48

260 46 10
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of  tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*

*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 48*

Ganin da nayi nak'i kawar da idanuwa na yasa ya kau da nashi cikeda tsoro saboda a zaton sa aljana ya hango a wajen

Hannu kawai yayi wa en aikin sa suka sake b'arka a jikin yayana suka fito duk abubuwa masu amfani acikin jikin sa

Babana kuwa wani irin kuka mai tsuma rai yakeyi da ganin yanda ake walakanta mai Yaro

Dariya mutumin ya saka cikin mugunta yana cewa"ka shirya yin magana ne kokuma sai mun cigaba daga kan matar ka?"

"Wallahi ban sani ba ne shiyasa! DanAllah ka bar mun iyalaina haka! Kayi hakuri!"

"Ai in bakayi magana ba bayan na gama da matar ka zan zo har wajen na karasa shi!"Mutum ya fad'a wanda hakan zai nuna maka cewan gaskiyan sa yake fad'a

Bud'e labulen nayi gabadaya yanda kowa zai iya hango ni da kyau

Cikin mamaki nace"Duk wannan abun akan flash? Flash!?"

Gabadaya sai idanuwa ya dawo kaina cikin mamaki
Kallo na yakeyi yana tunanin tin yaushe nake tsaye a wajen ina kallon su

"Kin gani??" Ya tambaya cikin mamaki!

Ganin banyi magana ba yasa wani daga cikin yaron sa ya sauk'o dani kasa

Aiko nan ya hauro sama zuwa waje na, cikin zaro ido yake mun magana wai don na tsorota... Azuciya ta nace aikin banza

Tab'a ni da yake kokarin yi nasa na matsa baya ina basa wani mugun kallo mai kad'a hanjin mutane

Sunkuyar da kansa yayi tare da matsawa gefe kaman wani dan aikina

Gaba tayi inda ya mara mata baya, akan stairs din karshe ta tsaya tana kallon su daga nesa kad'an

"Kana nufin yanda kuka shigo kokuma yanda ka taka kan hannun mamanmu kokuma yanda ka mata allura ka kuma yi wa yayana kafin kazo kuka b'arka shi! Kokuma mamakin da na hango akan fuskar ka lokacin da ka ganni!" Na fad'a ko numfashi ban ja ba

Gyara zaman sa yayi dakyau yace"So interesting! Wato kinga komai!?"

Karasa saukowa nayi kaman ba yar shekara 9 ba, cak na tsaya lokacin da idanuwa na suka gane min yayana dake kwance akasa shab'e-shab'e saboda ko tantama babu, rai yariga da yayi halin sa

Iya walakanci sun gama walakanta shi, saboda ko inda suka yanka basu dinke wajen ba aka suka bar wajen ko kyan gani babu

Zuciya ta ce ya tsinke lokaci guda cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba!

Hannu nasa na rufe bakina cikin son hana kaina fashewa da kuka da nake shirin yi

Wasu hawaye masu zafine suka soma zubo min babu kakautawa

Cikin rawar murya nake cewa" akan flash kuka Awalakanta shi har haka?? Akan Flash drive din banza??"

"Khatoon?" Naji babana ya kira ni da raunin murya

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now