86

15.8K 450 21
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

    Dedicated to
Hauwa A Usman
       jiddarh


Kainuwa writers association
(united  we stand and suceed our ambition is to entertain & motovite the mind of readers)

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

Page 106

Byn kowa ya watse. parloun'n ya dauki shr na tsawon wani lokaci big dady ya dinga kallon deeni yana mamakin reaction dinsa na dazu daya dinga Yi akan yarinyar.
"ahankali Big dady ya cigaba da kallonsa tmkr wani sabon Halitta agabansa.
sakamakon  yadda cikin kankanin lokaci gabadaya kamaninsa suka sauya ya dawo wani irin mutun Abin tausayi.
Ahankali big dady yake  kalleshi tare da nazarinsa Kana ya numfasa muryarsa a matukar raunane irin ta Manya ya kira sunan shi..... deeni ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala tsabar rudani da tashin hankalin da yake ciki .
ya zubawa big dady su yana kallonsa batare da yace uffan ba.
" sai ma hadiye abinda ya tsaya masa amakoshi yayi yana maida hankalinsa sosai gurin sauraron abinda  big dady zai ce .

Big dady ya sake fuskantarshi da kyau sannan yace nasuruldeeni na fuskacin kana matsanancin son yarinyar nan nabeelah kana mata mahaukacin so fiyye da tunanin me tunani wannan kalubali ne agareka sannan km babban yakine akanka daka San yadda zaka shawo hankalin yarinyar nan cikin sauki.
sbd daganin yarinyar tana da kafiya da taurin Kai da taurin zuciya sai kayi mugu mugun aiki da km yaki sannan Zaka samu ka shawo kanta da hankalinta.
" musamma sbd abinda akayiwa yarinyar wanda kowace Mace akayiwa hk zata iya yin hauka fiyye danata .
na Lura sosai kafi son yarinyar  akan zeenat duba da yadda ka dinga yi wasu abubuwa agabanmu gabadaya idanunka sun Rufe deeni akanta.
so nidai abinda zance anan bai wuce nace kayiwa Allah kayi aldalci atsakaninsu deeni.

kayi adalci atsakanin matanka kada ka taba fifita daya akan daya karka sake kabari daya tagane kafin son daya akanta .
duk wacce Kake so axuciyarka kabarwa ranka yazama sirrin zuciyarka .
daman dole ne sai kasamu wacce zakaji kafi so atsakanin matanka .
Amman karkar kuskura ka bayyanawa kowace daga cikinsu.
kabarwa zuciyarka kayi adalci kaji tsoron Allah karike matanka amana dan karkaga nabeelah ce me haihuwa uwar ya'yanka kace zaka wulakanta zeenat sannan kada kaga zeenat yar'uwarka ce ka biyewa mahaifiyarka.
ku taru  ku wulakanta nabeelah..
sosai big dady ya dinga masa Nasiha me ratsa jiki da huda zuciya dasa zuciya nadamar abinda ta aikata. Sannan zance ita yarinyar nan nabeelah kabarta anan tukun kafi asan abin Yi. ya daga kanshi alamun yaji.
byn big dady yagama dashi yace idan ya fita ya turo masa zeenat. Jikinsa a matukar sanyaye ya mike tsaye da kyar yana yiwa big dady sallama hade da godiya...

Byn ya fito ya iske zeenat zaune a karamin parlour'n gidan ya zauna kusa Daita sosai yana jin wani irin matsanancin tausayinta yayinda sound din kukanta ke taba zuciyarsa.   "gabadaya nadamar abinda ya aikata agabanta yakeyi.
hakika bata cancanci hk daga gareshi ba kodan duba da yadda take  matukar kaunarshi fiyye da komai arayuwata . cikin sayin jiki ya kamo tafin hannuta cikin nashi yasoma murzawa ahankali ahankali kafin yace wani Abu.
Da sauri ta zame hannuta cikin nashi tare da juyar da kanta alamun bata son ganinsa .
yaja numfashi da karfi ya fetsar yana tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa.
sannan ya bude bakinsa da kyar ya kira sunanta complete Name dinta muzeenat, ..............
zeenat taki juyowa ta kalli inda yake ballanta yasa rai da samun amasart.
sai ma jijjiga kafar daya da take tana cizan lips dinta.
Miryarsa a raunane ya sake kiran sunanta My Zeenat am sorry.... am very  sorry  for  what I did...nasan ban kyauta miki ba .
sannan baki cancanci hk agurina  ba.
  " tabbas naso na kuntatawa rayuwarki alokacin da kikayita zubar min da cikina arariya ....Amman bata wannan hanyar ba.
Ko auren sirrin dana Yi da nablah ba'a son Raina nayi ba.
Umarnin first love nabi wanda alokacin gabadaya daurewar farincikinki take nema agidana .amman kiyi please ki yafemin bisa biyyewa first love danayi gurin boye miki..
duk wannan bayanani dayake mata bata juyo ta kalleshi ba har yagaji ya Mike da niyar wucewa  tare da Sanar mata da sakon Big dady.

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now