62

302 63 8
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 61*

*Not edited*
"Nayi wata mummunan mafarki acikin doguwar baccin da nayi! Gabadaya banji dad'in baccin ba ko kad'an, ji nayi kaman bazan tab'a tashi daga wannan baccin ba!"ta sake fad'a tana cire Shugaba daga jikin ta

Kaman an fixgi maganan daga bakin ta tace"Ba mafarki kika yi ba!"

Kallon ta sukayi dukkansu inda matan Uncle dinta ta rufe bakin ta hannu ganin yanda tayi maganan gatsal batare da tayi la'akari da irin yanayin da maman ta zata shiga ba!

"Mene??"

"Azahiri wa'innan mafarkin suka faru!"ta fad'a hawaye na zubowa daga cikin idon ta

Hawayen fuskar ta maman ta shafo tana cewa"dama kina da ruwan hawaye ne??"

Sharewa tayi da sauri saboda batayi tunanin cewan itama kuka takeyi harda hawaye ba

Rik'e hannun maman ta tayi tace"waye baya kuka mama?? Jinjiri ma in baiyi kuka sanda aka haifi a asibiti ba ba'a basu Sallama!"

"Bakiyi kuka acikin mafarki na ba!"

"Nace miki ba mafarki bane!"ta fad'a tana kallon cikin idanuwan mamanta

Wani irin sanyi shuuu maman ta soma Ji harda b'ari"kina nufin sun mutu?? Kuma zaffafiyar mutuwa sukayi??"

Maman ta tambaya a hankali ba tare da ta cire idanuwan ta daga na cikin na Shugaba ba

Hawaye ne suka sake zubo mata cikin tsinkewan zuciya, tamke hannun maman tayi acikin nata sannan ta gyada kanta tana mai rufe bakin ta da dayan hannun ta

Gaban ta ne yayi wani irin bugawa wanda hakan yasa taji kaman an kwad'a mata guduma a tsakiyar kai, sanadiyar hakan ne yasa maman ta damko zanin gado gam kaman zata yaga shi

Itakuma Shugaban kuka takeyi batare da ta lura da irin yanda yanayin maman nata ta chanza ba

Uncle dinta ne ya matso kusa yana tab'a ta, bud'e idanuwan ta tayi tare kallon shi

"Maman ki!"ya fad'a yana nuna ta

Miyar da duban ta wajen maman nata tayi tana cewa"Mama!?"

Tsit kakeji babu amsa illa waje dayan da tayi focusing tana kallo,da sauri ta dan tab'a ta nan maman tayi luuu ta fad'i baya wanda hakan ya nuna musu cewan suman Zaune tayi

Uncle din ne ya fita kiran doctor da sauri inda aka bar ta da Matar uncle

Ba b'ata lokaci suka shigo ward din, dubata doctor yayi tare da yi mata allura sannan ya miyar da duban sa wajen su

"Bai kamata kuna fad'a mata abinda zai sa ta shiga shock ba! sauran kiris yanzu da ta samu dead brain!"doctorn ya fad'a musu da turanci

Gyada kai suka yi, sanda uncle ya bari doctorn ya fita kafin yace" miyesa rayuwan ki ya zamo haka ne?? Kashe ta kike son yi??ke baki san akwai maganganun da bai kamata ana fad'a bane??"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now