46

265 50 4
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 46*

'''#not edited'''
Dare ne sosai inda gari yayi tsit, a lokacin ne wasu daga cikinmu ke bacci,wasu na bautawa Ubangiji wasu kuma na raya Sunnan aure, a wannan lokacin nake zaune a kofar shiga cikin gidan mu
Katuwar gida ne sosai wanda ya gama had'uwa, ga hasken kwan lantarkin da ya haskaka farfajiyan gidan wanda hakan sai sa ka d'auka ko da rana ake
A bakin kofan shiga cikin gidan nake zaune ni kad'ai kaman wata mayya
Karan motan da naji ya shigo farfajiyan gidan mu yasa ni mik'ewa ina matsawa wajen
Wani magidanci ne ya fito daga motan agajiye wanda kana ganin sa tunanin ya dawo daga tafiya kokuma daga wajen aiki zai ziyarce ka
Ware idanuwan sa yayi sosai yana kallon yar tasa da yasan jiran dawowar sa take yi daga wajen aiki kaman yanda ta saba yi kullum
Da murmushi ya tare ni yana fad'in"naji dadin ganin ki cupcake!"
Ba tare da nayi magana ba na karb'i suitcase dinsa tare da yin hanyan cikin gida
Girgiza kai yayi tare da rataya jacket dinshi a kafadarsa sannan ya mara mun baya
Fad'in had'uwan palornmu b'ata baki ne saboda ya had'u iya had'uwa, nan ma ko ina da haske
Wata kyakyawar mata ce ta sauk'o daga sama tana mai sannu da dawowa
Ware mata hannu yayi yana cewa"nayi missing matata!"
Ya mutsa fuska nayi sannan tace"tsami!"
Tsayawa matan tayi bata karasa wajen sa ba dalilin jin abinda na fad'a
Dan shinshina kansa yayi shima, shikam baiji komai ba amma sanin halina yasa shi yace"ohhhh...am sorry lemme freshen up!"
Kallon Dawlat matan tayi tace"ke Khatoon ba zaki iya yin shuru bane wai? Haba danAllah kwanan sa nawa baya gida!? Ya dawo din ma bazaki barshi ya dan huta ba!"
Tafiya na soma yi zuwa dinning room batare da ta yi magana ba
Yayana dake wasa da spoon din dake cikin empty plate ne ya kalle ni tare da cewa"minti nawa ne mun gama cin abincin da bazaki iya jura ba! You're so Oversensitive!"
Saboda har ga Allah ya gaji! Haba, mutum da hanci kaman na kare! Har abinda basu ji ba zata ce taji
Ban kula shi ba sai ma yi nayi kaman bana wajen, mamana ma dawowa tayi ta zauna sannan ta fara zubawa Yayana abinci acikin plate din gabansa
"Ki fara zuba mishi!"na fad'a tana kallon plate din babanmu
Ba tare da ta musa ba ta zuba wa baban, aiko sai gashi ya dawo yana fad'in
"Nagode Cupcake sai yanzu naji dadin jikina wallahi!"
Nan ma shiru nayi, ko loma uku bai kai ba wayarsa ta fara kara
Ganin mai kiran sa ya sashi dauka da sauri inda mamanmu ta zuba mai ido
Gani sukayi ya mik'e da sauri yana cewa ga shi nan zuwa
"Ina zaka je kuma yanzu??"mamanmu ta tambaya cikin damuwa itama tana mik'ewa
"Sorry dear! Case din da muke kai ne naji wai anyi releasing dinsu! So I have to go naji dalilin! ku gama cin abincin ku sai kuje kuyi bacci!"
Kallon agogon mamanmu tayi, karfe3:00am dot ne ya buga akan katuwar agogon dake makale ajikin bango
A baya nabi babanmu har zuwa waje, da murmushi a samar fuskar sa ya shafa kaina yana ce mun bari yaje ya dawo
"Kijirani gobe da kaina zan kaiki makaranta!"shine abinda ya fad'a cikin so
Gyada kai nayi nace"zan jira ka! Amma karka dad'e!"
"Yauwa mamana! A d'an yi mun murmushi mana na dad'e banga kinyi ba!"ya fad'a yana kallon fuska ta
Samun kaina nayi da sak'in mai murmushi wanda hakan yayi mugun mishi d'adi sosai
Katuwar kumatuna yaja yace"yar duma-duma kawai! Kinyi kyau sosai! Da so samu ne ki dinga mun wannan murmushin kullum!"
Ganin ban yi magana ba yasa shi shiga cikin motar sa yana tayarwa
