64

271 51 6
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 63*


*'''Freshly cooked for breakfast😉☕️'''*
"that's my line!" Shugaba ta fad'a tana kallon Ateefa

Waro Ido Ateefan tayi tace"so how was it?? Intriguing right?? Ko am not allowed to say it ne??"

Ya mutsa fuska tayi wanda hakan ya mugun kara mata wani shegen kyau kafin ta wuce gaba inda ta bar su Asiya da sakin baki

Dan juyowa Ateefa tayi bayan Shugaba tayi gaba tace"baku ce mun she's this pretty ba!"

"Akia Muma idanuwan ta kawai muke gani fa! Bamu tab'a ganin fuskar ta ba!"Asiya ta fad'a cikin mamaki itama

Bata yi magana ba tasa sauri tana cewa"haba k'awa ki jira ni mutafi tare mana!"

Ko tsayawa batayi ba ta shiga cikin gidan, kaman yanda tayi tunani a parlour ta gansu a zaune

Da sallama ta shiga cikin palourn tana kallon maman ta dake zaune,mikewa maman tayi cikin farinciki ganin yar ta da sabuwar fuska

"Khatoon!"

Wani irin sanyi taji acikin ranta ganin cewan Mamanta tasake gane ta a karo na biyu

Murmushi ta d'aura akan fuskar ta tana cewa"nadawo!"

"Sannu da dawowa!" Da ido maman take mata magana akan ta gaishe da mutanen dake zaune wanda hakan ya faru akan idon Ateefa da shigowar ta kenan kuma sarai ta gane abinda maman Shugaban ke nufi dukda bawa ita ake yi ba

"Ina wunin ku!"ta fad'a cikin jam'i Saboda gaskiya ba ta Jin zata iya binsu da gaisuwa daya bayan daya

Amsawa sukayi inda Hajiya ce kawai tace mata sannun ta da dawowa

Awajen ta tsaya ba tare da ta sake yin magana ba

Da murmushi asaman cute face nata ta karasa shiga cikin palourn tana cewa"muje cikin d'aki akwai abinda Zan nuna miki!"

Waro idanuwan ta da suke kaman suna kokarin lumshe wa tayi cikin son tsawatar wa Ateefa da Ido

Amma kasancewa Ateefan ta mugun iya takun ta yasa ta kawar da idanuwan ta daga kan Shugaba tana Jan ta zuwa d'aki

Suna shiga d'aki Shugaban ta fixgi hannun ta tana cewa"bana son shishigi!"

"Ohhh... Ashe hausan ki ma baya fita da kyau!"Ateefan ta juya zancen saboda karaf daya tasan cewan Hausan dake fitowa daga bakin Shugaban bai fita da kyau wanda sai tayi magana mai tsayi ne zaka iya gane hakan amma ita Ateefan karaf daya ta gane

Ahankali tace"Ya...na... fiita!"

"Ohhh... kalya!"..."bana karya!"..."kin sake yi kuma!"Ateefa ta sake fad'a

Shuru Shugaba tayi dalilin Jin yanda take neman yanda zata hukunta Ateefa

"Bari na d'ebo miki porridge din da nayi!"

"Bana so! Ai bawa ni kika yi ba!"..."ai bance wa ke nayi ba!"ta miyar mata batareda ta bari yayi sanyi ba

"Wa saurayin ki kikayi ni bazan ci ba!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now