53

242 38 5
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 53*


_Hajrah M Hassern🦋🤍 wannan page din naki ne na ke kad'ai, you lighten up my mood with your comment... Much love dear_

✍️ Akan idanuwan Shugaba aka fitar da Shazia asibiti, tab'e baki tayi tace"kad'an kuka gani... Yanzu Zan fara da kai!"

Motarta ta tayar sannan tayi gaba a 360,saboda ita bata iya tuk'i a hankali, rough tuk'i takeyi koda kuwa ba sauri take yi ba,duk inda ta wuce kuwa sai sun rakata da tsaraban zagi, wasu kam ma sun d'auka ko biyo ta ake yi

Parking tayi a gaban wani club wanda yanxu aka fara zuwa kasancewan yamma tayi,

No respect ta kafa a idanuwan ta tana mai gyara face cap dinta da kyau sannan ta fito daga cikin motan

Idanuwa ne suka dawo kanta saboda motan ta ma abin kallo ne balle mamallakiyar motan

A hankali ta shiga cikin club din, tana shiga ta soma dube-dube da alaman akwai wanda take nema

Tsaki taja lokacin da wani inyamuri yazo yana mata how far baby,

Kauce mai tayi ta karasa shiga ciki abinta, corner ta nema ta zauna

Sanda tayi mintuna har talatin kafin mutane suka fara cika saboda akwai wasan da za'a yi a daidai wannan lokacin

Tana ganin lokacin da ya shigo kaman yanda take tunani, a ta wajen gefen ta ya zauna yana mawa waiter magana bayan ya cire tie dinsa da alaman daga office yake direct

"Wasu dai basu san komai ba in Banda cika ciki da kayan maye!"ta fad'a wa na gefen ta indirectly

Ture kwalaben gabansa yayi gefe yana cewa"Dani kike yi??"

Tsaki taja ganin ya d'auki zafi kenan murfin tukunya,wani ne ya karasa wajen yana cewa.

"Ranka shi Dad'e Shugaba!,wani abu kake nema ne?".

"Shugaba?? Na ina kenan??" Ta tambaya tana haurawa yaron harara

"Shugaban mu ne! Shi ke heading dinmu!"..."A Shan giya yake heading dinku kokuma??"ta sake tambaya

Wani guntun dariya ya sake yana cewa"Yarinya kiyi gida! Da alaman kin bugu ne!kar ki jawo ajalin ki a yau dinnan!"

"Buguwa??ai ko duka kwalaben nan Zan sha bazan bugu ba, kalli nan..." Ta fad'a tana sanya idanuwan ta acikin nashi cikin son samun control akan sa

Aiko ko second 10 ba'a yi baya dawo kaman soko, sai nan nan yake yi da ita

Kwalba daya ta fasa wanda hakan ya dawo da hankalin wa'inda suke gefe da gefen ta kanta

Kaman wacce ta shayu take cewa"Anan wajen akwai wanda ya isa ya ja dani ne??"

Girgiza kai na gefen ta yayi yace"ai duk nan babu wanda ya isa ya ja da Shugaba, in kud'i ne akwai na kanki, in ilimi ne kaman ruwa aka yake a wajen ki, in karfi da Mulki dakuma isa ne babu wanda ya isa yayi ja dake!"

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now