28

290 39 3
                                    

'''TYPING'''📱


*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_


_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_


*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*Shugaba_*
*_SAN(Uwa ta gari)_...(na kud'i ne)*

*Page 28*


✏️Shiru tayi tana kallon sa kaman wanda ruwa ya cinye, murmushi mai sauti yayi kaman yanda ya saba sannan yace

"Kinga Shazy bata da matsala! Idan har na sake mata fuska tou ba tantama har d'aki na zata dinga biyoni, ai kema kinsan ba wani tarbiya kika bawa y'ar ki ba... kaii asalima kou tarbiyan baki bata ba! tou don haka ki kiyaye ni in ba so kike na miki abinda har ki mutu bazaki manta ba!"

Wasu yawu ta had'iye makwat sannan tace"kar ka kuskura ka tab'a mun yarinya! In kuma ka tab'a ta zamu shiga kafar wando daya da kaine!"

Tafi yayi daidai ya gama fesa wasu irin turarika masu sanyaya zuciya sannan ya juyo yace"maman shazia kenan! As you can see zan tafi hira ne! Kuma nasan tana jira na , so karki b'ata min lokaci in kin gama fad'in abinda ya kawoki ki fita mun a d'aki saboda zan rufe kofa gudun kar amun barbad'e!"

Labbanta ta ciza da karfi jin wai ita zata mai barbad'e! Ita da tinda take bata tab'a wucewa koda kofar gidan boka ba balle har ta shiga amma wannan yaron ba karamin raina ta yayi ba, koda yake zata gyara mai zama nan ba da dad'ewa ba

Murmushi tayi cikin barikanci tare da karasowa wajen sa tace"ko kana bukatan k'ari ne?? nasan ban Ishe ka ba a rannan kuma ma baka cikin hayyacin ka lokacin! Ya kamata mu kara kana cikin hayyacin ka saboda ka dand'ana Zuma ta kaman yanda na dand'ana naka!"

Hannu ta ya watsar cikeda takaicin matar uban nasa , ace mutum bashi da kan gado haba!

"Bani da lokacin ki!"ya fad'a yana tura ta waje, yana kaita waje ya danna lock tare da yin wucewar sa yana mai barin ta awajen

Yatsar ta ta ciza tana tunanin yanda akayi har ya fara soyayya

Ita yanda ta san shi , inba Shazia ba, bata tab'a ganin ya kula mace ba saboda irin tsanan matan da ya tashi dashi

Amma ya akayi hakan ta faru??lallai dole ne ma ta murza kanbun ta saboda bazata lamunci ganin sa da mace ba,

Wani tunanin da ya darzu a zuciyar ta ne yasa ta yin hanyan d'akin ta da sauri

Wayar ta ta d'auka tare da danna wasu numbers"yanzu zai fito daga gida! Ku tabbata kunyi aikin ku yanda ya d'ace"

Tana gama fad'in hakan ta katse wayar ta tana murmushin mugun ta

"Yarinya zakiyi bankwana da duniyar mu!"...

★★★★★

"Sisi ko zamuje ne??"M² ya tambayi BabynMourad

Kai ta girgiza tana gyara face mask din fuskar Azizat, kafadar sa ya d'age yana cewa

"Tafi nono fari! Mudai zamu yi having fun iya son ranmu!..."wani kallon da ta watsa mai ne yasa shi yin shuru kaman ruwa ya cinye sa

"Azeee! Kar ki yarda ki bari ya rik'e miki nan!..ta fad'a tana tab'a kugunta Azizat din....dakuma nan..ta sake nuna kafadar ta!..iyakansa hannun ki ,kinji ni kou??"

Gyada kai tayi alaman taji sannan ta sakar mata murmushi,

"Miye kike yi haka sisi!?"M² ya tambaya cikin had'a rai

"Miye kake tunani?? Tsaro fa kawai nake bata koda bana nan! Kar giyan soyayya ya kwashe ka kazo kana Sorry I love you bayan komai ya kanmala!"