A hankali nace"bazan iya ba! Amma zan kokarta"
"Nooo karki damu wish dina kawai na fad'a miki bai zama lallai sai ki cika mun shi ba amma zan ji dadi in kika cika mun!"ya fad'a yana mun murmushi
Murmushin yak'e nayi ina mai wasa da bakin rigan baccin jikina
"Karka dad'e! Ina jiran ka gobe da safen!"na sake fad'a mai
Gyada kai yayi tare da yin reverse, har ya bar gidan bai daina kallona ta mirrorn motan sa ba nima ko motsawa ban yi ba har sanda naga Fitar sa, juyawan da zan yi naga mamanmu a bakin kofa tana kallon mu itama
A hankali ta nufi bakin kofa inda taji maman ta na cewa"boarding zamu tura ki saboda gaskiya kina hana ni jin dadin mijina! Kullum kece aransa! Please ki saki jiki damu saboda muji dadi muma! Kaman ba a gidanku kike ba?? Please! Wallahi muna damuwa kawai don babu yanda muka iya ne!"
Kallon mamanmu nayi cikin tausayawa rayuwan mu duka!nima ba a son raina nake nuna musu halin ko in kula ba! I wish nima zamu zauna su dinga hira da mamanmu saboda shi baban mu ba kullum yake kwana a gida ba amma bana iyawa! Cos wata rana sai nayi sati ban yi magana da kowa a gidan ba shiyasa ma babu wanda sukayi sabo dashi....
*Laqeet AbdulQuadir* shine ainihin sunan Baban ta, babban ma'aikacin CBI wanda yasan kan aikin sa kuma yabawa aikin sa muhimmanci sosai
Dan Nigeria,haifafen dan garin Maiduguri kuma Kanurin asali saboda kana ganin sa ma zaka ga yana d'ibi da asalin kanurai
Ya fito daga ahali masu hali sosai kuma shine na 3 acikin yayun sa
Familyn su sun shahara a harkan mai sosai shiyasa yayun sa suka sadaukar da rayuwan su suma ga harkan man
Shine kawai ra'ayin su ya banbanta yasamu ya shiga police school saboda a cewar sa yana mugun son aiki acikin uniform
Lokacin da yaje yin masters dinsa a Dubai ne ya had'u da *Nafiah* kyakyawan mace yar asalin Shuwa Arab
Kallo daya suka mawa juna suka san they're made for each other,
Ba b'ata lokaci ko masters din bai gama ba ya matsa da sai an mai aure gashi daman ita din ma tana final year dinta shiyasa ta yarda
Basu wani ci soyayya a waje ba akayi musu aure, anan Dubai din suka cigaba da zama saboda makarantun su
Da Allah yayi nan ne wajen zaman su kuwa aka bashi aiki daidai lokacin da ya karaci masters dinsa
Babu yanda suka iya sai zama, shekara daya cif Allah ya basu d'a wanda ya ci sunan baban Laqeet wato AbdulQuadir amma suna kiran sa da *Baba*
Sanda baba yayi shekara hudu kafin ta sake haifo musu kyakyawar baby mai kama da ita
Itakuma aka sa mata suna *Dawlat Khatoon*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu inda matsalar da suka fara fuskanta shine rashin fara'an Dawlat!
Bata cika magana da mutane ba, kuma bata son hayaniya ko kad'an cos abinda baka san kayi ba ita zata hankarar da kai
Ko cin abu kake yi a gefen ta ta dinga ya mutsa fuska kenan wai kana damunta
Ga hancin nan kaman na kare babu abinda bata ji dashi, she's so sensitive
Sai wani abu daya kuma shine jefi-jefi zakaji tana magana ita kad'ai
Kuma babu yanda maman bata yi akan ta fad'a mata dawa take magana ba amma tak'i
Toh da suka ga abun yayi tsanani ne yasa suka daganta mata da Addu'a dakuma maganguna
Sanda sukayi shekara 6 a Dubai kafin aka mawa mijin ta transfer zuwa UK toh anan ne suke zaune yanxu...
A yanzu wani aiki ne yake dad'ar da babanta a wajen aiki har ya zamana cewan yana kwana achan din....
Wasu yen Nigeria suka kama suna yin black market da wasu turawa
Abun yayi mugun tsanani saboda trafficking din mutane akeyi ana kai kasashe ana sayar dasu
