49

271 46 9
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 49*

_Bayan kwana biyu_

Wiwiwiw shine karan motocin polisawa dakuma na ambulance da ke kara a farfajiyan gidanmu

Kasancewan ba'a tashi samo mu ba sai a wannan lokacin, shidinma don homeroom teacher na taga na kwana biyu ban zo ba kuma in ta kira wayan gidanmu ba'a d'auka shiyasa tayi tattaki don duba ko lafiya

Abinda bata yi zato ba ta gani a gidan namu nan cikin gaggawa ta danna lambobin yensanda ta sanar dasu

Basu wani b'ata lokaci suka iso aka kwashe mun zuwa asibiti inda yen jarida suka hau binmu a baya

Yayana har ya fara wari,iya walakanci angama walakanta mun yaya, in ka kalli gawan sa sai ka zubda kwalla masu zafi na tausayin sa

Gyara yayana sukayi daidai gwargad'on yanda zasu iya sannan suka wuce dashi morgue

Inda mamanmu kuma bata farfado ba har sanda suka dinga d'ura mata allurai kala daban-daban

Lokacin da ta farfado ma kaman mahaukaciya haka ta dawo, gabadaya maman namu ta fara samun tab'in hankali

Kullum sai da allura ake calming dinta down, lokacin da muka samu ta fara dawowa daidai yayi dai dai da zuwan yayan ta wanda yake zama a cikin state kuma ya kasance babban soja

Sosai abun ya tab'a shi sosai barinma da yaga gawan yaya na gashi duk yanda sukayi nayi magana shi da yensanda dakuma shidin akan na fad'a musu su waye nak'i

Da ba dan condition din da nake ciki tou ba shakka babu abinda zai hana shi Zane ni tass babu ruwan sa, amma babu ya da ya iya haka ya had'iye b'acin ran sa yana kallona, su ma yensanda kyaleni sukayi suna jiran lokacin da mamana zata dawo daidai sai su tambaye ta

Sanda aka wanke mun da maganguna kafin suka rufe mun shi da bandage dukda daman har kunan ya bushe

Lokacin da suka cire mun bandage din ko fuskata bana iya d'agawa saboda yanda nake jin kaina

Gani nake kaman na dawo beast, abubuwa suka min zafi sosai,numfashi ma dakyar nake shak'a

Sanda mamana ta farka ko waje na bata kallo, she was insisting cewan ni na kashe yaya na

"Bana son kallon ki! Na yafe yarinya mara tausayi! Ki tafi!" Shine abinda take fad'a

Ni gabadaya banma san miye nayi ba! Saboda banda masaniya akan abinda take fad'a

Transfer yayan mamana ya nemi a mata daga _John Hopkins hospital_ zuwa Massachusetts General Hospital, Boston!

Abun ya basu mamaki sosai saboda ba kasafai ake transferring din mutane daga asibitin su zuwa wani asibitin ba saboda asibitin su aka fi sani da inda suka tara gabadaya kwararrun likitocin duniya amma kasancewan guardian dinta ne yace A musu transfer babu yanda suka iya

Achan aka cigaba da bata kulawa inda nikuma na koma barrack dinsu da zama saboda iyalan sa suna nan Nigeria

Daga baya ne dai jikin maman nawa ya daina karb'an maganguna sai ya zamana tayi weak sosai wanda hakan shi ya jawo mata shiga dogon suma amma jefi-jefi takan firgita amma bawai ta farfad'o ba

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now