"Yanzu shaidan da zaki mun kenan?? Ban tab'a tunanin hakan daga gareki ba!" Ya fad'a cikin rashin jin dadi

"Oho dai Allah ya kiyaye hanya!"ta fad'a tana bud'e Mai kofan mota

Share ta yayi tare da zuwa dayan bangaren da Azeee sannan ya shigar da ita motan

Waving ta dinga musu har aka bud'e musu gate suka fita

Hancin motar su na shan kwana na Fareed kuma ya danno kai

Kaman wani dan gida ya danna horn, da sauri maigadin ya lek'o saboda ba yanayin horn din motan mutanen gidan ba kenan

"Ina neman Zulfa ne!" Ya fad'a cikin gadara bayan ya fito daga cikin motar sa yana pocketing hannun sa

"Waye??" maigadin ya tambaya cikin neman k'ari bayani

"Budurwan gidan nan!"..."budurwaye hudu ne agidan nan daya tayi aure daya tana Dubai sauran biyun kuma suna nan wanne acikin su! Kuma ma yanzu daya ta fita guda daya ne aciki yanzu!"

Lumshe idanuwa Fareed yayi cikin takaici mara misaltuwa da wannan parrot maigadin din ya fara kunsa masa

"wacce take nan yanzu na zo nema!"

Baki ya washe sannan yace"tou miye zai hana ka kirata a waya wato ka sanar da ita isowar ka"

"Malam Usman kai da waye?" Ta fad'a lokacin da ta lek'o da kanta waje

Murmushi yayi yana cewa"ina ta cewa Zulfa nake nema!"

"Saboda baka da number na shiyasa ka tsaya making scene anan kou??

"Afuwan emmata na! Gabadaya namanta cewan in an zo gidan masu kud'i sai an yi kira a waya su bada izini kafin a bari a shigo! Kokuma azo a shiga dani!"

Kallon maigadin tayi alaman ya basu waje,shiko ya d'auka tace yaje ya bud'e gate ne, aiko nan ya hau bud'e gate

"Miye kake yi  haka Malam Usman??nace ka bud'e ne??"...cikin rawar jiki yace..."Allah ya baki hakuri Hajiya karama!"

"Miyesa baza'a bari na shigo ba??"... murtuke fuska tayi tace"miyesa kazo? Nayi inviting dinka gidanmu ne??Bana son gayyan sod'i! Kuma ma ban tab'a kiran ka nace maka ga hanyan gidanmu ba which means background check kayi a kaina!...wait! Da miye da miye aka fad'a maka game dani?? Anya an fad'a maka wace ni kuwa?? Tou bari kaji na fad'a maka! Aure na is around the corner gwanda ka daina wahalar da kanka akan abin bazaka tab'a samu ba!"

Duk maganan da tayi babu wanda ya shige sa sai ma cewa da yayi "oh Allah you're making me to fall in love over again!"

"Sai kayi tayi ai!" Ta fad'a tare da shigewa abin ta saboda bazata so ran ta ya b'aci akan wannan stalkern ba,ga wani haushin kanta ta fara ji dalilin rashin bin su M² Cinema kallon wani released movie ba

Cikin d'aga murya yace"emmata na zan sake dawowa gobe!"

Ko kula sa bata yi ba tayi banging kofan da karfi wanda hakan yasa shi matsawa baya da sauri saboda a tunanin sa fad'owa gate din zatayi

Dariya ya fashe da shi yana shafa kansa cikeda shauk'in soyayya

"I love your style emmata na!"ya fad'a yana shigewa cikin motar sa

"Oops"ya fad'a lokacin da ya tina cewa akwai abubuwan da ya siyo mata a bayan motar sa

D'auka yayi tare da kwankwasa gate sannan ya mik'a wa mai gadi akan ya bata....


*MHIZZPHYDO...*
'''17th. July.2020'''

*#Vote,*
*#comment&*
*#Share*

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now