57

281 46 8
                                    

'''TYPING'''📱

*_👑SHUGABA👸_*
_(Cigaban Zulfa)_

_Wannan labarin kirkirere neh! Any likeness of tale or way of life should be considered as a coincidence_

*_Wattpad:Mhizzphydo_*


*My Books are;*
*_Abar so_*
*_Zulfa_*
*_Shugaba_*

*Page 56*


Zaune tayi a gabansa tana kuresa da razannanun idanuwan ta wanda hakan ya tsunbula shi acikin ruwan rashin nutsuwa

"Ina yake??" Shine tambayan da ta jefa mishi lokaci daya

Cikin rawar murya yace"waye??..."babana!"ta bashi amsa still idanuwan ta na kanshi

"Nasan na kashe rayuka da yawa amma kuma bana rik'e fuskar su ko sunan su balle insan cewan shine baban ki! Sai dai kiyi hak'uri!"ya fad'a a takaice yana sunkuyar da kanshi kasa

Wani irin  mik'ewa tayi cikin b'acin rai idanuwan ta na komawa fari wanda hakan yayi sanadiyar haska fuskar sa dake bu-bushe da jini

Baya yayi atsorace saboda gani yayi kaman cinye sa zata yi da ganin yanda ta wani dawo,cikin rawar baki yace"waye babban ki tou?"

"Flash!"ta fad'a a takaice ba tare da ta kawar da idanuwan ta daga kanshi ba

Zaro idanuwa yayi a kidime yana zamewa daga kan kujeran dake zaune

Kyallen fuskarta ta cire tana cewa"ka tina??ina yake,babban nawa?"

Kneeling yayi yana cewa"DanAllah kiyi hak'uri!"

"Miye zanyi dashi?? lokacin da Mamana da babana suke rokon ka kaji ne?? Ko ka manta ne??"

Shuru yayi cikin rashin sanin abin Fad'a gashi gabadaya nutsuwan su ya riga ya bar gangar jikin sa da jimawa

"Ina babana!?"ta sake tambaya.... cikin i'ina yace"y..ya mmutuu!"

Katse shi tayi da cewa"Ka kashe shi dai!"

Girgiza kai yayi yace"bani na kashe shi ba...had'iyan zuciya yayi ya mutu!"

"Kai ka jawo ai! Kai ka kashe shi! Na maka alkwarin bazaka tab'a sake dariya ba arayuwar ka! Kai da sake ganin danka kuma sai a lahira! Kuma sai na tabbata an yi maka hukuncin da ya kamata, sai na sa wa'inda ka hallaka farinciki a chan inda suke!"ta fad'a tana kifar mai da table cikin b'acin rai saboda daman tasan da wuya in har yanzu yana nan kawai dai ta gwada sa'an ta ne

Har ta fice ta sake dawowa baya tana cewa"Ya kukayi da Gawan sa? Ci kuka yi??"

Cikin sauri ya girgiza kansa yace"bari muka yi a wajen!"

"Location??"ta tambaya a dakile... Nan ya fad'a mata sannan ta kama hanyan ta ta fita

Tana ce musu ayi gaggawan transfer dinshi, saboda daman ainihin laifin sa ba a zallan Nigeria ta tsaya ba, don haka dole suyi handing dinshi over tinda daman yana daga cikin yarjejeniyan su...

Uniform dinta kawai ta d'auka tare da jakan su na sojoji wanda gabadaya duk abubuwan ta yana ciki, ko kwana daya bata kara ba aka zo aka d'auke ta ko yar'ta bata je ta duba ba dukda yarinyan tana ranta, amma kuma ya zatayi?? Dole ne ta tafi

Suna isa barrack aka dinga firfito wa ana saluting mata har ma da sabin zuwa wa'inda suka bata shekaru... Office din ogan wato Uncle dinta ta shiga taje tayi reporting mishi kaman yanda ya kamata tayi ba tare da ta nuna cewan sun san juna ba, har sai sanda ta fita ya aika a kirawo ta yana mamakin yanda ta dawo,

👑👑SHUGABA👑👑Where stories live. Discover now