbyrta" ke dai ki duba min lfyrta kawai .

Doctor saira tayi murmushi duk da batasan matsayin yarinyar gareshi ba ,Amman sai taga sunyi matukar dacewa da junansu .
tace Ok sir  ,amman mr DEENI baza'a yi hk ba ,ciwon nan  ajikinta yake yakama mu Dan daji wani abu Daga bakinta first  so that za'a San ta inda za'a soma duba lamarin .

DEENI yayi shr tare da dauke kanshi bai sake tsuma musu baki  ba sai ma  phone dinsa daya Ciro  yasoma operating.

ita km doctor saira ta sake maida hankalinta sosai a kan nablah .

yauwa  kanwata Ina jinki  yi kokari ki sanar min da abinda ke damunki da kyar dai doctor saira tasamu nablah tace mata  wani abu .
A gsky Ni bana jin ciwon komai ajikina ,sai dai sometimes hk  nakan ji  motsin wani abu acikina... 'cikin wani irin yanayi na shock DEENI ya dago rikitattun idanunshi ya zuba mata yana kallonta ,ta Dan tsuke bakinta ganin yadda yake kallonta sannan  tashareshi  tamkar batasan ita yake kallo ba, tacigaba da mgn da muryarta a shagwabe.
Amman Ni doctor Allah  Ina ganin kmr appendix  ke damuna.
ba doctor saira ba hatta deeni sai da mgnrta, ta kusan sashi dariya .
Aiko yayi saurin juyar da kanshi gefe yana fitar da sanyayyir murmushi .
hk kawai  ya tsinci kanshi 'cikin wani irin farincikin Na daban km mara misaltuwa .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now