👑SHUGABA👸

411 46 1
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Mhizzphydo_*

*_Page 5_*

✏️Lumshe idanuwan ta tayi a hankali , daga baya ta wuce abinta ba tare da ta bata amsa ba

Kallon Arsh Amaya tayi tace"miye sunan ta?"

"Lu~lu! Sunan ta kenan!"ya fad'a tare da yin gaba saboda bai san kuma tambaya na gaban da zata jefo mai ba!

"Suna mai dadi wallahi!"ta fad'a cikin jin dadi,juyawa tayi tare da yin gaba abinta sai washe baki take yi

Chan ta tsaya chak tare da dafe kan ta dalilin tunowa da tayi ashe an aike ta

Cikin sauri ta juyo tana neman su da idanuwan ta amma ko kuran su bata gani ba,tab'e baki tayi tare da dag'e kafadar ta alaman chan ta matse musu sannan tayi wucewar ta...

Kwance yake akan gado mai matasan dake ofishin sa da alama akwai abinda yake tunani, karar wayar sa ne ya dawo dashi , a hankali ya sa hannu ya d'auka

Ganin Masoyiyar sa ke kira yasa shi tashi zaune, tattara nutsuwar sa yayi ya had'a su waje guda tare da d'aukan wayan

Cikin nishad'i ya ce"Amincin Allah ya tabbata gare ki ya ke masoyiya ta!"

"Tare da kai Masoyi na!"maman sa ta fad'a..."lafiya naga baka dawo ba?"

"Masoyiya yau zan dan dad'e kafin na dawo!"Ya bata amsa cikin ladabi

"Anything special today??"ta tambaye sa

"Kusan haka masoyiya amma in na dawo zan baki labarin abinda ya faru!"ya fad'a yana zuba murmushi

"Allah ya kare mun kai Masoyi!"

"Ameen masoyiya ta!"...

★★★★★★★★★★

✏️✏️ Cikin kwanciyar hankali take kwasan baccin ta, daga ita sai karamin gajeren wando da kuma bes dukda uwar sanyin da akeyi

Waras ta ware idanuwan ta tare da mikewa da sauri, kwat mai hannun bes ta d'auko tasa tare da boot 

Hulan kwat din ta rufe kanta dashi sannan ta fice daga d'akin ta...

★★★★★★★★★★

✏️✏️✏️Banda tsaki babu abinda yake ja saboda gabadaya ran sa a b'ace yake

Jefi-jefi kuma yakan daki steering motan sa, daidai ya karyo kwana ya Lura da motan da ke bin sa tin kafin ya bar cikin makaranta

Wani irin wawan birki ya ja sanadiyar ganin mutum tsaye ta tare hanya da zai wuce

Hasken motan ne ya haska ta, cikin sauri ya kashe hasken tare da runtse idanuwan sa dalilin ganin fararen cinyoyin ta a waje

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now