Wasu kuma cire musu part akeyi ana siyarwa abun gabadaya babu dadin ji ko kad'an
Shine dai suka yi nasaran kamasu, kasancewan baban ta yana daga cikin oguna shiyasa abubuwan suke shafan sa
Tohh yanzu duk evidence ya nuna cewan su din ne masu black market da mutane kuma har ya samu yayi nasaran tura mataimakin ogan su wanda suke tunanin shine ogan gidan yari shiyasa ya dawo gida....
Alokacin da ya office dinsu har ya samu an sallame su wai daga sama akace ayi freeing dinsu
Wani irin b'acin rai ne ya turnuke shi nan ya haye sama wajen ogansu
Ba Tare da yayi mai bayani ba ya mik'a mai wani file sannan ya fita
Zama yayi akan kujeran office din tare da dafe kansa agajiye
Ace sun fi wata suna investigating case din amma a dare daya aka Sallame su abun yayi mugun mishi ciwo
Wayan sa da yayi kara ne yasa shi cire hannun sa daga kai sannan ya fito da wayan
"yes sir!"ya fad'a a hankali
"USB da kuma sauran evidence din hannun ka zaka kawo mun yanzu!"ogan sa ya fad'a tare da katse kiran
File din hannun sa ya bud'e yana dubawa, mik'ewa yayi tare da yin hanyan waje yana kiran yaran sa....
Ashirye take acikin uniform din makaranta tana jiran sa a bakin kofa kaman yanda ta saba
Wristwatch din black eagle dake hannun ta take ta faman dubawa
Fitowar yayan ta dakuma maman su yasa ta cusa kanta a tsakiyar cinyar ta
"Khatoon!?"maman ta ta kira ta a hankali, dan d'agowa tayi kad'an tare da kure maman da ido
"Muje kawai na kaiku tare!"
Girgiza kai tayi alaman a'a dukda tasan sun kusa yin latti amma zata bari babansu ya dawo
"Hmmmm..."mamansu tayi sannan tace Baba ya shiga cikin motan
Har mamanmu ta dawo daga kai baba makaranta babanmu bai dawo ba kuma itama bata Mike daga inda take ba
"Na kaiki dinne?in yaso In ya dawo ya d'auko ki?"
"Zan jira sa!"na fad'a tare da  d'aura kaina akan kafa ta
Waya maman mu ta zaro tare da danna lambobin babanmu amma shiru kake ji bai d'auka ba
Ba tare da wani damuwa ba ta kyale saboda daman suna haka sai daga baya inya fa missed call sai ya kira back
Har dare tayi babu labarin babanmu kuma bai kira back  wanda yasa abin dawowa banbarakwai
Uniform dina na cire cikin rashin jin dadin ya fa babanmu bai cika Alkawarin sa ba
B'acin rai fa nake ciki yasa ko waje bane na jira sa ba kenan yanda na saba kullum maman mu ma tasha mamaki kwarai dagaske
Horn din motan da naji ne   yasa gabata tsinkewa, mik'ewa nayi daga  kan gadon da nake a Hankali
Kallon mamanmu dake zaune akan coach nay nace
"Mama dama zamuyi bak'i ne?"
Kallon wani bak'i kuma tayi mun sannan tace " bak'i kuma?!"
Gyada kai tayi nace"naji karan horn din daban tab'a ji ba!"
"Tou maman jiye-jiye!" Ta fad'a sanin cewan gate din gidanmu akwai nisa sosai da inda muke saboda daga gate zuwa wajen mu yayi minti 10
Ta wajen windown d'akina mamanmu ta tsaya tana kallon waje
Aiko gani tayi bakak'en motaci suna shigowa, ganin mutanen da suke sauk'a daga cikin motocin yasa gaban ta fad'uwa cikin tsoro
"Khatoon! Mik'o mun waya ta!"ta fad'a mun ba tare da ta kawar da hankalin ta daga kan windown ba
Mik'a mata wayan nayi tare da tsayuwa a gefen ta nima
"Kira yayan ki ta landline"
Har telephone din d'akin yaya na ya gama ringing ba'a d'auka ba
Wayar hannun ta ta mik'a mun tana cewa na cigaba da dialing numbern baban namu sannan ta fita don dubo yayana wanda hakan yayi daidai da shigowan su main palourn mu...

*MHIZZPHYDO...*
'''28th. September. 2020'''

*#Vote,*
*#comment&*
*#Share*

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now