61

64 6 0
                                    

*🤍THE MAID(MAI AIKATAU)🤍*



          BY THE DMKs✍🏻





                  *61*

Hussaina rabo, Marsisi, Rahama baby, Rukkaya Abdul and jiedderh and others wanan sadakarwa ne Gareku
Inajin dadin yadda kuke bada naku gudumuwa ta hanya karfafa min gwiwa.  ❤️❤️❤️





Inteesar ta yanke jiki ta fadi  itama akayi rushing Inta,zuwa daki aka fara bata treatment, daidai da lokacin shigowar su ummah... Suna tambaya ina ne dakin wa'inda aka kawo yanzun... Wata Mata da take tsaye agun tace mata da namiji koh?

Ummah Tace eh.

Mijin balarabe ne koh?

Ummah Tace eh eh su..

Allah sarki, sai dai kuyi hakuri Mijin Allah yayi mai rasuwa aman Ita matar tana can dakin. Ta nuna mata da Hannibal.. Matar naganin Mijin ya rasu ta yanke jiki ta fadi da Yaron a hannunta, inki ganta sai kin tausaya Mata, sai danayi kuka, matar sai zuba takeyi kamar wacca akasa ma battery

Ummah taga koh Ina Ya koma Fuji,
Innallillahi Wa Ina ilahi rajiun
Innallillahi Wa Ina ilahi rajiun

Abinda ummah ta dinga repeating har ta zauna akasa bata Sani ba, Abby koh suman tsaye Yayi sabida ya kasa magana kuma ya kasa motsi, amma yayi ta maza yafara lallashinta yace we need to see the doctor first, ummah Tana kuka tace kana jin Abinda matannan tace anan kawo shi Allah yayi mai rasuwa...duk da Haka Gara muji tabakin doctor, suna cikin Haka wani doctor ya fito daga hanyar emergency. Abby yayi sauri yaje gunshi

Ummah tayi kuka Tayi kuka,sai kuka takeyi...can wata Nurse Tazo da sauri mai yafaru kike kuka... Ummah takasa magana Nurse ta taimaka Mata ta tashi, ummah ta nuna mata dakin da zata Nurse ta rakata, Taga wata Nurse da Muwaffaq a hanunta  Ummah ta karbe Shi kawai sai ta fashe da kuka Sabida kamar Hazrat yana yaro... Komai nasu iri daya, tana Kallon shi tana hawaye....

Shikuma Abby yaje gun doctor, yace ma Abby ya bishi office akan maganar Hazrat.. Sai yanzu yasamu hawaye ya fito,

Doctor where is my son?

Plz ku Kai ni in gan Dana...

Doctor yace calm down plz. Zaka gan danka amma sai ka kwantar da hankali ka.

Amman mai yasa bakuyi gaggawa sanar da 112 ba?

Doctor it’s a long story... Ni kawai ka kai ni in gashi koh zan ji dadi...

I'm sorry to say Alhaji ba Zaka iya ganin shi yanzu ba....kamar ya? Ni ne mahaifinsa dole in gan da na.. Ka kai ni inda yake in bahaka zaka iya loosing job inka....

its not about loosing my job, just look at your self, you look unrest and tensed....so I want you to calm down first.

No doctor, gara in ganshi yanzu kafin sauran mutane su zo... Ina son in zama Na Farko Wanda zai mai Adu'a. Nidai kawai muje...

Alhaji zaka gan danka amma Ina son inyi ma explaining komai, amma tunda kace kana so kaganshi dankanka muje in Kai ka...doctor ya tashi Abby ya bi bayansa.

Ummah ta Kasa bin Abby Don ta kasa yarda da maganar, tana ji kamar a mafarki, Kuma batasan ya Zatayi in taga one and only son inta a macce ba, kawai she can't bear to see him dead, sai kuka takeyi tananan tana Adu'a Allah yasa Abinda taji ba Gaskiya bane, amma kuma yanda matar ta fada cewa yana ta Amai jini yasa ta yarda cewa baya Raye... Takara Kallon Muwaffaq Tace Shikenan kazama maraya, kana naka Allah na nashi Naso inga jikoki na da yawa amma Allah bai kadara ba, Oh Allah!  Allah kabani juriya da Hakuri...tana cikin Haka ne wata Nurse tace Kije ta farfado, ummah ta shiga bayi ta wanke fuskanta ta yanda Inteesar baza ta san Tayi kuka ba... Ummah na tafiya kamar Bazatayi ba har ta isa inda Inteesar Ke kwance.

THE MAID(MAI AIKATAU)Where stories live. Discover now