56

58 6 0
                                    

*🤍THE MAID(MAI AIKATAU)🤍*



       BY THE DMKs✍🏻






                *56*



Su Fahad suka hadu a meeting joint insu amma mota daya zasuyi using, Najib suka ga Yayi hanyar Nyanyan duk suna Kallon shi da mamaki, Ina Zamu kuma Najib?

Ku tsaya ku gani.. Najib Yayi packing daidai gidan su jamila yasa akayi Sallama da ita, tana fitowa Najib yace kishiga motan mutafi, ba musu tashiga sabida ya nuna mata 🆔 insa tana shiga aka fesa mata abu ta suma,ya hau hanyar bwari.. Bai tsaya koh Ina ba sai wani Tsohon gida.
Ya ajiyeta agidan kafin ya dauki hanyar apo...

Najib Wai Ina Zamu ne apo new site.  Anan suke Sabida sumata da tracker dake jikin Hazrat duk wayon su Basu ganshiba tanan ne nasamu dama samu location din dasuke.


****×****×****×****×***

jummai inaso in sa labarinki Kuma ke wacece , Mai hadin ki da mijina sanan ina baba Laure

hajiya Kiyi breakfast zan baki Labarin komai akai na sanan dalilin dayasa nazo gidanki

nakoshi Nide kawai Kibani amsoshin abinda na tambaye ki,

Toh Farko dai sunana Yusrah Jamilu moddibo also known as Yusrah MJ the CEO of moddibo.. Hamza wa nane sanan kuma baba Laure ba Abinda muka hada da ita kuma batasan komai ba amma kawu basiru yasan komai,

jummai yarsa tadade dazuwa AIKATAU Kuma Haryanzu basai koh tana Raye ba koh ta mutu sabida... Mukama yanda mukasan kawu basiru ta wajan mama dake mana Aiki ne, ita kanwace a gunshi. Tabamu Labarin cewa tunda ta tafi AIKATAU yarshi bata koma ba, Saide Suta tura mai kudi, yayi kuka ya gaji akan adawo mai da yarshi..

Damukayi bincike sai muka samu Labarin cewa yarsa tadade da rasuwa ta wajan yin abortion, Wanda mata ke ma Aiki basa kasa.... Sai Nayi disguising Kai na as ita, nakoma gari dazama a matsayin nayi accident nayi loosing memories ina, Kuma fuskata ta lalace,
Duk wanan Abun yafaru ne lokacinda aka auro Ki, Yayana na da tabbacin cewa zaki so yar Aikin Sabida Yanayi.. A Haka aka hadani da baba Laure kanwar maman jummai..

inko Allah, jummai har mutane nawa suke cikin game in ku?

Hajiya taimako kawu basiru mukayi kuma Kanwarsa ta ammince mana Sabida komai zamuyi saida shawarar ta, ta zame mana uwa tazame mana uba.

toh naji yanzu labarinki nake son ji kuma Mai yahada da mijina?

Hajiya sai kinyi min alkwarin cewa zaki yanke mai hukunci dadai da abinda Yayi min.

Hmmmmmmnm, in shaa Allah zan yi

       
      *Labarina yafara ne kamar haka:*
*Hajiya Nide tun da nazo duniya bansa mai nene son uwa ba, mahaifiyata Tana Hayhuwa Na Allah yayi mata rasuwa. Na taso a Hannu Kakata acan Ruma. Ina da shekara uku a duniya Allah yayi wa Kakata rasuwa,  Sai babana ya dauko ni da yaya Hamza zuwa Abuja a inda yake aiiki a matsayin mai gadin ma wani attajirin mutum Wato Alhj. Tafeeda tun ina yarinya nasaba da Aiki wahala cuz at my early age Nike wanke wanken Gidan sanan kuma yaya hamza shike Shara duk wagege Gidan. Saidai mutane gidan basu da wulaqanci suna son tallakawa rashin sa'a da mukaci shine gun Yaran su,*
*Sabida yara naji haushi yanda iyayensu ke mana, har yakai ga atare ake koyamana karatun adini dasu, Kuma gashi Nafisu sauran daukan karatu shiyasa suka kara tsanata, Ina da shekara takwas a duniya nayi saukar Al-Quran mai girma, kuma a primary school da Alhaj yasa mu ma sabida Yanayi kokari na nake samu double promotion, har ake kira na da "The gifted" dalilin haka yasa nariga Yaran Alhaj gama primary school, ina da Shekara takwas nazana jarabawa shiga jss 1 Matan Alhj sukace basu yarda ba sai dai in zauna a gida Injira saura yara su, koh in ba Haka ba sai dai ya daina biya min kudin makaranta, Alhj yakira babana ya sanar dashi halin da ake ciki, babana yace ba damuwa zai Sani ana government school kuma Haka ya faru, after three years of junior secondary school I was awarded the best student of the school ni nazo na daya a junior waec din shine nasamu Scholarship zuwa "Turkish Intentional school Abuja" Gashi babana baida wani karfin da zai siyamin uniform and other school materials, haka dai yayi squeezing har ya siyamin wasu Amma ba sandal din makaranta na junior nake using. Rana Dana Fara zuwa school din nasha zolaya da tsagwama wajajen student, sai nuna kafa na akeyi ana dariya, sanan kuma bani da jaka a hanu.. Aka Kira assembly Haka muka fito   assembly din wasu in su gani su Rufe hanci wasu Kuma Suta dariya, har aka nunamin class in da zan shiga, na shigo zan zauna a seat Ina, wani dake Bayana yaja kujeran na fadi kasa, duk suka kwashe da Dariya.. Bayan wani Dan lokaci chemistry teacher mu ya shigo. Yaune Farko da aka fara karatu, bayan mun gaishe shi.*

THE MAID(MAI AIKATAU)Where stories live. Discover now